26
Apr
Daga UMAR M. GOMBE Gwamnan jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya naɗa Majalisar Gudanarwa da za ta sanya ido kan gudanar da harkokin Jami'ar Jihar Barno. Zulum ya naɗa majalisar ne a ranar Litinin a fadar gwamnatin jihar, wadda za ta gudana ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mohammed Indimi. Sauran mambobin majalisar sun haɗa da Farfesa Abubakar Mustapha, Farfesa Bankole Ogumbameru, Farfesa Shettima Umara Bulakarima, Alhaji Lawan Buba, wakilin majalisar dattawa na jami'ar da dai sauransu, yayin da rajistaran jami'ar zai kasance riƙe da muƙamin sakataren majalisar. Gwamnan ya yi kira ga 'yan majalisar da su samar da tsari mai inganci wajen…
