Kwalara ta halaka mutane 100 a Neja

Daga IBRAHIM HAMISU

Gwamnatin Jihar Neja ta ce fiye da mutane 100 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar annobar amai da gudawa cikin watanni huɗu.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Muhammad Makunsidi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar da ta gabata a Minna babban birnin jihar, yayin buɗe wani taron bada horo ga ‘yan jarida.

Kazalika ya ce, an samu ɓarkewar annobar ne a ƙananan hukumomin jihar 25.

Kwamishinan ya kuma ce, an samu wannan adadi ne tun lokacin da annobar ta ɓarke daga  watan Afrilun da ya gabata zuwa yanzu ne.

Haka kuma ya bayyana yawan yin bahaya a sarari a matsayin babbar hanyar afkuwar annobar, musamman a yankunan karkara da suke amfani da ruwan da ya gurɓace sakamakon irin wannan bahaya.

Dakta Muhammad Makunsidi, ya ja hankalin al’umma da su riƙa kare kansu daga kamuwa da cutar ta Kwalara.

Haka kuma ya shawarci mutanen da suka kamu da ita su tabbata sun je asibiti, domin karɓar magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *