Gwamnati ta nemi kotu ta janye haramcin kamo Igboho

Babban Lauyan Nijeriya, Abubakar Malami, ya miƙa wa Babbar Kotun jihar Oyo takarda ta neman tsallake dokar hani da kotu ta gindaya da ta hana kama Sunday Adeyemi (Sunday Igboho) da kuma daƙile asusunsa na banki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito a ranar 4 Agusta, kotun ta aminta da buƙtar da Igboho ya nema ta hana hukumar DSS da Babban Lauyan Ƙasa su damƙe shi da kuma daƙile masa asusunsa na banki.

Tun farko lauyan Igboho, Mr Yomi Aliyu, ya shaida wa kotu cewa rayuwar wanda yake karewa na fuskantar barazana tun bayan da DSS ta kai wa gidansa farmaki ran 1 ga Yuli wanda hakan ya yi sanadiyyar lalata masa dukiya mai yawa.

Bayan da aka dawo da ci gaba da shari’ar, lauyan Malami, Mr Abdullah Abubakar, ya shaida wa kotu cewa ya shigar da takardar ƙin yarda kan batun.

Abubakar ya ce ba zai iya komai yanzu ba sabo a makare ya shigar da takardar farko, don haka ya buƙaci kotun da ta ƙara masa lokaci.

Daga bisani, Alƙalin Kotun, Jastis Ladiran Akintola, ya aminta da buƙatar ƙarin lokacin da aka gabatar wa kotun amma tare da tarar N50,000.

Sannan ya ce dokar hana cafke Igboho da daƙile masa asusun banki da aka gindaya tana nan har sai lokacin da kotu ta ɗage ta.

Daga nan ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ran 30 ga Agusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *