Rundunar Sojojin Sama za ta binciki musabbabin hatsarin jirginta a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Shugaban Rundunar Sojojin Sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, ya umarci hukumar binciken haɗurran da ta fara bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin ‘Super Mushshak’ na horar sojin sama da ya afku a sansanin sojojin saman Nijeriya (NAF) da ke Kaduna.

Daraktan hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai na Enugu ranar Laraba.

Air Commodore Gabkwet ya ce, CAS, yayin ziyarar ta’aziyyar da ya kai ranar Laraba ga iyalan waɗanda haɗarin jirgin ya rutsa da su, ya ba da tabbacin cewa, NAF za ta tabbatar da cewa ta binciki musabbabin hatsarin kuma za a ɗauki matakai don daƙile sake faruwar hatsarin jirgin a nan gaba.

Hukumar ta CAS, ta jajantawa iyalai, dangi da abokan jami’an matuƙan jirgin guda 2, Laftanar Janar Abubakar Muhammed Alƙali da na jirgin Laftanar Iliya Haruna Karatu, waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin.

Air Marshal Amao ya kafa hukumar binciken haɗɗura bayan samun labarin faruwar hatsarin, domin tantance musabbabin abin da ya jawo hatsarin.

Yayin da ya ke Kaduna a safiyar Talata, ya tabbatar wa da jami’an jiragen sama na makarantar horar da matuƙan jiragen sama na 401 cewa, za a yi amfani da dukkan matakan da suka dace don daaile afkuwar irin wannan abu a nan gaba.

Ya kuma tunatar da su kan buƙatar su tsaya tsayin daka tare da mayar da hankali kan ayyukan da aka ɗora musu bisa la’akari da babban aikin da ke gaban hukumar NAF da sauran hukumomin tsaro na kawar da ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma da ma ɗaukacin al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Lamarin da ya faru na hatsarin jirgin sama na masu horar da matuƙan, ya sake zama wani abin tunawa mai ban tausayi game da mummunan yanayin da ake ciki na aikin tuƙin jirgun saman soja da kuma haɗarin da matuƙan jirgin NAF ke cigaba da fuskanta a kullum, don tabbatar da yankin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *