Gwamnati ta amince da kashe bilyan N797 kan aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano

Daga UMAR M. GOMBE

Majalisar Zarartawa ta Tarayya, ta amince da kashe naira bilyan N797.2 domin aikin babbar hanyar Abuja-Kaduna-Kano.

Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske kan lamarin jim kaɗan bayan kammala taron majalisar a Abuja, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce aikin wanda da farko kwaskwsrima aka so yi wa hanyar amma aka canja shawara zuwa sake gina hanyar baki ɗayanta.

Ministan ya ce canjin fasalin aiki da aka samu shi ya haifar da ƙari kan kuɗaɗen da aka yi nufin kashewa da farko daga naira bilyan N155 zuwa bilyan N797.2.

Daga nan, ministan ya lissafo wasu hanyoyin da aka kammala aikin yi musu kwaskwarima waɗanda ake shirin miƙa su da suka haɗa da: Hanyar Benin-Asaba da ta Abuja-Lokoja da ta Kano-Katsina da ta Onitsha-Aba da ta Sagamu-Benin da ta Kano-Maiduguri, da ta Enugu- Port Harcourt da ta Ilorin-Jebba, sai kuma hanyar Lagos-Badagry.

Duk da dai ministan bai faɗi takamaiman lokacin da za a miƙa hanyoyin ga yankunan da ayyukan suka shafa ba, amma ya ce ana magana ne a kan hanyoyin da ke da nisan kilomita 375, don haka kammala komai zai zamanto rukuni-rukuni ne.

Yana mai cewa rukuni na biyu na ayyukan da ya ƙunshi hanyar Zariya zuwa Kano mai nisan kilomita 137, za ta kammala a gaɓar farko na 2023. Sai kuma rukunin ƙarshe na ayyukan na hanyar Abuja zuwa Kaduna, wanda za su kammala a gaɓa ta biyu a 2023.