Labarai

Kaduna: ‘Ba mu wakilta kowa don sasantawa da ‘yan fashi ba’ – Aruwan

El-Rufai Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha alwashin hukunta duk wanda ta kama yana sasantawa da 'yan fashi ko 'yan ta'adda a jihar. Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata. Kwamishinan ya ce Gwamnatin Kaduna ba ta wakilta kowa ba don shiga tsakaninta da 'yan fashi, tare da ƙaryata rahoton da ke cewa Gwamnatin Nasir El-Rufai ta naɗa wasu wakilai domin tattaunawa da masu aikata muggan laifuka a jihar. Sanarwar Kwamishinan ta buƙaci 'yan jihar da su kai rahoton…
Read More
Filato: An tsige DPO bisa zargin kashe wasu makiyaya biyu

Filato: An tsige DPO bisa zargin kashe wasu makiyaya biyu

Daga BASHIR ISAH Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Filato, Edward Egbuka, ya tsige tare da tsare DPO mai kula da yankin ƙaramar hukumar Bassa a jihar, wato DSP Solomon Machu, bisa zargin kisan wasu makiyaya biyu a jihar. An zargi DPOn ne da kashe Musa Giwa ɗan shekara 24, da Ibrahim Sa'idu ɗan shekara 30, ta hanyar mafani da bindigabayan da 'yan bijilanti na yankin suka kama makiyayan a ƙauyen Dogon Daji tare da miƙa su ga DPOn cikin ƙoshin lafiya a Lahadin da ta gabata. Manhaja ta tattaro cewa a Alhamis da ta gabata 'yan sanda suka miƙa gawarwakin…
Read More
Ogun: Gwamna Abiodun ya ƙaddamar da Amotekun

Ogun: Gwamna Abiodun ya ƙaddamar da Amotekun

Daga WAKILINMU A matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da matsalar tsaro a Jihar Ogun, Gwamnan jihar, Dapo Abiodun, ya ƙaddamar da shirin bada tsaro na cikin gida, wato Amotekun. Da yake jawabi yayin ƙaddamawar, Gwaman ya ce ba a samar da Amotekun don ta zama kishiya ga sauran hukumomin tsaro ba, face don ƙarfafa wa fannin tsaron jihar. Ya ce gwamnatinsa za ta bai wa shirin Amotekun cikakken haɗin kai tare da samar masa da kayan aikin da yake buƙata don cim ma manufar kafa shi. Tuni Gwamnan ya nuna alamar mara wa shirin baya ta hanyar…
Read More
Filato: Gobara ta yi ta’asa a kasuwar doya a Qu’an Pan

Filato: Gobara ta yi ta’asa a kasuwar doya a Qu’an Pan

Daga WAKILINMU An samu aukuwar mummunar gobara a kasuwar doya ta Namu ta Tsakiya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Qu'an Pan, Jihar Filato. Manhaja ta kalto cewa gobarar ta auku ne da daddare a Lahadin da ta gabata inda ta lalata tarin doya da sauran kayayyakin abincin na muƙudan kuɗaɗe. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, jaridar Daily Nigerian ta ce ba a kai ga gano sababin faruwar gobarar ba. Bayanai daga yankin sun nuna sama da manona 100 ne ibtila'in gobarar ya shafa. Tare da yin kira ga gwamnati a matakai daban-daban da su tallafa wa waɗanda lamarin…
Read More
An gano mutum 51ɗauke da cutar tarin fuka a Binuwai

An gano mutum 51ɗauke da cutar tarin fuka a Binuwai

Daga UMAR M. GOMBE Dr Chubby Eze daga gidauniyar KNCV Foundation mai zaman kanta, ya ce mutum 51 ne aka tabbatar sun kamu da cutar tarin fuka (TB) daga cikin mutum 609 da aka yi musu gwaji a Makurdi babban birnin jihar Binuwai. Eze ya bayyana haka ne sa'ilin da yake amsa tambayoyin manema a Makurɗi a Juma'ar da ta gabata, tare da cewa an ɗauki samfurin mutane daga sassan ƙananan hukumomin jihar aka tafi da su cibiyoyin gwaji. Mr Dominic Alamkah wanda ke da hannu a shirin gwajin, ya shawarci waɗanda aka gano ɗauke da cutar da su tabbatar…
Read More
Kaduna: Ana ci gaba da binciken gano sarakunan da suka ɓace

Kaduna: Ana ci gaba da binciken gano sarakunan da suka ɓace

Daga FATUHU MUSTAPHA A halin da ake ciki, jami'an tsaro a jihar Kaduna sun bazama bincike domin gano wasu masu rawani su uku da suka ɓata a masarautar Atyap cikin ƙaramar hukumar Zangon Kataf waɗanda aka sace su bayan kammala wani taron sulhu da suka gudanar a Lahadin da ta gabata. A cewar Gwamnatin Jihar Kaduna, mutum shida ne suka ɓata da farko a kan hanyarsu ta komawa gida bayan taron. Ta ce jami'an tsaro sun samu nasarar gano mutum guda daga cikinsu kuma sun miƙa shi ga 'yan sanda, kana wasu mutum biyu daga ciki sun tsere daga hannun…
Read More
Ƙoƙarin da Nijeriya ke yi don kauce wa sake fama da annobar korona, Ministan Lafiya

Ƙoƙarin da Nijeriya ke yi don kauce wa sake fama da annobar korona, Ministan Lafiya

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnatin Tarayya ta bada haske kan wasu matakan da ta ɗauka domin tabbatar da Nijeriya ba ta yi fama da ɓarkewar annobar korona karo na uku ba. Yayin da wasu ƙasashen duniya suka soma sake fama da bugun annobar karo karo na uku, Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aikin gwaje-gwaje da take yi domin ganowa, killacewa da kuma kula da waɗanda suka kamu da cutar. Ehanire ya bayyana haka ne a Litinin da ta gabata a Abuja yayin da kwamitin Shugaban Ƙasa kan Yaƙi da Cutar Korona ke…
Read More