NDLEA ta kama bindigogi 27 a Neja

Daga AISHA ASAS

Jami’an Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a jihar Neja, sun kama wasu mutum biyu ɗauke da bindigogi 27 yayin da suke bakin aiki na bincike abubuwan hawa a yankin Kontagora.

Waɗanda ake zargin, Danjuma Auta ɗan shekara 35, da Daniel Danrangi mai shekara 25, dukkansu ‘yan asalin Dirin Daji ne a yankin Ƙaramar Hukumar Sakaba, jihar Kebbi, sun faɗa a hannun jami’an ne a hanyar Kontagora zuwa Zuru a Litinin da ta gabata da daddare.

A cewar Kwamandan Hukumar na jihar Neja, Mr. Aloye Isaac Oludare, an kama su biyun ɗauke da bindigogi AK 47 ƙirar gida guda 12 da kuma ƙanana guda 15, ɗaure cikin buhu a kan babur.

A wata sanarwar manema labarai da hukumar ta fitar ta hannun daraktan labarai na babban ofishin hukumar a Abuja, Femi Babafemi, ta nuna tsakanin Kontagora inda suka kama bindigogin da kuma garin Kagara inda aka yi garkuwa da ɗalibai kwanan baya, nisan kilomita 107 ne.

Hukumar ta ce bincikenta ya gano maƙerin bindigogin mazaunin Kamfaninwaya ne nan kusa da Kontagora. Ta ci gaba da cewa, za ta miƙa waɗanda lamarin ya shafa da bindigogin da aka kama su da su ga hidikwatar ‘yan sanda a Minna don zurafafa bincike da kuma hukunta su.