Tsohon mataimakin shugaban Bankin CBN, Mailafia ya kwanta dama

Bayanan da suka riski MANHAJA a wannan lokaci, sun tabbatar da cewa tsohon mataimakin Babban Bankin Nijeriya (CBN), Obadiah Mailafia, ya kwanta dama.

Mailafia ya rasu ne da safiyar Lahadi a Babbar Asibitin Ƙasa da ke Abuja, inda ya bar duniya yana da shekara 64.

Marigayin wanda ɗan asalin yankin Kudancin Kaduna ne, masanin tattalin arziki ne wanda a halin rayuwarsa ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan Babban Bankin Ƙasa (CBN).

A gaɓar ƙarshe ta rayuwarsa, Mailafia ya kasance ‘yan kan gaba wajen sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro a matsayin tasa gudunmawa a fagen yaƙi da matsalolin tsaro.

Ba da jimawa ba hukumar tsaro ta SSS ta gayyaci marigayin don ya je ya yi ƙarin haske kan wasu kalaman da ya yi masu alaƙa da batun tsaro.