Zuwan Buhari jinya a ƙetare ba gazawa ba ne ga fannin kiwon lafiyar Nijeriya, cewar Lai

Ministan Yaɗa Labarai da Raya Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa tafiya ƙetare da Shugaba Muhammadu Buhari kan yi don kula da lafiyarsa, hakan ba yana nufin fannin kiwon lafiyar Nijeriya ya durƙushe ne ba.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin tattauna da wasu manyan kafafen yaɗa labarai na duniya da suka haɗa da BBC da Bloomberg da kuma Politico, a Amurka.

Kamafanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, Minista Lai ya ziyarci Amurka ne don ganawa da manyan kafafen yaɗa labarai kan abin da ya shafi irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu da kuma ƙoƙarin da take yi wajen daƙile matsalolin ta’addanci, satar mutane da sauran nau’ukan manyan laifuka.

Da yake tattaunawa da NAN bayan kammala ganawa da kafafen yaɗa labarun, Lai ya ce Shugaba Buhari na da damar ya zaɓi likitan da zai duba shi, tare da cewa ba kansa farau ba dangane da abin da ya shafi zuwa neman lafiya a ƙetare.

a cewarsa, “A matsayina na Ministan Labarai da Al’adu, in ya kasance tun farko ina da tsayayyen likita mai duba lafiyata, ba na tunanin hakan zai sauya wai don na zama minista.

“Ba tare da la’akari da likitan ko ɗan wane ƙasa ne ba, saboda ra’ayina ne in zaɓi likitan da nake so ya riƙa kula mini da lafiyata.

“Kamar yadda na faɗa musu, Buhari ba shi ne Shugaban Ƙasa na farko da ya soma zuwa jinya a ƙetare ba.


“Idan ya zamana cewa Buhari na da likitan da ya saba kula da sahi sama da shekaru 30 da suka gat
bata, wanda ya fahimci matsalolin lafiyarsa, mene ne ya sa batun neman lafiyarsa zai zama abin muhawara.”

Ya ci gaba da cewa, duk da ƙalubalen da fannin lafiyar ƙasa ke fuskanta, fannin bai cancanci a nasabta shi da durƙushewa ba.

Ya ce duk da sukar da fannin ke sha a wajen wasu ‘yan ƙasa, hakan bai hana Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ayyana Nijeriya a matsayin ƙasa ta huɗu  a faɗin duniya a fagen ɗaukar yaƙi da cutar korona da muhimmanci ba.