‘Yan bindiga sun kutsa NDA, sun kashe mutum 2 sun yi garkuwa da 1 a Kaduna

A safiyar yau Talata wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kutsa cikin makarantar horarar da sojoji ta Nijeriya, Nigerian Defence Academy (NDA) da ke Afaka a jihar Kaduna.

Sanarwar manema labarai da NDA ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, Manjo Bashir Muhd Jajira, ta nuna jami’ai biyu sun rasa ransu sannan an sace guda yayin ɗauki ba daɗin da aka yi da ‘yan bindigar.

Sanarwar ta ce NDA tare da haɗin gwiwar 1Division na sojojin Nijeriya da cibiyar horar da da sojojin sama da sauransu da ke Kaduna, sun sunkuya bincike domin daƙile ‘yan bindigar da ke yankin baki ɗaya da kuma ceto jami’in da ɓarayin ke riƙe da shi.

Haka nan, sanarwar ta nuna sauran jama’ar da ke zaune cikin NDA kowa na ƙalau. Tare da ba da tabbacin nan ba da jimawa ba za a ga bayan ɓarayin sannan a kuɓutar da jami’in da suka sace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *