Tsufa

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki.

Yau insha Allah,  zan magana ne akan tsufa. Malam bahaushe ya na cewa: “Tsufa Labari”. To yau idan Sarkin ya so, labarin zan Baku. Da fatan za ku gyara zama domin yin karatu cikin nutsuwa.

Shi ɗan Adam, tun lokacin da Allah ya halicce shi, kullum cikin sauyi yake. Fatarsa, ƙashinsa, ɓargonsa, jininsa, da makamantansu ana sauya su daga lokaci zuwa lokaci. Wato yayin da su ka tsufa, ko kuma aikin su ya ƙare. Misali: jajayen ƙwayoyin jini ana sabunta su ne duk bayan wata uku; fata kuma (gaba ɗaya fatar jikin mutum) ana sauyata duk bayan shekara bakwai. To amma a yayin da sauyin ke faruwa, sababbin halittun da aka samar ba za su kai ƙarfi da ƙarkon waɗanda suka mutu ba.

Babban abin da ke kawo tsufa shi ne shuɗewar lokaci. Na biyu kuma shine yawan kwafi da ƙwayoyin halittar jiki ke yi. Bari na Baku misali: Mu ƙaddara ka ɗauki takarda original kai kaita wajen masu bizines Santa su yi maka kwafen wannan takarda. To bayan da su ka yi maka, sai ka ajiye original ]in, sannan ka miƙa kwafen ka ce a yi maka kwafenta ita ma. Mu ƙaddara haka kayi ta yi har zuwa lokacin da takardun za su ƙare. Ita wannan takarda original da ka bayar, ita ce a matsayin ƙwayar halitta ɗaya daga cikin biliyoyin ƙwayoyin halitta da ke jikin ɗan Adam.

Kwafen-kwafe kuma da aka ta yi maka, shi ne a matsayin yadda ƙwayar halittar Jikinka ke yi kafin ta mutu. Ma’ana, kafin ƙwayar halittar jiki ta mutu, a mafi yawan lokuta, sai tayi kwafe irin nata sak, sannan ta mutu. Idan da zan ce ka kwatanta original takardar da kuma kwafen da kayi na ƙarshe, za ka fuskanci cewa ta ƙarshen ta tsufa tukuf! To haka shi ma jikin fan Adam ya ke yi.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce :” Tsufa yana nufin sauye sauye da ake samu a jikin ɗan Adam tun daga haihuwarsa har izuwa mutuwarsa.” Wato a mahangar su, mutum kullum ƙara tsufa ya ke matuƙar rana za ta hudo kuma ta faɗi alhalin ya na numfashi.

Amma duk da haka, akwai shekarun da idan mutum ya kai su, shi da kansa ko ita da kanta za su fara ganin wasu alamu da ke nuna cewa lallai tsufa ya ƙwanƙwasa sofa. Zan kawo bayanin su ɗaya bayan ɗaya da yardar Allah. Kafin nan, ya na da kyau mu sani cewa tsufa ya banbanta daga mutum zuwa mutum, ma’ana wani na da saurin nuna tsufa wani kuma akasin haka ne. Wannan na da alaƙa da ƙwayoyin halittun gado da mutum da ya samo tun kaka da kakanni; shi yasa sai kaji ana cewa “ai wane ko wance tana kyan jiki.”

Bayan rawar da gado yake takawa a wajen bayyanar tsufa, akwai wasu abubuwan kuma da su ke da nasaba da tsufa. Misali: tsarin rayuwa, cima, muhalli, gwargwadon motsa jiki, da kuma yanayin tunanin da mutum yafi yi.

Tsarin rayuwa ya ƙunshi wasu jiga-jigan lamura da suka shafi rayuwa da lafiyar ɗan Adam kamar lokutan bacci, lokacin hutawa, lokutan aiki da sauran su. Za a samu a cikin mutane waɗanda ba su da tsarin tafiyar da akalar rayuwarsa, Wanda hakan ke sanya jiki cikin ruɗu da gajiya, wanda hakan ke barazana ga lafiya, kuma hakan na da alaƙa da saukowar tsufa kamar yadda bincike ya nuna.

Cima ita ma tana da rawar da ta ke takawa wajen samun ingantacciyar lafiya. Cima mai kyau tana da wanzar lafiyar jiki, kuma tana rage saurin bayyanar tsufa. Rashin cima mai kyau yana gadar da akasin haka. Cin muggan sinadaran da ake samu cikin abubuwa irin su taba, shisha, da gita suna matuƙar kawo saurin tsufa Wanda da turanci ake Kira da “premature ageing”.

Muhalli na tasiri ƙwarai a cikin samuwar tsufa. Mutumin da ya taso cikin muhallin da babu ilimi ba ruwan sha mai kyau, ba cima mai kyau, ba sauran abubuwan da ke inganta rayuwa da lafiya ba ɗaya su ke da Wanda ya taso cikin muhalli mai kyau ba. Rashin waɗancan abubuwa kan rage kuzarin ƙwayoyin halittar jiki, ta yanda garkuwar da su ke bayarwa za ta iya rauni, Wanda hakan ka kawo naƙasu ga cikakkiyar lafiya.

Rashin cikakkiyar lafiya kuwa na da alaƙa da saurin saukowar tsufa. Na tava kwanciya ɗaki ɗaya a asibiti ni da wani bawan Allah, kowa ya zo dubani sai ya ce masa :”sannu Baba”, bayan sun tafi sai yayarsa wadda ke jiyyarsa ta shaida mana cewa shekarar sa arba’in da biyu, kawai rashin lafiya ce ta sanya furfura ta baibaye ilahirin kansa!

Motsa jiki shima tasirinsa kamar sauran ne. Masu ɗabi’ar motsa jiki sun fi masu ɗabi’ar ci-ka-kwanta lafiya. Motsa jikin da su ke yi yana basu alfanu mai yawa, ɗaya daga ciki shi ne yana rage wasu kemikals zafafa masu ta’annati ga ƙwayoyin halittar jiki. Waɗannan kemikals ana kiransu da “free radicals” a turance, kuma haƙiƙa suna gajiyar da ƙwayoyin halitta kuma suna kawo saurin tsufa. A sanadiyyar haka, za mu iya cewa masu yawan motsa jiki sun rage wa kansu saurin saukowar tsufa fiye da sauran takwarorinsu wa]anda ba sa yi.

Na san wataƙila wannan zai ba ku mamaki.  Tunanin da ɗan Adam ke yawan yi na da alaƙa ya yanayin lafiyarsa da kuma gwargwadon saukowar tsufansa. Bincike daga asibitin Mayoclinic da ke Amurka ya nuna cewa mummunan tunani irinsu damuwa, tada hankali,da dugunzuma, ka  iya kawo matsaloli da dama ciki har da rashin isassshen bacci da sanya gajiya. Kuma kamar yadda nayi bayani a baya, kun ga yadda waɗannan abubuwa guda biyu ke bada gudunmawar su wajen wanzuwar tsufa.

In sha Allah a rubutu na gaba, zan kawo alamun da ke nuna cewa tsufa ya ƙwanƙwasa ƙofa. Kafin nan, Ina so na yi tambihi kaɗan. A ɗabi’ar ɗan Adam, ba ya son tsufa da nutsuwa, waɗanda kuma jarrabobi ne da basu da magani. Maƙasudin wannan rubutun shi ne ilmintarwa, da kuma bada haske kan abubuwan da ke kawo saurin tsufa waɗanda mutum zai iya yin wani abu a kansu. Allah ne masani!

Masu karatu ku tara mako mai zuwa da yardar Sarkin halitta.