Mahaifiya ta na yi wa waƙar ‘Ummi Mummina’ a lokacin da ciwon ta ya yi tsanani – Aminu Ladan Ala

*Har yau ji nake tamkar mahaifiya ta ba ta mutu ba – Aminu Ala

Kamar yadda dubban masoya Aminu Ladan Ala su ka samu labarin babban rashi da ya yi na mahaifiyar sa a ranar biyu ga watan Agustan wannan shekara, wato Hajiya Bilkisu Sharif Adamu Rijiyar Lemu. Tabbas wannan babban rashi ne da ilahirin masoyan sa su ka nuna alhini tare da addu’ar rahama ga mamaciyar. Duk da kalma ko jimla da za a iya amfani da ita gurin ban haƙuri ga wanda Allah ya jarabta da rashi irin wannan, Manhaja za ta yi amfani da wannan dama gurin miqa ta’aziyya ga mawaƙi kuma marubuci Aminu Ladan Abubakar Ala. Allah ya jiƙanta ya ba ku haƙuri. Shafin adabi na wannan sati ya samu damar tattaunawa da Alan waƙa akan rasuwar mahaifiyar tasa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Daga AISHA ASAS

Da farko dai za mu so ka fara da gabatar da kan ka.
Assalamu alaikum. Da farko dai sunana Aminu Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da Alan waƙa.

Kwanan nan Allah ya yi wa mahaifiyar ka rasuwa. Ko za ka iya ba mu labarin yananyin yadda Allah ya kawo ajalin na ta, shin ta yi rashin lafiya ne gabanin rasuwar ta zo?
To Alhamdu lillah. Yau kimanin kwana biyar kenan da rasuwar mahaifiya ta, wadda sunanta Hajiya Bilkisu Sharif Adamu Maidoki, kuma za a iya cewa ta na tare da jinya. Tun da ta na tare da lalura ta hawan jini, tsawon shekaru sama da arba’in, wanda dama ta na zuwa ganin likita a asibitin Aminu Kano, da sauran asibitocin da ta ke zuwa idan an yi yajin aiki. Shi mai cutar hawan jini ta na zuwa ne wasu lokuta, ko yayin vacin rai ne, ko yayin ganin wani abin damuwa, ko wani abu da ya tada hankali, ko kuma a’a ciwon kawai ya zo haka. Saboda haka wani lokacin za ka gan shi da lafiya ya na harkoki kamar sauran mutane. Ko lokacin da za ta rasu, ranar da za ta rasu ma ta je ziyara asibiti, to wanan ziyarar asibiti, dama mun san cewa duk sanda ta ga wani abu da ya tayar ma ta da hankali, to ciwonta na dawowa, don kwanaki ba a fi wata biyu ba maƙwabciyar ta aka hauro aka zo aka caka mata wuqa, to ta na da juna biyu, irin yadda ta ga maqwociyar nan cikin mawuyacin hali, to ita ma sai da ta shiga wani hali. Aka yi ta magani sannan aka samu kanta.

Haka ma shi wannan ɗan’uwana da ta je duba shi a asibiti, ta kama hannunsa ta na faɗin “Alhaji Ado ba zan iya tafiya in barka a halin da ka ke ciki ba. Ba kuma zan iya zaunawa ina kallonka a halin da kake ciki ba.” Haka ta ke faɗa kamar yadda su ka faɗa, sanda ta je dubiyar. Amma shi bai ma san ta na yi ba. To da ta dawo gida, ka ga ta dawo da wannan ta na jujuyashi a ranta, har ma ta shigo gida, ta je ta siyo waɗansu abubuwa da take da buqata, ta ɗora miya, ta yi miya ta gama, ta yi farfesu ta kai wa maqwabta wasu marayu nan. Ta dawo, to abincin da ba ta gama ba kenan, sai ta kwanta, ba a ma san ta mutu ba.

To ka ga akwai jinya ta hawan jini, sannan kuma a ranar ma ta je ziyara ta marar lafiya. A cikin kwanakin kuma duk ta kewaye ‘yan’uwanta na sauran garuruwa na vangarenta kenan. Ta je Rijiyar Lemu, har ta yi wasu isharori wanda daga baya suke faɗa. Akwai ƙaninta shi Shafir Muhammad, wanda ya ce ta kawo masa takardun gidan ƙaninsa, wanda yake ƙaninta ne, ta ce “wannan takardu ka ajiye su a hannunka saboda halin mutuwa”. Ya ce ba zan karɓa ba sai in Aminu ya na nan. Haka yake gaya mana a maƙabarta, ya ce sai in ina nan zai karɓi takardun. Sannan kuma tsakanin ziyartar da rasuwarta kwana biyu. Saboda haka wannan jinyar ce ta hawan jini, da kuma abubuwa da ta gani na damuwar ɗan’uwanta, wanda kuma shi ma bayan ta kwana uku da rasuwa shi ma Allah ya masa rasuwa.

Kuma sai aka yi wata sa’a da muka je inda aka yi ƙabarinta to na kusa da shi ne na ɗan’uwan na ta. Cikin wata ƙudurar Allah. To a bisa wannan jinyar ta rasu, kuma ta rasu ta na da ‘ya’ya guda biyu wanda su ke a raye, amma ta haifi ‘ya’ya sun kai biyar sun rasu, jikoki ta na da 25.

Shin kuna tare da ita ne ko kuwa ita kaɗai take zaune a wani gidan?
Gidanta daban, amma duk muna tare ne, don Katanga ɗai ce ta raba mu. Gidan da nake zaune da iyalina, akwai gidan da aka ware mata daban, amma duk Katanga ce kawai ta raba, sai dai ƙofar shiga gidanta daban ne. saboda in ta yi baƙinta, ko ‘yan’uwanta in sun zo za su zo gurinta su zauna gurinta.

Yaya mu’amalar ka da ita ta ƙarshe ta kasance?
Mu’amalar mu ta ƙarshe na je na bata kuɗin asibiti ne, saboda ta je asibiti kuɗin da na ke ajiyewa ya ƙare, saboda haka ta ce an biyo mu naira 6500. Na ce to ga kuɗin asibiti, ga kuma wasu kuɗin ki bayar in za ki koma asibitin a dubaki, idan lokacin da su ka baki ya yi. Saboda haka sannan na bata kuɗin cefane kamar yadda nake bata, saboda komai na ta daban take yi, haka ta fi so. Wannan shi ne hulɗarmu ta ƙarshe. Kuma mun yi tattaunawa kamar yadda muka saba tsakanin ɗa da uwa na tambayar lafiya, ya ake ciki da sauransu.

Yayin zaman makokin rasuwar mahaifiyar Aminu Ala

Ko za ka iya tuna wani canji da ka gani a tare da ita a ranar?
To ai ita kullum kamar yadda Malam ɗan’uwanta yake faɗa zuciyarta a karye take, kullum mace ce wadda take ganin kamar yau ko gobe za ta mutu, idan ba ka manta ba tsawon shekara goma na yi wata waƙa ‘Ummy Mummyna’, ‘that was’ 2006, a ciki ina rarrashinta a kan cewa “cuta yau cuta gobe ba mutuwa ba ce, cuta mai waraka ta zamo kaffara, cuta marar magani a cika da sa’ada, Allah sa a cika da imani da salama.” To ka ga baitin na ta ne, a lokacin ciwo ya mata tsanani, amma da Allah ya hore sai ya zama an gane in da matsalar ta ke. Duk sauran cututtuka babu sai wannan hawan jinin, wanda kuma aka ɗaurata kan magani, tana zuwa tana ganin likita. Da ba ta iya tafiya ta yi kazar-kazar irin yadda kowa ke yi, amma yanzu ta fi mu yawon zumunci ma.
Kamar yadda Malam ya faɗa, ga azumi su suna raraɓewa, suna bin inuwa, ba za su iya shiga rana ba saboda wahalar da za a sha in aka shiga rana da azumi, sai su ganta ita kuma ta zo ta kawo masu ziyara, da ɗan abubuwa na yara da ta ke rarabawa. Saboda haka ya ce, kullum maganarta nunawa take yi wannan rayuwa, wannan rayuwa, saboda ita kullum lafazinta kenan. Har ya ce, ɗan Adam yana da buri, har ba ya son a yi maganar mutuwa, to amma ita kullum shigen irin maganganunta kenan, kamar maganganu ne na bankwana. Saboda haka kaga kenan zuciyarta ta karye da duniya, kullum kamar a shirye take da mutuwa, saboda da aka duba ma kayan da ta ajiye ta tanadi turare da magarya da wasu abubuwa da duk za a kimtsa ta da shi ta tara har da zamzam. To zam zam ɗin ne ma aka nemi inda ta ajiye aka rasa, sai da aka je aka karɓo wani gidan sannan aka zo yi mata amfani da shi.

Me za ka ce ka fi tunawa da shi game da ita a yanzu da ta rasu?
Babu wani abu da za a ce me aka fi tunawa da shi, saboda a ko wane lokaci a tare ake da ita, saboda matsayinta mahaifiya na farko, sannan ni ina tare da ita, kuma ‘ya’yana ma suna hannunta, saboda haka to ka ga duk abin da za a ce ka tuna ko wane lokaci tana tare da kai ne a cikin zuciya. Saboda gani kake yi a koyaushe, ga shi dai zaman makoki muke yi yau kwana biyar amma har yanzu a cikin jikinka gani kake yi idan ka karya kwana ka shiga za ka ganta, har yanzu haka nake ji, ba ma maganar a tuno ba ne. Abin da aka manta ne ake tunowa, amma abin da yake tare da kai kullum gani kakeyi kamar ga shi, kamar ya na nan. Sai zuwa wani lokaci ne za mu shiga wannan yanayi na tunowa da ita, ko in mun rasa kaza sai mu tuno Hajiya, saboda ga wani abu da ita ta ke yi, sai mu tunota, da Hajiya tana nan da an yi kaza. To wannan abin sai a gaba ne za a same shi, amma a yanzu an yi mutuwar, mun tabbar an yi, an binne ta, an kai ta kushewa, amma har yanzu a jikin mu ji muke tana nan.

To mun gode.
Wassalamu alaikum.