24
Aug
'Yan bindiga a Jihar Filato sun kashe jami'in ɗan sanda da wasu mutum takwas a yankin Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar.Ɗan sandan da aka kashen mai suna Abdulrahaman Isah, shi ne kwamandan runduna ta musamman da Sufeto-Janar na 'Yan Sanda (IGP) ya kafa mai zamanta a Mangu. Harin wanda ya auku a ranar Litinin da ta gabata da yamma kusa da ƙauyen Ƙwai, ya rutsa har da wani ɗan bijilanti mai suna Hassan Mohammed.Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Filato, Ubah Ogaba, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata. A cewar Ogaba: “A…
