Da Ɗumi-ɗuminsa: An tsige Shugaban Majalisar Kebbi da mataimakinsa

Rahotannin da MANHAJA ta samu daga jihar Kebbi na nuni da cewa, ‘yan Majalisar Dokokin jihar sun tsige Shugaban Majalisar, Samaila Abdulmunin Kamba da mataimakinsa, Muhammad Buhari Aleiro daga muƙamansu.

Binciken MANHAJA ya gano cewa, mambobi 20 daga cikin ‘yan majalisa 24 da Majalisar Jihar ke da su ne, suka kaɗa ƙuri’ar goyon bayan tsige waɗanda lamarin ya shafa a wannan Talatar.

Bayan tsigewar, ba tare da ɓata lokaci ba ‘yan majalisar suka zaɓi Mohammed Abubakar Lolo da Muhammad Usman Ankwai a matsayin sabbin shugabannin majalisar.

Duk da dai babu wani cikakken bayani kan dalilin da ya sa aka tsige tsoffin shugabannin majalisar, sai dai an zarge su da saɓa wa ƙa’adojin majalisar.

MANHAJA za ta kawo muku cikakken rahoto kan wannan badaƙalar na gaba kaɗan.