Labarai

Za mu yi maganin ‘yan fashi da masu tada ƙayar-baya, cewar Buhari

Za mu yi maganin ‘yan fashi da masu tada ƙayar-baya, cewar Buhari

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yayi gargaɗin cewa babu wani sassauci game da matakan da gwamnati ta shirya ɗauka na neman kawar da matsalolin 'yan fashi da masu tada ƙayar-baya da sauran manyan laifuka da suka addabi al'umma a faɗin ƙasa. Buhari ya yi wannan gargaɗi ne ta bakin Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, yayin wani taro kan sha'anin tsaro wanda gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya suka gudanar a Jihar Kaduna. Buhari ya yarda cewa lallai Nijeriya na fama da matsalolin tsaro, amma cewa ya buƙaci sabbin shugabannin tsaro da samar da sabbin dabaru kuma…
Read More
EFCC ta yi sabon shugaba

EFCC ta yi sabon shugaba

Daga FATUHU MUSTAPHA A Larabar da ta gabata Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC). Sanatocin sun shafe sa’o’i biyu suna tantance Bawa kafin daga bisani suka tabbatar da shi a sabon matsayin nasa. Yayin da ake tantance shi, Bawa ya bai wa majalisar tabbacin cewa zai yi aiki tukuru don gyara wa hukumar zama ta hanyar inganta harkokinta kafin ƙarewar wa’adin jagorancinsa. Bawa ya ce zai yi aiki tare da waɗanda suka dace a sassan duniya domin tabbatar da Nijeriya ta…
Read More
Bello ya rattaba hannu a wasu sabbin dokokin jiharsa

Bello ya rattaba hannu a wasu sabbin dokokin jiharsa

Daga AISHA ASAS Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanya wa wasu sabbin dokoki guda biyu hannu. Dokokin su ne, dokar gudanar da binciken sanin lafiyar masu shirin yin aure kafin ƙulla aure da kuma dokar haramta tada hankalin jama'a da abin da ya jiɓanci haka. Taron sanya wa dokokin hannu ya gudana ne a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Minna. Da yake jawabi bayan kammala sanya wa dokokin hannu, Gwama Bello ya bayyana dokokin a matsayin masu muhimmancin gaske. Bello ya yaba wa Majalisar Dokokin jihar bisa ƙoƙarin da ta yi wajen nazarin dokokin yadda ya dace har…
Read More
An yi garkuwa da sirikar Mangal a Katsina

An yi garkuwa da sirikar Mangal a Katsina

Daga FATUHU MUSTAPHA Rahotannin da Manhaja ta samu daga jihar Katsina, sun nuna 'yan bindiga sun sace sirikar hamshaƙin ɗan kasuwar nan Alhaji Dahiru Barau Mangal, a Katsina. Majiyar Manhaja ta ce lamarin ya faru ne a daren Talata a yankin ƙaramar hukumar Matazu, inda 'yan bindigar suka je suka ɗauki Hajiya Rabi. Majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce da misalin karfe 1 na daren Talata 'yan bindigar suka shiga gari suka tafi kai tsaye zuwa gidan Hajiya Rabi suka ɗauke ta suka yi gaba ba tare da an san inda suka nufa ba. Da ma dai…
Read More
EFCC ta kama ‘yan fashin intanet 9 a Minna

EFCC ta kama ‘yan fashin intanet 9 a Minna

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta cafke wasu 'yan fashin intanet su tara a Minna, babban birnin jihar Neja. EFCC ta cafke waɗanda lamarin ya shafa ne a ranar Litinin biyo bayan bayanan sirri da ta ce ta samu a kansu dangane da ayyukan zambatar mutane da suke aikatawa. Kayayyakin da EFCC ta ce ta ƙwace a hannu matasan sun haɗa da ƙananan kwamfutoci da wayoyin salula da kuma motoci. Hukumar ta ce, za ta gurfanar da 'yan fashin a kotu da zarar ta kammala bincikenta.
Read More
Gwamnati ta buƙaci gidajen talabijin su riƙa fassara labarunsu da yaren kurame

Gwamnati ta buƙaci gidajen talabijin su riƙa fassara labarunsu da yaren kurame

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin tashoshin talabijin a faɗin ƙasa su riƙa amfani da yaren kurame a lokutan gabatar da labarai don fassara labarun da suke bayarwa don ƙaruwar masu fama da nakasa. Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ne ya bada wannan umurni yayin wani taro da suka gudanar ta bidiyo tare da jami'an Cibiyar Kula da Nakasassu, a Litinin da ta gabata a Abuja. Wannan na zuwa ne bayan da shugaban cibiyar nakasassun, David Anyaele, ya yi ƙorafin an baro masu fama da nakasa a baya game da sha'anin labarun da tashoshin kan bayar balle…
Read More
Ministar Jinƙai ta jajanta kan faɗowar jirgin saman sojoji

Ministar Jinƙai ta jajanta kan faɗowar jirgin saman sojoji

Daga WAKILIN MU Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana alhinin ta kan faɗowar jirgin saman Rundunar Mayaƙan Sama ta Nijeriya (NAF) ƙirar Beechcraft KingAir B350i Aircraft a ranar Lahadi a Abuja. Rahotanni sun ce jirgin ya samu matsalar inji bayan ya tashi sannan ya faɗo ƙasa. Hajiya Sadiya ta bayyana baƙin ciki kan haɗarin jirgin da kuma asarar rayukan waɗanda ke cikin jirgin da aka yi. Ta ce, "Ina cikin tsananin alhini da baƙin cikin wannan abu maras daɗi da ya faru. Ina miƙa gaisuwa ta ga Rundunar Mayaƙan Sama da iyalan waɗanda…
Read More
Neja: Gwamna Bello ya karɓi fasinjoji 39 da aka kuɓutar da su

Neja: Gwamna Bello ya karɓi fasinjoji 39 da aka kuɓutar da su

Daga FATUHU MUSTAPH Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya karɓi mutum 53 da aka yi garkuwa da su kwanan baya a motar sufuri mallakar gwamnatin Neja (NSTA). Gwamnan ya karɓe su ne a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, babban birnin jihar bayan da aka samu nasarar kuɓutar da su daga hannun ‘yan bindigar da suka kwashe su. Bello ya bayyana cewa, an yi nasarar kuɓutar da mutanen ne biyo bayan tattaunawa da dama da aka yi da kuma ƙwazon da gwamnati ta nuna. Yana mai cewa an kammala dukkan shirye-shirye don binciken lafiyar mutanen kafin a sada su da…
Read More
Nasarawa: Gwamna Sule ya yi ta’aziyyar rasuwar Janar Abokie

Nasarawa: Gwamna Sule ya yi ta’aziyyar rasuwar Janar Abokie

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abadullahi A. Sule na jihar Nasarawa, ya miƙa ta'aziyyarsa ga al'ummar jiharsa, iyalai da abokan Janar Ahmed Aboki (Mai murabus) dangane da rasuwarsa. A wata sanarwa da ta sami sa hannun gwamnan, Injiniya Sule ya bayyana marigayin a matsayin ɗan'uwa wanda ya zama abin koyi a tsakanin al'umma a halin rayuwarsa. Kazalika, ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wanda ya bada gudunmuwarsa ga cigaban ƙasa. A madadin gwamnati da ma al'ummar jihar Nasarawa, Gwamna Sule ya yi ta'aziyya ga iyalai, makusanta da abokan mu'amalar marigayin bisa wannan rashi. Kana, ya…
Read More
Rikicin Biliri: Gwamanati ta kafa dokar hana zirga-zirga

Rikicin Biliri: Gwamanati ta kafa dokar hana zirga-zirga

Daga WAKILIN MU Gwamnatin Jihar Gombe ta kafa dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a garin Biliri da ke cikin ƙaramar hukmar Biliri, biyo bayan rikici da ya ɓarke a yankin. Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahin Abubakar Njodi, ya fitar a Juma’ar da ta gabata, ta nuna dokar ta soma aiki kai tsaye ba tare da wani jinkiri ba da zummar maido da lumana a yankin da rikicin ya shafa. “Gwamnatin jihar ta jaddada buƙatar zama da juna lafiya da kuma ƙoƙarinta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Saboda haka gwamnati ta dakatar da haɗa kowane nau’i na…
Read More