Gwamna Sule ya nuna takaicinsa kan jinkirin kammala cibiyar lantarki

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Nasarawa, Engineer Abdullahi Sule, ya nuna takaicinsa kan jinkirin da aka samu wajen kammala aikin cibiyar lantarki mai ƙarfin 330 KV a yankin Akurba.

Gwamnan ya nuna damuwarsa ne bayan da ya kai ziyarar gani da ido domin duba yadda aikin kafa cibiyar ke gudana.

Sule ya nuna rashin jin daɗinsa ga ‘yan kwangilar da aikin gina cibiyar ke hannunsu, tare da bada tabbacin cewa gwamatinsa za ta tallafa don tabbatar da aikin ya kai ga gaci nan bada daɗewa ba.

Bayanai sun nuna an samu jinkiri wajen kammala aikin ne sakamakon tsaiko da aka samu wajen isowar kayayyakin aikin da ake buƙata don kammala aikin.

Gwamna Sule ya ce bisa la’akari da abin da ya gani, aiki na dab da kammaluwa. Tare da cewa rashin cim ma matsaya tsakanin Hukumar Kwastam da Kuma Ma’aikatar Kuɗi ta Ƙasa kan batun biyan haraji wajen shigowa da kayayyakin aiki shi ne ya haifar da jinkiri wajen ƙarasowar kayyakin aikin da suka rage.

Don haka ya yi alƙawrin gwamnatin jihar za ta shiga cikin lamarin don tabbatar da an samu daidaito wanda hakan zai bada zarafin kammala aikin cibiyar lantarkin baki ɗaya.