Gwamna Ikpeazu ya maida martani ga Sanata Adeyemi

Daga WAKILINMU

Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia, ya kwatanta Sanata Samrt Adeyemi na jam’iyyar APC daga jihar Kogi da mahaukaci saboda kiran sa da ya yi da mashayi.

Santa Adeyemi ya kira Gwamna Ikpeazu da mashayi ne a lokacin da ya miƙe yana tofa albarkacin baki a majalisa kan batun matsalar tsaro, inda ya ce gwaman mashayi ne wanda ke cikin ɗaya daga waɗanda ba su damu da tsaron jama’arsu ba.

Da yake maida martani kan batun a wajen wani taron ƙaddamar da littafi a Abuja, Ikpeazu ya ce shi dai ba ya shaye-shaye balle kuma ya zama mashayi.

A cewarsa, “Ni ba na shaye-shaye kuma ba na tarayya da masu shaye-shaye. Saboda lamarin shugabanci na buƙatar kamun kai da natsuwa, wannan shi ne dalilin da ya sa akwai buƙatar waɗanda aka wakilta a shugabanci su zamo masu lura da abin da suke furutawa da kuma aikatawa.

“Ba na da ra’ayin faɗa da duk wanda ya yi mini mummunan zargi, saboda shahararren marubuci Chinua Achebe ya faɗa a wani littafinsa, “Idan mahaukaci ya wawushe suturar mai wanka a rafi ya arce, mai kayan ya yi hattara kada ya ce zai bi mahaukacin don ya ƙwato kayansa, saboda idan ya aikata haka mutane za su kasa tantance wane ne mahaukaci tsakanin su biyun”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *