Daga KABIRU YUSUF
1.0 Gabatarwa:
Rubutu wata dabara ce ta rubutattun kalmomi ko wasu abubuwa da za su zama a matsayin kalmomin da ake yin su a wasu abubuwa kamar takarda, ko itace, ko dutse ta hanyar amfani da abubuwan rubutu kamar dutse, ko itace, ko burushi, ko alƙalami ta yin ‘yan alamomi da za su wakilci magana.
Rubutu ya samu ne domin sadarwa ta magana, yadda ba za a manta saqon ba, da adana tarihi, da waƙoƙi, da labarai da sauran hanyoyin ilimintarwa.
Wannan takardar za ta yi magana ne a kan gudunmawar ɗan adam ɗin da yake yin wancan aikin; rubutu, wato marubuci.
1.1 Wane ne marubuci?
Marubuci ɗaya ne daga cikin halittar ɗan Adam da Allah ya kevanta da baiwar yin rubutu cikin salo da tsari na jan hankali domin isar da saƙo na shi ko na wasu ko na rayuwa da alamuran yau da kullum ga waɗanda abin ya shafa.
Marubuci kan isar da waɗannan saƙonnin na shi ta hanyar ƙirƙira ko ayyanawa a littafi, ko gajeren labari, ko takardu, ko waƙoƙi, da sauransu. Yakan rawaito wani abu, ko ya fassaro, ko ya ayyano, ko ya fasalta yadda saƙon zai kai ga inda yake fata.
1.2 Rabe-raben marubuta:
Marubuta sun kasu kaso da dama, da ya kamata mu san kashe-kashen su kafin mu san irin gudunmawar da suke bayarwa. Rabe-raben marubuta sun haɗar da;
Marubutan waƙoƙi
Marubutan littattafan hikaya
Marubutan nishaɗi ko ban-dariya
Marubutan gajerun labarai
Marubutan wasan kwaikwayo (na littafi)
Marubutan wasan kwaikwayo na talabijin
Marubutan jawabi (speech writer)
Marubutan tarihin rayuwar wani
Manazarta (masu sukar rubutun wani don gyara)
Editoci/’yan jarida
Marubutan kundin adana halittun duniya
Marubutan alamuran da ke faruwa
Marubutan tarihi
Marubutan ƙamusu (masu fassara kalmomin harshe da harshe)
Malamai ko masana ko masu bincike su rubuta dalili ko asalin samuwar wani abu (musamman na makaranta)
Masu fassara
Marubutan yadda abu yake aiki (kamar inji ko na’ura)
Wasu marubutan suna yin rubuce-rubucen daban-daban, kamar wani yana rubuta gajerun labarai da wasan kwaikwayo da sauransu. Wannan darasi zai yi magana ne musamman ga marubuta littattafan Hausa, na ƙagaggu ko ayyanannun labarai waɗanda wasu suke kira littattafan soyayya.
2.0 Gudunmawar marubuci ga al’umma:
Shi marubucin littafi (marubucin hikaya) sha-ƙundum ne, domin a yayin rubutunsa na hikaya yakan shiga kowanne fanni kuma ya nuna shi gangaran ne wanda ya fi gwani, don haka gudunmawarsa ta kutsa koina a fannin rubutu, wasu daga cikin gudunmawa su ne;
2.1 Yaɗa ilimi
Ilimi ya haɗar da na addini, na boko, na zamantakewa, na kimiyya da sauransu, marubuta da dama sun yi rubuce-rubuce a kan ilimin addini da tarbiyya, kamar mai daraja Sarkin Musulunci; ya rubuta littafi mai suna ‘Hali Zanen Dutse’ (Norla, 1959/NNPC), Abubakar A. Imam kuma ya rubuta ‘Haji Mabuɗin Ilimi’ (Norla 1959), haka nan Aminu Yahuza ya rubuta littafin ‘Farin cikin Maza Da Mata Izuwa Fahimtar Tarihin Musulunci’ da sauransu.
Wata gudunmawa da marubuta ke bayarwa ita ce ta hanyar littattafan hikaya sukan jefo dukkanin ilimuka da na faɗa a baya cikin hikima tare da ayyana yadda ilimin yake a rubutun su.
A littafin ‘Duhun Damina’ (2020) na Maryamerh Abdul ta kawo mahanga da ilimin addinin Musulunci da likitanci a kan abin da ya shafi zinar hannu (Istimna’i); hanyoyin afkuwarsa da illolinsa da hanyoyin magance shi.
Rahma Abdulmajid a littafinta; ‘Mace Mutum’ (2005) ta kawo ilimin yadda addini ya bai wa mata ‘yanci da kuma yadda mutane suke tauye wannan ‘yancin saboda son ransu. Haka nan a wasu littattafan da dama, za ka tarar da wasu ilimuka na rayuwa.
2.2 Adana tarihi
Tarihi shi ne bayyana wata rayuwa da ta faru a da, da wadda ke faruwa a yanzu tare da hasashen yadda za ta kasance a nan gaba.
Rubutu a lokacin da aka yi shi yana bayyana ainihin hali da yanayi da irin yadda rayuwar alumma take ciki, marubuta suna yin rubuce-rubuce su faɗi hali da lokacin da ake ciki, don haka ko bayan shekaru dubu za a san a zamani kaza ga yadda al’adu da hali da yanayin da al’umma ke ciki ta dalilin wannan rubutu na marubuci.
Haka a rubutun, marubuta sukan bayar da labarun shekaru ɗaruruwa da suka wuce. Rubutu yana cikin hanyoyin da ake sanin tarihin al’umma da wanzuwarta, marubuta sun bayar da gudunmawa a tarihin al’ummar Hausawa da asalin ta.
2.3 Haɓaka adabi
Rubutun zube ɗaya ne daga cikin rassan adabi guda uku. A wannan zamanin rubutattun ƙagaggun labaru shi ne kan gaba a tsakanin rukunan adabi guda uku. Marubuta sun bayar da gudunmawa wajen haɓaka adabin Hausa.
2.4 Wayar da kai
Hukumomi da ƙungiyoyin sa kai na ciki da wajen ƙasar nan sun sha yin amfani da marubuta ta hanyar rubutun su don wayar da kan al’umma.
A 1929 gwamnatin ƙasa ta kafa Hukumar Fassara mai suna Translation Bureau ƙarƙashin Mr. C.E.J. Whitting don samar da littattafan karatu na Hausa, har zuwa kafa hukumomi irin su Norla da Gaskiya da NNPC don samar da littattafai waɗanda za a yi amfani da su wajen wayar wa da al’umma kai ta fuskoki daban-daban.
A nan baya-baya, akwai hukumomi da ƙungiyoyi irin su Bambaɗiyya da Gusau Institute da Ɗangiwa da BBC da Aminiya Trust da Alandalus da sauransu duk sun sa gasa don samar da labaru da marubuta za su bayar da gudunmawa wajen wayar da kan al’umma kamar na danne haƙƙin mata da ƙananan yara, ko na siyasa ko na taaddanci, ko na muhalli da sauransu.
Haka nan su kansu marubutan suna yin rubutun su don wayar wa da al’umma kai ta fanni daban-daban.
2.5 Nishaɗantarwa
Marubuta sun bayar kuma suna kan bayar da gudunmawarsu ta hanyar rubuce- rubucen littattafan ban-dariya da hikima da fasahohin Hausawa don nishaɗantar da al’umma.
2.6 Sanar da halin da duniya ke ciki
Littattafan Hausa na hikaya cike suke da labarun da duniya ke ciki, ta hakan mutane suke sanin irin rayuwar da ake yi a sauran nahiyoyi da qasashen duniya bakiɗaya.
2.7 Samar da ɗabi’ar karatu
Rubuce-rubucen Hausa sun samar da tarin littattafai waɗanda suka taimaka aka samu masu karatu da yawa; musamman mata da ƙananan yara. Littattafan sun haifar da ɗabiar karatu a bainar al’umma, ta yadda wasu ma ba su taɓa shiga makaranta ba, sai ta dalilin son yin karatun littattafan Hausa. Wasu ma littattafan ne suka zame musu makarantar koyon karatu.
2.8 Tattalin arziki
Rubutun marubuta kafin ya zama littafi yana da matakan ayyuka tun daga gyara (editing) zuwa bugun naura mai ƙwaƙwalwa zuwa sayen takardu da bugawa a injin bugu da haɗawa, hakan ya sa marubuta sun bayar da gudunmawa ta fuskar haɓaka tattalin arziƙin al’umma da na ƙasa, domin mutane da yawa suna samun kuɗaɗen shiga ta fuskar aikin littafi, haka ma gwamnati.
2.9 Mafita:
Marubuta suna bayar da gudunmawar samun mafita ga al’amuran rayuwar al’umma na yau da kullum da zamantakewa. A cikin waɗansu littattafan al’umma ke gano mafitar su a rayuwa.
Kammalawa:
Komai ya yi farko yana da ƙarshe. Tabbas idan aka ce za a bayyana ire-iren gudunmawar da marubuci ke bayarwa ga al’umma, to waɗannan yan takardu sun yi kaɗan, haka ni ma na yi tsururu in ce wani abu, kawai na tsakuro wasu ‘yan kaɗan daga bayanin da masana suka riga, suka yi a kan gudunmawar marubuta ga al’umma, fatana wannan rubutu ya haska mana tarin gudunmawar ta su, kuma su zama an ƙarfafa musu gwiwa su ma sun ƙarfafi gwiwoyin kansu, su ci gaba da bayar da gudunmawa ga alumma, Allah Ya yi mana jagora, amin.
Manazarta:
Bunza, A.M. (2002) Rubutun Hausa (Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa) Don Masu Koyo Da Koyarwa. Lagos, Ibrash Islamic Publication Centre L.T.D. Surulere.
Ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa. Zaria: Amana Publishers Limited
Gidan Dabino, A.A. (2006) Muhimmancin Marubuci A Cikin Al’umma. Takardar da aka gabatar a taron gangamin marubuta, wanda ƙungiyar Brigade Authors Forum suka shirya, ranar Lahadi 21-05-2006, a GGSS, Gama Tudu, Kano.
Indabawa, I.M. da Fagge, K.Y. (2014) Dabarun Rubuta Ƙagaggun Labarai. Kano, Gimbiya Publishers, Fagge.
M. Isa (2004) Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai. Kano, Usman Alamin Publishers.
Muhammadu, Y. M. (2005). Adabin Hausa. Zaria: University Press Limited.
Yahya, I.Y. (1988). Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, Zaria: NNPC.
Zarruƙ R.M. da wasu (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire (Littafi na Biyu) Ibadan: University Press Limited.
Kabiru Yusuf ɗalibi ne a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero da ke Kano.