HOTUNA: An yi fidda’un kwanaki uku da rasuwar Sarkin Kontagora, Alhaji Sa’idu Namaska

A wannan Lahadin aka gudanar da addu’ar fidda’u na kwanaki uku da rasuwar marigayi Sarkin Kontagora, Alhaji Sa’idu Namaska a fadar masarautar.

Taron ya samu halarcin jama’a da dama, na kusa da nesa, ciki har da Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, tsohon gwamnan jihar, Dr Mu’azu Babangida Aliyu, Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar da manyan ‘yan siyasa da jami’an gwamanti a matakin ƙasa da jihohi.

Yayin taron, Gwamna Sani Bello ya yi kira ga al’ummar Masarautar Kontagora da su ci gaba da yi wa marigayin da iyalansa da ma masarautar baki ɗaya addu’a,

Kazalika, Bello ya buƙaci al’ummar masrautar da su kwantar da hankulansu tare da va su tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba za a soma shirye-shiryen zaɓen sabon sarki.