Sarkin Kagara ya rasu

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa Sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko, rasuwa.

Tuni dai Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya yi jajantawa ga Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, iyalai da ma ɗaukacin al’ummar Masarautar Kagara dangane da rasuwar.

Bello, ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin da rahma, Ya sanya Aljanna makomarsa, kana ya bai wa iyalansa haƙuri da juriyar rashin.

Marigayin ya rasu ne a wannan Talatar, a garin Kagara, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Rafi. An haife shi ne a ran 5 ga Afrilun 1930 a Tegina. Ya rasu ya bar ‘ya’ya, mata da jikoki.

Garin Kagara na daga cikin yankunan da suka yi fama da hare-haren ‘yan bindiga a baya-bayan nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *