Yadda kallon kitsen rogo ke rusa auratayya

Daga AMINA YUSUF ALI

Sannunku da jimirin karatun shafin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja! A wannan mako mun kawo muku yadda wasu ma’aurata suke yi wa aure kallon kallon kitse a rogo. Wanda abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen kawo rikici a gidajen aure har ma idan abu ya yi ƙamari ya kai ga rusa auren gabaɗaya. To wai meye kallon kitse a rogo?

Na san mai karatu zai so ya san ma’anar azancin maganar nan. Wannan azancin na nufin kamar yadda muka sani rogo yana da fari, musamman ɗanyensa idan aka ɓare shi. Daga nesa za ka gan shi fari sol har ɗaukar ido yake yana wani maiƙo kamar dai kitse yake. Amma daga ka matso kusa, sai zance ya sha ban-ban domin za a ganshi a bushe kuma ba zai kai darajar da ake tsammanin yana da ita ba a lokacin da ake hangensa daga nesa. To haka ma rayuwar aure a ƙasar Hausa.

Wato dai yanke hukunci da hange a zamantakewa ba tare da zurfafa bincike ba.

A ƙasar Hausa wani lokacin dalilai da yawa da suke jawo mutuwar aure shi ne yi wa aure kallon kitsen rogo. An kasa gane shi aure wani zama ne da ake fatan mutu-ka-raba wato da’iman. Ɗaukar aure akasin haka, matsala ce babba wacce za ta sa ya yi ƙarkon kifi. 

Da farko ba a shiga aure da gaskiya sai don hangen wani abu wanda ba shi ba ne. Mutane da yawa suna shiga gidan aure da nufin shaƙatawa da watayawa. An manta aure gidan bautar Allah ne. Kuma ita bautar Allah ba abu ce mai sauƙi ba. Eh an san ba wanda yake fatan ya samu matsala a gidan aure. Amma kuma ita matsala dole ce. Bahaushe ya ce: “zo mu zauna, zo mu saɓa”. Amma wasu sukan shiga aure da wannan zaton saboda yadda abokin rayuwar tasu ya ɗora su a keken ɓera ko igiyar zato.

Misali kamar wasu mutanen idan an zo maganar aure sukan yi wa wanda za su aura wata ƙarya har a ɗora shi a igiyar zato. Kamar maza sukan kwaɗaita wa mata wata rayuwa da ka san ba za ta ɗore ba. Ita kuma sai ta yaudaru da wannan abun, ta aure shi. Tana ganin mai ɗorewa ne. Haka wasu mazan a satittikan farko na aurensu sukan tarairayi mace su sangarta ta ko cimaka ma sukan ba ta wacce suka san za ta birge ta. Ita kuma sai ta afka cikin tarkon, ta yaudaru ta dinga ganin za a ɗore. Daga lokacin da abubuwa suka, canza sai rigima ta faru. Idan ba a ci sa’a ba auren ma ya ruguje.

Akwai kuma wani kallon kitsen a rogo da ma’aurata kan yi a kan rayuwar wasu ma’auratan. Wanda rashin godiyar Allah ne yake jawo hakan. Wasu ma’auratan sukan dinga hangen rayuwar wasu har ma su dinga shauƙin ina ma su ne. Har ma su dinga ta da wa abokan rayuwarsu da hankali a yi ta rigima kala-kala har ma a rusa auratayya.
 
Wasu ma fa kawai rayuwar da suke gani a akwatinan talabijin ɗinsu ko a littattafan ƙagaggun labarai da suke karantawa. Sai a ruɗe a raina ƙoƙarin wanda ake tare da shi.

An san cewa ana koyon wasu abubuwa na rayuwa da kuma zamantakewa a sashen adabi amma a sani, wasa daban rayuwar zahiri daban. Mata su suka fi yin wannan. Musamman masu ƙananan shekaru. Daga zarar mijinta ba ya yi mata irin rayuwar da ta ga mijin wata ƙawarta ya yana yi mata, ko yadda ta ga tauraron wani fim ko ƙagaggen labari yana wa matarsa ba, to za dinga ganin kamar ba sonta yake ba.

Haka shi ma namiji yana ruɗuwa da cika bakin abokanensa ko ‘yanuwansu maza. Su dinga cika bakin yadda suke tafiyar da rayuwar gidansu da yadda suke ɗaure wa matarsa ko matansa fuska da sauransu. Kai kuma sai ka yi sha’awa ka gwada a kan baiwar Allar matarka.

Haka su ma mata akwai ƙawaye da za su dinga cika muku baki mijinta ya yi mata kaza da kaza. Ya kashe mata kuɗaɗe kaza-kaza. Ko kuma ta dinga nuna irin yadda ta mallake shi yake mata biyayya da sauransu. Ko yadda take dila kishiya ko ‘ya’yan miji ke kuma ki yi sha’awa ki gwada a naki gidan kwaɓarki ta yi ruwa. Ki rusa aurenki idan ba ki yi sa’a ba.

Ko kuma ki hango ko ki ji labarin wata a wani tamfatsetsen gida ga motoci, ga daula. Ki dinga hangen ke ba ki yi sa’a ba, ki fitini kanki a banza. Wata ma sai ta kashe aurenta saboda wancan hange da take yi ya sa har ta dinga raina mijinta da dukkan samunsa da abubuwan da yake yi mata na kyautatawa.

Amma abinda muka kasa ganewa shi ne, shi fa rogo, rogo ne. Kitse ma, kitse ne. Duk yadda ya yi maka kyau daga nesa, sai ya ba da kai idan ka matso kusa. Don haka mu daina yaudaruwa da kallon kitse a matsayin rogo.

Sannann mun kasa gane cewa shi kowanne miji ko mata da irinsa. Kowanne mutum bai cika goma ba. Duk yadda abokin rayuwarku yake ɗan Adam ne. Dole akwai inda ya gaza komai ƙoƙarinsa. Ku daina hangen rayuwar wasu. Su ma yadda kuke sha’awarsu haka wataƙila suke ganin kamar ku ma ba ku da matsala.

Kuma kowanne ɗan Adam da tasa jarrabawar. Misali kamar matar nan da kuka gani tana fantamawa a cikin daular makeken gidan nan. Allah ne kaɗai ya san wacce jarrabawa Allah ya ɗora mata. Wataƙila akwai matsalar dangi ko na uwar miji da ba sa ƙaunarta, ko kangararren ɗa, ko rashin adalcin miji da sauransu. Amma ke ba ki yi tunanin komai ba sai daular da take ciki. To ki buɗe idanunki ki gane, wancan kitsen da kike hangowa mai yiwuwa rogo ne. Rogon ma busasshe mai ɗaci.
 
Haka wasu ma za su iya yi muku ƙarya su nuna muku sam ba su da matsala. Kamar wancan mijin da na kawo misalinsa a sama wanda yake cika baki a kan yadda yake dila iyalansa. Wataƙila ma fa duk bula ce. Wataƙila a gidan ma ba shi da kataɓus. Amma ya cika muku baki ya ɗora ku a keken ɓera kuna neman rusa aurenku.

Haka ma mata, musamman masu sayar da kayan mata kan kuranta cewa, mazansu a tafin hannunsu suke. Ke kuma ki je ki yi ta wahalar da kanki sai mijinki ya zama haka. Daga ƙarshe ki tuge igiyar auren naki gabaɗaya. Hattara da kallon kitse a matsayin rogo.

Abu na gaba kuma, a sani kowanne ɗan adam da irin yadda yake rayuwarsa. Wani ba za ka iya canza shi ya koma yadda kake ko kike so ba. Sai a yi haƙuri da shi. Don ba zai rasa wasu abubuwa kuma masu kyau waɗanda kai kake so ba daga wajensu.

Sannan kuma ku sani, akwai sirrika birjik a gidajen aure waɗanda ma’aurata ko danginsu da wuya su sani. Amma don ba su faɗa ba, ba ya nufin babu matsaloli. Kawai su sun fi ku godiyar Allah ne shi ya sa ba sa ƙorafin. Sun rufa wa kansu asiri sun zauna lafiya.

Misali ki ga wata mace mijinta yana ta lallaɓa ta ina ka sa, ina ka ajiye. Ke kuma ki ji duk Duniya ta yi miki zafi saboda ke naki mijin ba ya yi miki haka. To ki sani, wataƙila ita wannan matar komai na gidanta ita ta ɗauki nauyinsa. Mijinta ba ya kashe mata ko sisi daga kuɗinsa. Misali ne kawai na bayar. Ban ce ko’ina haka ne ba.

Amma kin ga idan ba ta faɗa miki ba, ai ba za ki sani ba ko? Ke kuma daga ganin wannan sai ki je ki ɗaga wa mijinki hankali saboda ba ya miki haka. Haba ‘yaruwa! Shi fa rogon nan matuƙar yana nesa ba ki zo kusa kin kashe kwarkwatar idanunki ba za ki yi ta ganinsa a kitse. Kuma za ki yi ta yaudaruwa da wahaluwa a rashin binciken haƙiƙanin lamarin.

Haka maza masu kushe matan Hausawa su dinga yi wa matan kanuri ko wasu ƙabilun kallon kitsen rogo su ma su yi hattara don wataƙila kallon kitsen rogo ne. Don haka kowanne ɓangare mata da maza a dinga gode wa Allah da abokan rayuwa. Bissalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *