09
Mar
Daga UMAR M. GOMBE 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 30 a Litinin da ta gabata a garin Kutunku da ke yankin ƙaramar hukumar Wushishi a jihar Neja. Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya fito ya bayyana cewa daga yanzu babu wata tattaunawa da 'yan bindigar da ke yin garkuwa da mutane. Bayanai sun tabbatar cewa 'yan bindigar sun shiga ƙauyen Kutunku ne ɗauke da makamai kuma a qafa, inda suka yi wa ƙauyen zobe. Wata majiya ta ce, 'yan bindigar sun ɓoye baburansu a daji ne sannan suka ƙarasa ƙauyen a…
