Labarai

An cafke dillalin ƙwayar da ke da alaƙa da badaƙalar Abba Kyari

An cafke dillalin ƙwayar da ke da alaƙa da badaƙalar Abba Kyari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja NDLEA ta cafke Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, ƙasurgumin dillalin ƙwayoyi, wanda shi ne ummul-aba-isi na cinikin ƙwayar Tramadol ta Naira biliyan 3, wacce a ke tuhumar dakataccen ɗan sandan nan, Abba Kyari.  Ukatu, wanda shine Shugaban Rukunin Kamfanin Mallison, dubun sa ta cika ne bayan watanni a na fakon sa kuma ana ta kulli-kurciya da shi. An dai cafke shi ne a cikin jirgin sama a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a kan hanyarsa ta zuwa Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Afrilu. Binciken hukumar NDLEA ya bayyana cewa…
Read More
Bikin Sallah: Gwamnati ta ba da hutun gama-gari na yini 2

Bikin Sallah: Gwamnati ta ba da hutun gama-gari na yini 2

Daga BASHIR ISAH Domin bai wa al'ummar musulmin Nijeriya musamman ma'aikata, damar gudanar da shagulgulan bikin Sallah Ƙarama cikin nishaɗi da annashuwa, Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun gama-gari na yini biyu, Litini 2 zuwa Talata 3 ga watan Mayu, 2022. Sanarwar hakan na ƙunshe ne cikin sanarwa da ta fito ta hannun Babban Sakataren Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Shuaib Belgore a madadin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola a ranar Alhamis. Ministan ya yaba wa ƙwazo da sadaukarwar da ma'aikatan gwamnati ke nunawa a bakin aiki wanda a cewarsa, hakan ta ƙara wa Nijeriya tagomashi a idon duniya. Sanarwar…
Read More
Shekara 52 na mulkin Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, sun ƙayatar – Buhari

Shekara 52 na mulkin Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, sun ƙayatar – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya jajenta wa gwamnatin Jihar Oyo da al'ummar jihar kan rasuwar Sarkin Yarabawa Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, ranar Juma'a. Buhari ya bayyana shekara 52 da sarkin ya shafe a karagar mulki da "masu ƙayatarwa ta hanyoyi da dama" cikin wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ƙasa Femi Adesina ya fitar. A ranar Asabar aka yi jana'izar sarkin a tsohon garin Oyo, inda aka binne shi a farfajiyar masarautarsa. Masarautar Oyo ta ce ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekara 83 bayan ya yi jinya a…
Read More
Yajin aikin ASUU: Gwamnatin Nijeriya za ta fara aiwatar da tsarin ‘ba aiki, ba albashi’

Yajin aikin ASUU: Gwamnatin Nijeriya za ta fara aiwatar da tsarin ‘ba aiki, ba albashi’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Alamu na nuni da cewa watakila Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da manufar ‘ba aiki, ba albashi’ domin daƙile yajin aikin da Ƙungiyar Malaman jami’o’i (ASUU) ta dade tana yi. Matakin da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan sanarwa da wasu wasiƙu da hukumar da ke yajin aikin ta aike wa da wasu ƙungiyoyin jami’o’in da suka haɗa da kwamitin haɗin gwiwa na JAC wanda ya ƙunshi NASU da SSANU. Majiyoyin da suka yi magana kan lamarin sun ce gwamnatin Nijeriya ta yi amfani da manufar tsayar da albashin ne a watan Maris ɗin 2022.…
Read More
Faɗuwar jirgi: Za mu ɗauki matakan kariya, inji Babban Hafsan Sojin Sama

Faɗuwar jirgi: Za mu ɗauki matakan kariya, inji Babban Hafsan Sojin Sama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babban Hafsan Sojin Sama na Nijeriya, Air Marshal Oladayo Amao ya kai ziyara wurin da hatsarin jirgin sojin sama mai ƙirar 401 ya faru don jajenta wa dangin mutane biyun da suka rasa rayukansu. Jirgin dai ya faɗo ne a Kaduna da yammacin Talata a wani sansanin sojan sama a Kaduna. a lokacin da ya ziyarci Kaduna ranar Larabar da ta gabata don jajenta wa iyalai, abokai da 'yan uwan matuqa jirgin saman da ya faɗo a Kaduna mai qirar 401 na makarantar koyon tuƙin jirgi, inda ya tabbatar da cewa an ɗauki dukkan…
Read More
Mataimakin Gwamnan Katsina ya ajiye muƙaminsa

Mataimakin Gwamnan Katsina ya ajiye muƙaminsa

Daga UMAR GARBA a Katsina Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu ya ajiye muƙaminsa na kwamishinan ma'aikatar aikin gona, muƙamin da yake riƙe da shi tun kimanin shekaru 7 da su ka wuce a bisa jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari. Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Musa Kalla ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai jiya Alhamis. Kalla ya bayyana cewar mataimakin gwamnan ya ajiye muƙamin nasa ne don bin umarnin sabuwar dokar zave da shugaban ƙasa ya saka wa hannu mai lamba 84(12) ta shekarar 2022 wadda aka gyara. Ya ƙara…
Read More
Rundunar Sojojin Sama za ta binciki musabbabin hatsarin jirginta a Kaduna

Rundunar Sojojin Sama za ta binciki musabbabin hatsarin jirginta a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Shugaban Rundunar Sojojin Sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, ya umarci hukumar binciken haɗurran da ta fara bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin ‘Super Mushshak’ na horar sojin sama da ya afku a sansanin sojojin saman Nijeriya (NAF) da ke Kaduna. Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai na Enugu ranar Laraba. Air Commodore Gabkwet ya ce, CAS, yayin ziyarar ta'aziyyar da ya kai ranar Laraba ga iyalan waɗanda haɗarin jirgin ya…
Read More
Dalilinmu na ƙin tura jirgin yaƙin Tucano Arewa Maso Yamma – Fadar Shugaban Ƙasa

Dalilinmu na ƙin tura jirgin yaƙin Tucano Arewa Maso Yamma – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya ta bayyana cewa, kafin a aike da jiragen saman yaƙi na Tucano da aka sayo daga Amurka a yankin Arewa Maso Yamma, wanda ’yan bindiga suka mamaye, akwai buƙatar a bi ƙa’idojin sayen jiragen, domin kada Nijeriya ta kasance cikin baƙin littafin Ƙasar Amurka. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatar da wabi shiri a gidan talabijin na Trust. “Sojojinmu ƙwararren soja ne. Shugaban ƙasa ne ke da alhakin. Idan ya gama yanzu, muna son ya je Kaduna…
Read More
Gudunmawar marubuci ga al’umma

Gudunmawar marubuci ga al’umma

Daga KABIRU YUSUF  1.0 Gabatarwa:Rubutu wata dabara ce ta rubutattun kalmomi ko wasu abubuwa da za su zama a matsayin kalmomin da ake yin su a wasu abubuwa kamar takarda, ko itace, ko dutse ta hanyar amfani da abubuwan rubutu kamar dutse, ko itace, ko burushi, ko alƙalami ta yin 'yan alamomi da za su wakilci magana. Rubutu ya samu ne domin sadarwa ta magana, yadda ba za a manta saqon ba, da adana tarihi, da waƙoƙi, da labarai da sauran hanyoyin ilimintarwa. Wannan takardar za ta yi magana ne a kan gudunmawar ɗan adam ɗin da yake yin wancan…
Read More
Ya maƙale a tayar jirgin sama daga Afirka ta Kudu zuwa Holland

Ya maƙale a tayar jirgin sama daga Afirka ta Kudu zuwa Holland

’Yan sandan Holland sun ce, sun samu wani mutum da ya maƙale a tayar wani jirgin sama da ya tashi tun daga Afirka ta Kudu ya sauka a Amsterdam da ke ƙasar a raye. Jiragen sama dai na tafiyar sa’a 11 daga Johannesburg zuwa Amsterdam, kuma wannan jirgin na dakon kaya ana ganin ya yada zango sau ɗaya ne kawai a Nairobi a ƙasar Kenya. “Abu ne mai wuyar gaske ga mutumin da ya maƙale a tayar jirgin sama ya rayu a doguwar tafiya, saboda tsananin sanyi da kuma ƙarancin iskar shaƙa a sama. Ba a riga an gane shekaru…
Read More