‘Yan bindiga sun halaka kwamandan ‘yan sanda a Filato

‘Yan bindiga a Jihar Filato sun kashe jami’in ɗan sanda da wasu mutum takwas a yankin Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar.

Ɗan sandan da aka kashen mai suna Abdulrahaman Isah, shi ne kwamandan runduna ta musamman da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda (IGP) ya kafa mai zamanta a Mangu.

Harin wanda ya auku a ranar Litinin da ta gabata da yamma kusa da ƙauyen Ƙwai, ya rutsa har da wani ɗan bijilanti mai suna Hassan Mohammed.

Mai magana da yawun ‘yan sandan  jihar Filato, Ubah Ogaba, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

A cewar Ogaba: “A ranar 23 ga Agusta,2021 rundunar ta samu labarin aika-aikar da wasu ‘yan bindiga suka yi a ƙauyen Ƙwai da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar.

“Samun labarin ke da wuya sai aka haɗa kan rundunar musamman ta IGP mai zamanta a Mangu haɗa da ‘yan sandan da ke aiki a shiyyar da kuma ‘yan bijilanti suka bazama aiki.

“Bayan da ‘yan bindigar suka tsinkayi jami’an ne sai suka buɗe musu wuta, inda daga bisani jami’an tsaron suka yi nasarar kwantar da mutum shida daga ‘yan bindigar yayin da sauran suka tsere ɗauke da munanan raunuka.

“Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun ɓatagarin sun haɗa da bindiga ƙirar AK 47 guda uku.

Jami’in ya ce yayin artabun, jami’insu guda, Insp. Abdulrahaman Isah, wanda shi ne shugaban rundunar musamman ta IGP, ya rasa ransa, haka ma ɗan  bijilanti Hassan Mohammed, shi ma ya kwanta dama.