Labarai

Anambra: ‘Yan sanda sun bankaɗo gidan da ake safarar jarirai

Anambra: ‘Yan sanda sun bankaɗo gidan da ake safarar jarirai

Daga AISHA ASAS Rundunar 'yan sanda a jihar Anambra, ta ce ta gano wani gida da ake yi zargin ana safarar jarirai a cikinsa a Nnewi cikin ƙaramar Nnewi ta Arewa a jihar. Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar, CSP Haruna Muhammed ne ya bada sanarwar haka, yana mai cewa wadda ake zargin ita ce mai masana'antar jariran, Ms Gladys Nworie Ikegwuonu ta tsere sannan an kuɓutar da 'yan mata masu juna-biyu su huɗu. Jami'in ya ce sun yi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargin suna da alaƙa da harƙallar. Ya ci gaba da cewa sun gano masana'antar…
Read More
Dr Ngozi ta yi rashi

Dr Ngozi ta yi rashi

Mahaifin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, Farfesa Chukuka Okonjo, ya rasu. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 91. Dr. Ngozi ita ce wadda a kwannan nan aka naɗa a matsayin sabuwar Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO).
Read More
Tambuwal zai gina sakandare na zamani guda 40 a Sakkwato

Tambuwal zai gina sakandare na zamani guda 40 a Sakkwato

Daga AISHA ASAS Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal, ya bayyana aniyarsa ta gina Makarantun Sakandare irin na zamani guda arba'in a sassan jiharsa. A wata sanarwa da ya fitar, Tambuwal ya nuna ilimi shi ne ƙashin bayan cigaba a cikin kowace al'umma. Ya ce ayyukan da gwamnatinsa ta sa gaba wajen inganta fannin ilimin jihar, da suka haɗa da yi wa makarantun firamare 1,500 da ƙananan sakandare 180 kwaskwarima, wata alama ce da ke nuni da yadda gwamnatinsa ta ɗauki fannin ilimin jihar da muhimmancin gaske. Kazalika, ya ce gwamnatinsa ta damu da batun yaran da ba su tafiya makaranta…
Read More
Mata 2,900 kowace za ta samu tallafin N20,000 a Binuwai

Mata 2,900 kowace za ta samu tallafin N20,000 a Binuwai

Daga AISHA ASAS Ministar Jinƙai, Agaji da Kyautata Rayuwar 'Yan Kasa, Sadiya Umar Farouq, ta jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta neman fitar da talakawa da marasa galihun ƙasar nan daga ƙangin talauci. Ministar ta ce kimanin mata 2,900 ne gwamnati ta tallafa wa da kuɗi N20,000 ga kowannensu a jihar Binuwai ƙarkashin shirin musamman na Gwamnatin Tarayya na tallafa wa matan karkara a Binuwai da kuɗi don kama sana'a. Sadiya ta yi waɗannan bayanai ne a wajen bikin ƙaddamar da rabon tallafin ga matan karkara a Binuwai, in ji sanarwa da ta fito ta hannun Mataimakin Daraktan Labarai na ma'aikatar…
Read More
Gwamna Sule ya bada umarnin ladabtar da ɗaliban da suka haifar da zan-zanga a kwalejin Mustapha Agwai I

Gwamna Sule ya bada umarnin ladabtar da ɗaliban da suka haifar da zan-zanga a kwalejin Mustapha Agwai I

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bada umarnin a binciko tare da ladabtar da duk wanda aka samu da hannu a rikicin ɗalibai da ya auku kwannan nan a kwalejin fasaha ta Isa Mustapha Agwai I Polytechnic (IMAP) da ke Lafia. Gwamna Sule ya bada wannan umarnin ne ga shugaban kwlejin, Dr. Justina Anjide Kotso, a Juma'ar da ta gabata, domin tabbatar da an ladabtar da waɗanda suka haifar da rikicin da ya yi sanadiyar lalata kayayyaki da dama a makarantar. Ya bada umarnin ne bayan da ya kai ziyarar gani da ido a makarantar, tare…
Read More
Babu buƙatar tada hankula game da rigakafin korona – Gwamnati

Babu buƙatar tada hankula game da rigakafin korona – Gwamnati

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnatin Tarayya ta hori 'yan Nijeriya da su kwantar da hankulansu dangane da rukunin rigakafin korona na Oxford-AstraZeneca da ta karɓa saboda a cewarta, babu wata illa a tattare da rigakafin. Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) ita ce ta bada wannan tabbaci a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis ta hannun shugaban sashenta na hulɗa da jama'a, Mohammad Ohitoto. Yayin da wasu rahotanni ke nuni da wasu ƙasashe sun dakatar da yin allurar, amma hukumar NPHCDA ta buƙaci 'yan Nijeriya kada su tada hankulansu. Hukumar ta ce yayin da take lura…
Read More
EFCC ta cafke ‘yan damfara 37 a Ekiti

EFCC ta cafke ‘yan damfara 37 a Ekiti

Daga WAKILINMU Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) ta cafke wasu matasa 37 da aka fi sani da 'yahoo-yahoo boys' bisa zargin aikata damfara a intanet a Ado-Ekiti, jihar Ekiti. Hukumar da kanta ta bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai da ta fitar ta hannun Shugaban Sashen Yaɗa Labaranta, Wilson Uwujaren, a Litinin da ta gabata. Sanarwar ta nuna EFCC ta yi nasarar kama matasan ne biyo bayan bayanan sirri da ta tattara kan harkokinsu na damfarar mutane ta intanet a yankin. Hukumar ta ce sakamakon binciken da jami'anta suka gudanar a…
Read More
Ogun ta samu rigakafin korona guda 100,000

Ogun ta samu rigakafin korona guda 100,000

Daga AISHA ASAS A Litinin da ta gabata Gwamna jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya karɓi allurar rigakafin cutar korona na AstraZeneca/Oxford guda dubu 50,000 a matsayin gudunmuwa daga Gwamnatin Tarayya. Maganin ya shiga hannun gwamnan ne a ofishinsa da ke Abeokuta, jim kaɗan bayan dawowar tawagar da ta wakilci jihar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Tomi Coker. Gwamnan ya shaida wa manema labarai cewa Ogun ita ce jiha ta farko da ta soma karɓar rigakafinta. Yana mai cewa allura ƙwaya 50,000 da ta samu rukunin farko ne na abin da take sa ran samu baki ɗaya. Ya ce…
Read More