Azabtar da ‘ya’yan miji da sunan kishi

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

‘Ya’yan kishiyoyi: Yau zan yi magana akan zaman kishi, ma’ana yadda wasu matan ke mai da yaran kishiyoyinsu bayi ko su fifita nasu a kan na kishiyarsu da ba sa tare. Wasu ma suna tare da iyayen yaran, amma ba su da kataɓus a gidan. Wala’alla ta fi ƙarfin mijin, bai da yadda zai yi da ita, sai abin da ta ce. Ko kuma ta shiga ta fita ta raba uban da yaransa, bai ganin komai sai ita sai yaranta. Wannan ɗabi’a ta zama jiki ko na ce ta jima tana yawo gidajen masu mata fiye da ɗaya.

Mata ikon Allah! Mu fara tunawa shi ]a amana ne a gurinmu. Idan mun kyautata musu, to kanmu muka kyautata wa. Idan mun bijire, to fa za mu tsinci abun mu da muka shuka, wallahi. Ba za a ce dole abinda ka yi wa ɗanka ba za ka wa ɗan wani ba,  a’a ruwanki ki kyautata musu gabaɗaya ko don ki samu rabo a lahira.

Mata da yawa na wahalar da yaran miji da sunan kishi saboda ba nasu ba ne, suna jin daɗi. wannan ba ɗabi’a ce mai kyau ba. Duk wanda ya wahalar da ɗan wani, Allah zai wahalar da nasa. Wallahi mata mu kiyaye shiga haƙƙin Allah. Ita kanta rayuwar ba ta da tabbas. Duk wanda ya samu dama, to ya kasance yana gwada adalci, don kai ma ba ka san inda naka zai je ba a gaba.

Kishiya; Dole ce idan har Allah ya haɗa ku zama to ki karɓi ƙaddaraki, kuma gode Masa. Ki yi ƙoƙarin zaman lafiya da ita da mijin yadda yaranku za su ta so su yi koyi da ku. Ba ruwan yaro da cewa ba kya son ɗan ɗaya abokiyar zamanki. Wani sa’in kuma miji ke jawo rashin zaman lafiya don ya fi d son ɗaya daga cikin matansa, sai ya fifita yaranta fiye da sauran. Hakan yana jawo kan yara ya rabu, kuma su tashi da ƙin juna. Wannan ya yawaita a gidaje.

Ɗan kishiya ko ‘yar kishiya; Waɗannan su ne babbar matsalar. Da zarar uwa ta bar gida an danƙa wa ɗaya rikon yaran, sai ta nuna ita fa bata san magana ba, ba za ta riƙe ba. Ko ba za ta kula da su ba don ba nata ba ne. Idan miji ya kafe ya nuna mata jan ido, sai ta sake salon duka ko zagi. Ya Allahu wannan wacce masifa ce muka ɗora wa kan mu? don Allah mata meye ribarmu ta cusguna wa ɗan miji, don Allah?

Iyaye maza kuna ba da gudunmawa sosai ta ruguza gidanku. Da zarar ka ba wa ɗaya mukullin kula da gida bisa rashin adalci, to wallahi ka taro katon ‘match’ wanda daga baya za ka zo kana kuka da idanunka.

Tuwon girma; Hausawa sun ce “tuwon girma, miyarsa nama”. Haka maganar take. Idan har ka so ɗan wani kamar yadda za ka so naka, to kai ma wallahi dole naka a girmama shi. Wasu matan na kamantawa wasu kuma sun mai da yaran miji tuwon toshe; su ne ɗiban ruwa naki na kwance, wanke-wanke, shara, girki, wanki, gyaran gida, kaf ki tura wa yaran miji, ke naki na zaune. Ya Allahu, kai kuma uba ba ka bincike yaya yaranka suke. Wasu ma gaya maka laifinsu na ƙarya ake, sai ka bi kai ka zauna kana hura hanci. Ka hau kai, ka yi ta masifa in ta kama har da bugu.  Wannan ba dai-dai ba ne. Ka sa ido sosai kan rayuwar iyalinka. Muddin ka yi sake, wallahi za ka ji kunyar yaranka a gaba.

Rashin kulawa; Wasu iyayen ba sa kulawa da rayuwar gidansu, ko da kuwa yara sun kawo kukansu. Maimakon ka mai da hankali ka ji meke damunsu, sai ka kore su ko ka ƙaryata su. Wannan kuskure ne babba gare mu iyaye.

Mu ja yaranmu a jiki ko da uwarsu ba kwa tare, ku ji meye yake samunsu bayan ba ka nan. Hakan zai sa ka zamo uba na asali, kuma mai  son yaransa.
Kyautatawa; Kyautatawa tana ƙara danƙon ƙauna tsakanin mata da miji. Idan za ka zamo namijin tsayayye kuma adali, to sai ka kyautatawa ko wacce mace da yaranta. Babu bam-bamci tun da duk kai ka tara su. Me zai sa ka ce ɗaya ta fi ɗaya? Dole da ma cikin matanka a samu wacce ka fi so.

Wala’alla ta fi kyautata maka ne. to ku yi abinku a sirri. Kada ka zamo mai wariya cikin iyali. Hakan ya a jawo ƙiyayya tsakanin mata da yara.  Shikenan sai ka ga kowa daga shi sai ɗan ɗakinsu kawai ya sani. Bisa dalilin ka nuna ba ka son uwarsu, su ma an ƙullah musu ƙin junansu. Don Allah iyaye maza ku kula da tarbiyyar iyalinku, kar a nuna fifiko.

Gasar haihuwa ba tarbiyya: Wasu matan kawai gasar haihuwa ake kawai don ta fi kishiyarta yara ta samu gado. kai! wannan ba ƙaramin kuskure ba ne. Idan kin haihu, ta haihu da yawa ta yaya za a tarbiyyar yaran? Shi ya sa namiji yake rasa inda zai yi da ransa ga yara rututu cin yau da gobe ma na neman gagarar su.  amma sai haihuwar ake, sai a saki yara sakakka kowa da rayuwarsa, Uba nauyi ya yi masa yawa, cin yau bana gobe, babu kudin omo da sabulu, babu ilimin boko da Arabiyya. Duk wannan masifar da miji ke ciki, ita matar hangenta dole gadonta ya fi na ɗayar, ta manta ma bai da komai.
Yanzu inda rayuwa ta yi tsada an san ci da sha na Allah ne, to amma don Allah tarbiyya fa?

A yi ta haihuwa ana rasa yadda za a yi da su. Daga karshe a haifi annoba. Uba na gani ɗansa na shaye-shaye ba shi da damar hana shi. Yarinya na yawon banza,  uwa ko uba na tsoron yi mata magana, to ta yaya rayuwar za ta inganta?

Raba abinci; Muddin kuna gida ɗaya da matanku to a haɗe abinci ba kowa ta yi nata ba. wannan fa ware kan iyali ne. Zumuncinsu zai yi ƙasa, wallahi. Amma in ana haɗa abinci, to zaman lafiya zai samu ko da kuwa ba a samu Yadda ake so ba, to dai za a samu sausauci. Amma idan kowa nasa zai yi, daga ita sai yaranta, to akwai sauran rina a kaba. Kowacce irin tarbiyya ce daga iyaye take samuwa. Wasu zavka gan su kamar uwa ɗaya, uba ɗaya. Wasu ba a gane ma wancan da wancan ba ɗakinsu ɗaya ba. Amma idan zaman lafiya ya yi ƙaranci  komai zai iya faruwa.

Wasu iyayen ma gida ɗayan ake, amma ba a magana. Gaba ta masifa ake a gidan. Wannan kuskure ne babba da cutarwa. Ko a yi ta gasar haihuwa, wai saboda gado, waiyazubillah! Ina za mu kai wannan? Da ba a aure biyu ko fiye da haka wasu da ba a wa iyayensu ba. Wata mata huɗu ne a gidansu, amma wallahi ta fi kowa zaƙewa da fitinar ba ta son kishiya. Mata iyayenmu, to ba a yi ke aka yi a gidanku?

Haihuwa; Haihuwa lallai kyautar Allah ce, ba kuma laifi ba ne a haihu.  sai dai a yanayin rayuwar yanzu sai an yi taka-tsan-tsan.  Yaran kasa kulawa da iyaye suke yi da su. To ina amfanin baɗi ba rai? ka rasa kwanciyar hankali da za ka ba su tarbiyya. Ka kasa ba su haƙƙinsu na ‘ya’ya. Su ma su gaza yi maka biyayyah, an ɓata goma ɗaya ba ta gyaru ba kenan. A haifi Wanda za a iya tarbiyyantarwa. Saboda kowanne ɗa a gurin iyaye amana ne. Allah ya ba mu ikon gane gaskiya.

Iyaye mata; Mu ji tsoron Allah Mu gane cewa kacokan rayuwar yaranmu da mazajenmu duk haƙƙinmu ne mu kula da hakan saboda mu mata mun fi zaman gida da gane matsalolin gidan fiye da iyaye maza. Kamar yadda na faɗa a baya, maza su taimakonmu suke yi. Dalilin ba mazauna ba ne. Abun da za mu sani a kan yaranmu su ba za su sani ba. Sai idan har mun faɗa musu. Hatta shi kansa namijin, wani abun sai mace ta nusar da shi yadda zai yi. Ba don bai sani ba, a’a sai dai don wani abun ke kin fi shi hange akai. Wala Alla akan gidansa, ko maƙocinsa, ko danginsa, dole sai kin nusar da shi zamtakewa.

Kula; Ya zama dole Musa kula da lura ga rayuwar gidajenmu, yaranmu. Saboda duk yadda kika tafiyar da rayuwar yau da kullum cikin gidanki, to da hakan za ki gane kura-kuran da yaranki ko ke kanki, ko mijinki, ko ma wani baƙo ke gudana, har ki yi shimfiɗa tarbiyya a ciki. Muna da aiki sosai a gabanmu, mata.

 Babu murna don kin ga miji ya saki matarsa abokiyar zamanki, ta bar miki yaranta. Ke kuma kina ta murna dama ta samu da za ki cusguna musu. Babu wani abun burgewa a ciki. Wallahi sai tarin zunubi da wahala. ki ƙi su, Duniya ta so su. Ke kuma daga baya abun ya koma kanki. Idan irin mai son aure-aure ne, gobe wata zai ɗebo miki, ta zo ku yi ta gwabzawa. Abun da kike so na zama mowa a gidan baki samu ba. Ita da ta shigo wallahi ta gaske gida da mijin har yaran naki ,kina ji kina gani kuma ba yarda za ki yi. Lokacin za ki san ashe abun da kika shuka, za ki girba.

Mazaje, ku ji tsoron Allah kuma ku daina yi wa gidajenku riƙon sakainar kashi. Da sannu za ku girbi abunda kuka aikata. Allah ya sa mu gane, mu gyara mu kula da cewa shi aure don kwanciyar hankali muka yi ba abun wasa ba ne. Abu ne na a ji da ɗi a bauta wa Allah. Yadda yaranmu za su amfana su ƙara ilimi a kan ayyukka nagartattu fiye da ]iban magana da sharholiya.

Ma sha Allahu, Allah ya sa abunda muka yi na daidai ya amfane mu. Kuskure ciki, Allah ya yafe mana. Muyi aiki da zuciyoyinmu na gari. Allah haɗa mu sati na gaba. Shawara, da gyara duk ƙofofinmu a bu]e suke. Ina godiya da irin addu’ar da kuke min Allah ya sa mu dace.