Sadiq Daba ya rasu

Daga AISHA ASAS

Tsohon tauraron masana’antar fina-finai ta Nollywood, Sadiq Abubakar Daba ya rasu. Marigayin ya rasu ne a yammacin Larabar da ta gabata bayan ya yi doguwar jinyar fama da cutar daji.

A halin rayuwarsa, an samu wasu fitattun ‘yan Nijeriya da suka tallafa wajen ɗaukar nauyin kula da lafiyar marigayin, ciki har da hamshaƙin attajirin nan, wato Femi Otedola da Sanata Dino Melaye da Azuka Jebose dai sauransu.

A matsayinsa na ɗan wasan kwaikwayo a halin rayuwarsa, Sadiq Daba ya samu kyaututtuka da dama, ciki har da lambar yabo daga Africa Movie Academy wadda aka ba shi a 2015 sakamakon rawar da ya taka a matsayin “Inspector Waziri” a cikin fim din ‘October 1’.

Marigayin ya yi karatu a St. Edward’s Secondary School. Ya samu shiga manyan makarantu da dama, ciki har da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Haka nan, ya yi aiki a matsayin mai gabatarwa a tasha talabijin ta ƙasa (NTA).

Tauraruwar marigayin ta soma haskawa ne a wani wasan kwaikwayo na talabijin mai suna ‘Cockrow at Dawn’ tun a shekarun 1970.