19
Sep
Bayanan da suka riski MANHAJA a wannan lokaci, sun tabbatar da cewa tsohon mataimakin Babban Bankin Nijeriya (CBN), Obadiah Mailafia, ya kwanta dama. Mailafia ya rasu ne da safiyar Lahadi a Babbar Asibitin Ƙasa da ke Abuja, inda ya bar duniya yana da shekara 64. Marigayin wanda ɗan asalin yankin Kudancin Kaduna ne, masanin tattalin arziki ne wanda a halin rayuwarsa ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan Babban Bankin Ƙasa (CBN). A gaɓar ƙarshe ta rayuwarsa, Mailafia ya kasance 'yan kan gaba wajen sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro a matsayin tasa gudunmawa a fagen yaƙi da matsalolin tsaro.…
