Buhari ya bayyana waɗanda za su wakilce shi a wajen ɗaurin auren ɗansa da bikin sarautar Sarkin Bichi

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana sunayen tawagar da za su wakilce shi wajen ɗaurin auren ɗansa Yusuf Buhari da ‘yar Sarkin Kano, Zahra Bayero wanda za a yi a yau Juma’a a Kano.

Kazalika, tawagar ce za ta sake wakiltar Shugaban Ƙasa wajen bikin sarauta na Sarkin Bichi da zai gudana gobe Asabar idan Mai Duka Ya kai mu.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis.

Shehu ya ce, tawagar za ta wakilci Shugaban Ƙasa ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Kamar yadda sanarwar ta nuna, tawagar na ƙunshe ne da jiga-jigan gwamnati da suka haɗa da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (mai murabus), Ministan Harkokin Gona, Alhaji Sabo Nanono, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, Ministan Albarkatun Ruwa, Engr. Suleiman Hussein Adamu da kuma mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu.

A cewar sanarwa, bayan kammala ɗaurin auren Yusuf da Zahra, tagawar za ta ci gaba da zama a Kano har zuwa Asabar don halartar bikin sarautar Sarkin Bichi.