Hanyoyin Nijeriya sun zama tarkon mutuwa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Na fara wannan rubutu ne zuciyata cike da takaici, ƙunci da ɓacin rai, sakamakon ta’addancin da ya faru cikin makon da ya gabata na kisan gillar da wasu matasan Kirista suka yi wa wasu matafiya su kimanin 30 a kan wata babbar hanya da ke cikin garin Jos, a dalilin taka sawun ɓarawo da suka yi, yayin da suke ƙoƙarin kauce wa cinkoson ababen hawa a cikin gari, suka yi kuskuren bin wata hanyar bayan gari don yin ratse su wuce zuwa Abuja daga nan kuma su ɗauki hanyar komawa Jihar Ondo a Kudu Maso Yammacin Nijeriya, inda ‘yan uwa da iyalansu suke.

Rahotanni sun bayyana cewa, waɗannan mutane waɗanda akasarin su Fulani ne, mabiya ɗariƙar Tijjaniyya, sun fito ne daga Jihar Bauchi, inda aka gudanar da babban taron zikiri na ƙasa da addu’o’in zaman lafiya a gidan Babban Shaihun Ɗarikar nan, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, albarkacin shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1443 Bayan Hijira da aka yi. Amma hanya ta bi da su ta Jos, babban birnin Jihar Filato a kan hanyarsu ta komawa gida.

Sai dai sakamakon ƙaddara da aka ce ta riga fata, ko kuma tsautsayi da ake cewa ba ya wuce lokacin sa. Waɗannan matafiya suka shiga garin a lokacin da al’ummar Irigwe ke cikin makokin kashe-kashen da suke zargin maharan Fulani sun kai kan mutanen su a ƙauyukan Miango a ƙaramar hukumar Bassa, yankin da ke maƙwaftaka da babban birnin jihar. A dalilin rikita-rikitar da ta daɗe tana aukuwa tsakanin manoma da makiyaya a yankin, kuma take ci gaba da haifar da asarar rayuka da dukiyoyi, daga kowanne ɓangare.

An rawaito rundunar ‘yan sanda ta Jihar Filato na bayyana cewa, fusatattun matasan ƙabilar Irigwe ne suka far wa waɗannan matafiya Fulani da ke cikin manyan motoci ƙirar homa bas guda biyar, yayin da su kuma mutanen Irigwe suka ɗauko gawarwakin ‘yan uwansu da aka kashe za su je wajen binnewa. Ganin motoci cike da baqin fuska masu kamannin Fulani a cikin jerin motocin da ke hanya suna jiran masu wucewa da gawa waɗanda ke sanye da baƙaƙen kaya, ya sa su ƙara harzuƙa, inda suka far masu da jifa da duwatsu da sauran makamai da aka riƙa fitowa da su daga bisani, don halaka waɗannan matafiya da ake yi wa kallon maƙiya, waɗanda kuma suke zargin ‘yan uwansu ne suke kashe musu nasu ‘yan uwan su ma.

Sakamakon abubuwan da suka faru dai na ƙeta da mugunta, rahotanni sun ce an kashe mutanen da ba su gaza 30 ba, duk da yake a hukumance rahoton hukumar ‘yan sanda na farko ya bayyana cewa mutane 22 ne aka kashe yayin da ake cigaba da neman wasu da suka fantsama cikin duwatsu, da gidajen jama’a, don neman mafaka.

Kwanaki goma kafin wannan baƙar rana ta Asabar, nesa kaɗan da inda wannan ta’addancin ya auku a yankin Gada Biyu, wasu matasa sun far wa wasu matafiya Fulani da suka je wucewa da shanu a wasu motoci biyu za su kai Abatuwa, don sayar wa ga masu fawa. Nan ma haka aka kashe wasu da qona motocin. Abin da ya qara sanya fargaba da taraddadi a zukatan matafiya musamman mazauna garin Jos, waɗanda sanin halin da hanyar ke ciki suke ƙaurace wa bin ta. Sai dai baƙi da suke shigowa cikin rashin sani.

Jihar Filato ta daxe da kasancewa tarkon mutuwa, musamman ga matafiya waɗanda sau da dama suke shiga garin Jos ta maƙwaftan ƙauyuka inda ake yawan samun tashe tashen hankula, sakamakon rikicin ƙabilanci da na addini da ya dabaibaye jihar. Rayuka da dama sun salwanta a irin wannan faɗawa cikin tsautsayi da ƙaddara da matafiya baƙi kan yi, a hannun matasan ƙabilun Filato, da a duk lokacin da suka samu wata damuwa da abokan zaman su makiyaya ko mazauna jihar, sai su fita su datse kan manyan hanyoyin da suka ratsa ta jihar suna farautar duk wani da suka ga yana kama da wata ƙabila da suke rikici da ita, musamman ma dai Hausawa ko Fulani. Ba za mu manta da kisan gillar da aka yi wa Marigayi Janar Alƙali ba, a kan hanyar sa ta zuwa Jihar Bauchi, inda ya biyo ta hanyar Jos.

Wannan halayya ta tare hanya a riƙa afkawa matafiya da ba su san hawa ba ba su san sauka ba, ya kusan zama ruwan dare a ƙasar nan, musamman ma dai a yankin Arewa. Ya sha faruwa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda mazauna ƙauyukan da ke kan hanya sukan fita su datse hanya su riƙa kisa da lalata ababen hawa da ke wucewa ta kan titin gwamnati, saboda kawai suna tarzoma ko nuna rashin jin daɗi ga wani abu da ya ke faruwa da al’ummar su.

Ba a hanyar Abuja ba, hatta a yankin kudancin Jihar Kaduna ma inda ake samun faɗace-faɗace tsakanin manoma da makiyaya a yankin, wannan salon suke amfani da shi, wajen datse hanya suna binciken ababen hawa ko za su samu wani matafiyi da ya yi kama da ƙirar abokan gabar su, don kawai su huce fushinsu su ɗauki fansar abin da suke zargin an yi musu.

A daidai lokacin da nake wannan rubutu ma, akwai wasu rahotanni da ba su inganta ba da ke gargaɗin matafiya su kaucewa bin hanyar Kagoro a yankin kudancin Kaduna, saboda yadda wasu ɓata-gari ke tare hanya suna cutar da matafiya.

Rikicin ƙabilanci a Jihar Gombe ya sha haifar da irin haka, a wayi gari wani saɓani tsakanin mazauna jihar ya sa wasu marasa tunani su hau kan hanya suna buge masu ababen hawa da ba su ji ba ba su gani ba.

Ba ma batun rikicin ƙabilanci ba, dama wasu hanyoyin da dama sun gagara biyuwa ga matafiya saboda rashin tsaro, sace sacen ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane, da ‘yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas da suka sa ala tilas wasu manyan hanyoyin suka daina biyuwa ta daɗin rai ga matafiya.

Ga kuma wata matsalar da ita ma har yanzu aka kasa magance ta, wato matsalar lalacewar manyan hanyoyi da ke zama mutuwa kusa ga matafiya, inda rayukan ‘yan Nijeriya da dukiyoyin su ke salwanta, saboda rashin kyan hanya. Dubi dai misalin hanyar Zariya zuwa Saminaka zuwa Jos, hanyar da ta kusa mutuwa baki ɗaya, direbobi da dama sun qaurace mata, sun gwammaci su yi zagaye, wanda ke jefa su cikin wani haɗarin.

Babu shakka a yayin da muke kira ga hukumomin da abin ya shafa su qara zage damtse wajen ganin sun gyara manyan hanyoyin ƙasar nan da samar da ingantaccen tsaro da zai cire fargaba da tsoro a zukatan direbobi da sauran matafiya, a lokaci guda kuma, muna kira ga ‘yan Nijeriya musamman mazauna garuruwan da ke bakin hanya su guji amfani da waɗannan hanyoyin a matsayin wani makami na cimma burin su na ramuwar gayya, ko huce haushi kan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.

Tabbas wannan kuskure ne babba, kuma bam ne da zai iya jefa ƙasar nan cikin mummunar matsalar tsaro. Domin idan har aka ƙyale irin abin da ya faru a Jos ya ci gaba da faruwa ba a ɗauki tsattsauran mataki ba a kai to, lokaci zai zo da al’ummar wata jiha da aka tava mutanen su za su ce su ma ba su yarda ba, su shiga tare wasu matafiya a nasu ɓangaren suna ɗaukar fansa. Hakan ba zai haifarwa ƙasar nan ɗa mai ido ba!

An jiyo cikin wata sanarwa da kakakin fadar gwamnatin Jihar, Ondo Richard Olatunde ya fitar yana mai isar da saƙon Gwamnan Jihar Rotimi Akeredolu cewa, jama’ar jihar su kwantar da hankalin su bisu abubuwan da suka faru na kisan gillar da aka yi wa wasu ‘yan jihar a Jos. Sakamakon jajentawar da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya yi masa kan abin da ya faru.

Idan lamarin yana kai wa ga haka, har ta kai gwamnati da gwamnati na musayar maganganu kan rashin hankalin da wasu suka nuna a kan matafiya to, lallai alamu na nuni da wata rana abin da zai biyo baya ba zai yi wa kowa daɗi ba.

Ya kamata ‘yan Nijeriya a duk inda suke su kasance masu tausayawa juna da haɗin kai, domin a samu ingantaccen tsaro da zaman lafiya. Mu zama masu aiki da hankali, mu daina biye wa son zuciyoyin mu.

Allah ya jiƙan rayukan da aka rasa. Amin