Labarai

‘Yan sanda sun damƙe ɗan shekara 25 bisa zargin yin lalata da akuya a Jigawa

‘Yan sanda sun damƙe ɗan shekara 25 bisa zargin yin lalata da akuya a Jigawa

'Yan sanda a Jihar Jigawa sun damƙe wani ɗan shekara 25 kan zargin yin lalata da akuya a yankin Ƙaramar Hukumar Gwaram da ke jihar. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, shi ne ya bayyana aukuwar hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse a ranar Juma'a. A cewar jami'in 'yan sandan, sun cafke wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 1 na dare sa'ilin da suke sintiri a bakin aiki a cikin garin Gwaram. Ya ce, wanda ake zargin mazaunin Kunnadi kwatas ne, kuma an kama shi ne a daidai lokacin da…
Read More
Yadda Kwankwaso ya juya wa gayyatar EFCC baya

Yadda Kwankwaso ya juya wa gayyatar EFCC baya

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ƙi amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa a makon jiya don amsa mata tambayoyi. EFCC ta gayyaci Kwankwaso ne don ya amsa mata tambayoyi kan zargin da aka yi masa na amfani da ofishinsa wajen aikata ba daidai ba, karkatar da kuɗaɗen jiha, nauna rashin adalci wajen rabon gidajen gwamnati a lokacin da yake riƙe da kujerar Gwamnan Kano. A cewar majiyar MANHAJA, a ranar Alhamis da ta gabata EFCC ta buƙaci Kwankwaso ya bayyana a babban ofishinta da ke Abuja amma ya yi biris. Jaridar Platinum Post ta rawaito cewa,…
Read More
Dalilin da ya sa ɗan gidan Ganduje, Abdulazeez ya haɗa mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje da EFCC

Dalilin da ya sa ɗan gidan Ganduje, Abdulazeez ya haɗa mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje da EFCC

A makon da ya gabata ne hukumar EFCC ta gayyaci matar Gwamnan Kano, Hajiya Hafsat Ganduje, zuwa ofishinta da ke Abuja don ta amsa mata tambayoyi masu alaƙa da zargin rashawa, amma ta ƙi amsa gayyatar. A cewar jaridar Premium Times, Abdulazeez Ganduje, ya haɗa mahaifiyarsa Hafsat Ganduje da EFCC ne bisa zargin tana amfani da dukiyar ahalinsu wajen azurta kanta. A cewar wata majiya wadda ta samu zarafin leƙa takardar ƙorafin da Abdulazeez ya rubuta a kan mahaifiyarsa, ta ce Abdulazeez ya nuna yadda wani ɗan kwangila ya same shi a kan ya taimaka masa wajen sayen wasu filaye…
Read More
Rashin bin doka: Majalisa ta bai wa Ganduje sa’o’i 48 kan ya tsige Shugaban Hukumar Haraji na Kano, AbduRazak Salihi

Rashin bin doka: Majalisa ta bai wa Ganduje sa’o’i 48 kan ya tsige Shugaban Hukumar Haraji na Kano, AbduRazak Salihi

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bai wa Gwamna Umar Abdullahi Ganduje wa'adin sa'o'i 48 kan ya tsige Shugaban Hukumar Tara Haraji na Jihar, AbduRazak Salihi, daga muƙaminsa bisa laifin saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma rashin girmama majalisar da ya yi Bayanai sun nuna Salihi ya ƙi bayyana wa Majalisar matsayin harajin da hukumarsa ta tara wa jihar duk da buƙatar hakan da Majalisar ta nuna masa, maimakon haka sai ya rubuta rahoto kan harajin tare da miƙa shi ga gwamnati ta hannun Babban Sakataren Hukumar Kula da Filaye ta jihar. Kazalika, Majalisar ta hannun shugabanta Engr. Hamisu…
Read More
Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya don kinkimo bashin biliyan $4 da miliyan €710

Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya don kinkimo bashin biliyan $4 da miliyan €710

Duk da ƙorafe-ƙorafen da 'yan ƙasa ke yi game da yawan bashin da gwamnati ma ci ta ciyo, Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa da ta amince masa kan sake kinkimo bashin Dala biliyan 4 da Euro miliyan 710 daga ƙetare Buƙatar Buhari na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattatawa, wanda shugaban majalisar ya karanta ta a zauren majalisar a ranar Talata. A cewar Buhari, za a biya bashin da ake shirin karɓowa ne ta hanyar samo wasu basussukan daga Bankin Duniya da Cibiyar French Development da Bankin EXIM da kuma IFAD. Ya…
Read More
Bankin CBN: Jagorancin Emiefele ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasa – Kakakin Majalisar Matasan Arewa

Bankin CBN: Jagorancin Emiefele ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasa – Kakakin Majalisar Matasan Arewa

An bayyana cewa muddin ba a yi abin da ya kamata ba a kan lokaci, Nijeriya za ta faɗa cikin wani mawuyacin hali ta dalilin shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emiefele. Kakakin Majalisar Matasan Nijeriya, Mohammed Salihu Danlami shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin. Ɗanlami ya ce, Godwin Emiefele shi ne mafi munin abin da ya taɓa faruwa ga Nijeriya da tattalin arzikin ta, duba da yadda sha'anin tattalin arzikin Nijeriya ke fuskantar koma-baya, musamman yadda darajar kuɗin ƙasar ke ta ja baya. Ya ce Emiefele mutum ne mai…
Read More
Harin ‘yan bindiga: Fursunoni 240 sun tsere daga gidan yarin Kogi

Harin ‘yan bindiga: Fursunoni 240 sun tsere daga gidan yarin Kogi

Bayanai daga Jihar Kogi na nuni da cewa, aƙalla fursunoni 240 ne suka tsere sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai a matsakaicin gidan yarin da ke Kabba a jihar. Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yari na ƙasa, Mr Francis Enobore, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ran Litinin, inda ya ce an kai harin ne da tsakar daren Lahadin da ta gabata. A cewar jami'in, 'yan bindigar waɗanda ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari gidan yarin ne ɗauke da manyan makamai wanda ya…
Read More
An kuɓutar da ɗaliban Zamfara daga hannun ‘yan fashin daji

An kuɓutar da ɗaliban Zamfara daga hannun ‘yan fashin daji

Kimanin ɗalibai 70 na Makarantar Sakandare da ke Ƙaya cikin yankin Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara aka ceto daga hannun 'yan bindiga a ranar Lahadi. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 1 ga Satumba rundunar 'yan sandan Zamfara ta tabbatar da an yi garkuwa da ɗalibai 73 a jihar. Sai dai, a ranar da aka kwashi ɗaliban ba da jimawa ba biyar daga cikinsu suka kuɓuta. Lamarin da ya sanya gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya ɗauki matakin rufe dukkan makarantun firamaren da sakandaren jihar. Tare kuma da kafa dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 6 na yamma zuwa…
Read More
HOTUNA: An yi fidda’un kwanaki uku da rasuwar Sarkin Kontagora, Alhaji Sa’idu Namaska

HOTUNA: An yi fidda’un kwanaki uku da rasuwar Sarkin Kontagora, Alhaji Sa’idu Namaska

A wannan Lahadin aka gudanar da addu'ar fidda'u na kwanaki uku da rasuwar marigayi Sarkin Kontagora, Alhaji Sa'idu Namaska a fadar masarautar. Taron ya samu halarcin jama'a da dama, na kusa da nesa, ciki har da Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, tsohon gwamnan jihar, Dr Mu'azu Babangida Aliyu, Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar da manyan 'yan siyasa da jami'an gwamanti a matakin ƙasa da jihohi. Yayin taron, Gwamna Sani Bello ya yi kira ga al'ummar Masarautar Kontagora da su ci gaba da yi wa marigayin da iyalansa da ma masarautar baki ɗaya addu'a, Kazalika, Bello ya buƙaci al'ummar masrautar…
Read More