Kasuwanci: Matakan dawo da martabar Kano da Buhari da Ganduje ke bi

Ƙaddamar da aikin aikin shimfiɗa layn dogo daga Kano zuwa Kaduna, wanda Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a kwanan nan da kuma ƙaddamar da gada mai hawa uku, wacce Gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, alama ce ta yadda Buhari da Ganduje ke fafutukar ganin sun dawo da martabar Kano a idanun duniya bakiɗaya ta fuskar kasancewar ta jagabar kasuwanci a yankin Afrika ta Yamma.


Layin dogon na daga cikin wani ɓangare na aikin tabbatar da shimfiɗa shi daga Kano zuwa Legas, inda a ka fara aikin shimfiɗa gadar jirgin ƙasa ta zamani daga Abuja zuwa Kaduna da kuma Legas zuwa Ibadan, wanda shi ne zai taso ya haɗe da Abuja, sannan daga Kaduna ya dangana da Kano. Tuni dai an ƙaddamar da aikin Abuja zuwa Kaduna a watan Yuli na 2016, yayin da na Legas zuwa Ibadan kuma a watan Yuni na 2021.

A yayin da ya ke ƙaddamar da aikin a Kano, Shugaba Buhari ya ce, an kafa tashar jirgin ƙasan ne a kusa da tashar sauke kayan da aka sauke daga teku ta Dala Inland Dry Port da ke Birnin Kano bisa hikimar sauƙaƙa jigila da bunƙasa kasuwanci a yankin. Shugaban Ƙasar ya ce, gwamnatinsa ta lura da sufurin jirgin ƙasa a matsayin wata babbar hanyar bunƙasa tattalin arziki. Don haka ne ta bai wa fannin muhimmancin gaske.

“Ƙaddamar da aikin wannan ɓangaren na layin dogo daga Legas zuwa Kano a fili ta ke ya nuna mayar da hankalin gwamnatin ta hanyar farfaɗo da tsarin sufurin jiragen ƙasa, domin rage tangarɗar sufurinmu ko domin ma jin daɗin matafiya a cikin faɗin ƙasar,” a ta bakin Buhari.

“Wannan aikin yana da muhimmanci wajen saita harkokin sufuri daga Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja a lokaci guda, wanda hakan ke nufin layin dogon ya haɗe manyan biranen kasuwancin na Kano da Kaduna da Babban Birnin Tarayya Abuja. Bayan an kammala wannan aikin za kuma a samar da tashar jirgin ruwa ta Legas mai cibiya a Kano, wacce masu shiga da fita da kaya a cikin ƙasar daga Jamhuriyar Nijer za su more ta.

“Wannan zai samar da alheri mai yawa ta fuskar samar da tattalin arziki ta hanyar samar da aikin yi daga sababbin kasuwanci da damar cinikayya da kuma ƙirƙirar yalwa. Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya tana nan tana aiki, don ganin ta samar da haɗin gwiwar masu ɗaukar nauyi ta hanyar cimma yarjejeniyar bunƙasa layin dogo daga Kano zuwa Ibadan da kuma faɗaɗa harkokin ku]i a cikin aikin.

“Za a haɗa layin dogon da tashar jirgin ruwa ta biyu da ke Legas, wato Tashar Tin Can Island. A na tsammanin tabbatar da aikin tashoshin jiragen ruwa na kan tsandauri da suke a kan hanyoyin da layin dogon zai bi daga Kano zuwa Legas. Don haka kenan tashoshin tsandaurin za su riƙa samun kaya kai-tsaye daga kasuwannin ƙasashen waje, kamar yadda ake sauke kaya a tashoshin jiragen ruwa da ake da su a yanzu.

A nasa jawabin, Mnistan Sufuri na Nijeriya, Rotimi Amaeshi, ya ce, tashar jirgin ƙasa ta Zawachiki a Birnin Kano za ta zama tashar jiragen ƙasa mafi girma a Nijeriya, idan an kammala ta, inda hakan ke nuna irin fifikon da Gwamnatin Shugaba Buhari ta bai wa Kano ta fuskar dawo da martabarta a idanun duniya ta fannin harkokin kasuwanci.

“Aikin zai bunƙasa rayuwar al’ummomin da suke ciki tsundum, zai samar da aikin yi, inda za mu ɗauki aƙalla mutane 20,000 aiki. Aikin tashar kuma zai tallata harkokin kasuwanci. Kazalika, a nan gaba tashar za ta taimaka wajen sauwaƙa cunkoson tashoshin jiragen ruwan Legas da kuma cikakken cin moriyar tashoshin tsandauri na Ibadan, Kaduna da ita kanta Kano ɗin.

“Layin dogon Ibadan zuwa Abuja kuma zai haɗe tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya da Maraɗi da ke Jamhuriyar Nijer, wanda na tabbata zai bunƙasa kasuwanci da yauƙaƙa tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.”

Bugu da ƙari, Minista Amaechi ya ƙyanƙyasa albishir ɗin cewa, ba da jimawa ba Gwamnatin Tarayya za ta gina ƙarin layin dogo, wanda zai haɗe jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da sauran digar jiragen ƙasa na ƙasar.

“A yanzu haka mu na tsumayin sahalewar Majalisar Dokokin Ƙasa, domin amso bashin ci gaba da aikin layin dogo wanda ya tashi daga Fatakwal zuwa Maiduguri. Aikin zai haɗe Fatakwal, Aba, Umuahia, Inugu, Markurɗi, Lafiya, Jos, Kafanchan, Kaduna, Bauchi, Gombe, Damaturu, Gasua, da kuma Barno.”

Baya ga batun sufurin jirgin ƙasa kuma, Shugaba Buhari ya ƙaddamar da sabuwar gada mai hawa uku a Birnin Kano, wacce Gwamnatin Ganduje ta gina, domin sauƙaƙawa da magance matsalolin cunkoson hanyoyi na ababen hawa a birnin, inda gadar, wacce aka fi sani da Gadar Dangi, ta ke a kusa da bayan sakatariyar jihar.


Kan hakan, Shugaba Buhari ya yaba wa Gwamna Ganduje bisa ci gaba da gudanar da ayyukan da ya gada da ma ƙirƙirar sababbi fil, kamar ita wannan gada, wacce babu irin ta a dukkan faɗin Arewa. Daga nan sai Shugaba Buhari ya yaba wa Ganduje bisa kankaro jihar da fito da kyawunta da martabarta a ƙasa bakiɗaya. Sai ya nuna farin cikinsa da irin ayyukan da gwamnan ke ci gaba da aiwatarwa a faɗin jihar, yana mai ƙarawa da cewa, wannan ce kaɗai hanyar da za a iya nuna yadda ake kashe kuɗaɗen baitulmalin al’umma daga waɗanda suka bai wa amanar gudanar musu da shi.

Su dai waɗannan ayyuka da ake gudanar wa Birnin Kano, zai dawo da martabar birnin ne ba wai kawai a Arewa ko Nijeriya kaɗai ba, a’a, har ma da Afrika ta Yamma, domin aƙalla ƙasashe 15 za su amfana da layin dogo da ake yi a birnin, inda kuma hanyoyi masu kyau da gadoji za su taimaka wajen sauƙaƙa harkokin kasuwanci a birnin, musamman ga baƙi ’yan kasuwa.

Don haka Shugaba Buhari ya cancanci yabo bisa ƙaddamar da wannan aiki na layin dogo a Kano, haka nan shi ma Gwamna Ganduje ya dace a yaba masa bisa namijin ƙoƙarin da ya ke yi wajen ganin ya inganta hanyoyin jihar ta yadda nan gaba za a fa fa’ida da cin moriyar waɗancan ƙofofi da Gwamnatin Buhari ta buɗe.

Idan martabar kasuwanci da masana’antu ya dawo a Kano, ko shakka babu Arewa da al’ummarta ne za su fi kowa amfana da cin moriyar hakan. Don haka yabon gwanaye ya zama dole!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *