Labarai

INEC ta samu buƙatun rajistar zaɓe miliyan 2.4, yayin da an yi rajistar mutum miliyan 1.9 ta yanar gizo

INEC ta samu buƙatun rajistar zaɓe miliyan 2.4, yayin da an yi rajistar mutum miliyan 1.9 ta yanar gizo

Ya zuwa yanzu, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta samu buƙatar yin rajista guda 2,449,648 daga ranar da ta fara aikin rajistar masu zaɓe (wato Continuous Voter Registration, CVR) wato 28 ga Yuni, a cewar wani jadawalin mako-mako na aikin wanda aka fitar a ranar Litinin a Abuja. Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa jadawalin ya kuma nuna cewa ya zuwa yanzu, 'yan Nijeriya 1,923,725 ne su ka kammala matakan farko na yin rajistar su ta hanyar yanar gizo a cikin wannan lokacin na mako bakwai a daidai ƙarfe 7 na safiyar ranar Litinin, 16 ga Agusta. Bugu…
Read More
Abin da ya sa ba mu kashe tubabbun ‘yan ta’adda, cewar sojoji

Abin da ya sa ba mu kashe tubabbun ‘yan ta’adda, cewar sojoji

Rundunar sojan Nijeriya ta ce, babban taro na duniya wanda ita ma Nijeriya ta sanya hannu a kansa, bai yarda da kashe tubabbun 'yan ta'addan da suka miƙa wuya ba. Rundunar ta faɗi haka ne a matsayin martani ga ra'ayin wasu 'yan ƙasa da ke ganin cewa me zai hana a kashe 'yan Boko Haram ɗin da suka ce sun tuba maimakon amincewa da su su ci gaba da rayuwa a cikin al'umma. MANHAJA ta kalato cewa a tsakanin watanni ukun da suka gabata, mayaƙan Boko Haram da na ISWAP sama da 3,000 ne aka damƙe ko suka tuba suka…
Read More
Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Mantu ya kwanta dama

Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Mantu ya kwanta dama

Allah Ya yi wa tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Nasiru Mantu. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a cikin daren Litinin a wata asibitin Abuja bayan fama da rashin lafiya. A halin rayuwarsa, marigayin cikakken ɗan siyasa ne, kuma tsohon sanata da ya wakilci Filato ta Tsakiya a Majalisar Dattawa. An zaɓe shi a matsayin sanata ne 1999 inda ya zama mataimakin shugaban Majalisar a shekarar 2000. Baya ga haka, Mantu ya yi aiki a wurare da dama tare da riƙe muƙamai daban-daban inda ya ba da tasa gudunmawa ga cigaban ƙasa. An haifi Mantu ne a ranar…
Read More
Amincewa da tubabbun ‘yan Boko Haram na iya haifar da tawaye a Borno – Zulum

Amincewa da tubabbun ‘yan Boko Haram na iya haifar da tawaye a Borno – Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Uamara Zulum, ya bayyana cewa tubabbun 'yan Boko Haram su 1,000 da suka miƙa wuya sun bar gwamnatin jihar da al'ummarta cikin wani mawuyacin halin tsaro mai baki biyu. A cewar gwamnan, muddin gwamnati da masu faɗa a ji a jihar ba su haɗa kai sun ɗauki matakin daƙile matsalar tsaron da jihar ke fuskanta a halin yanzu ba, hakan ka iya haifar da 'yan tawayen farar hula a jihar. Zulum ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa shugabannin jami'an tsaro da sarakuna jawabi a Bama da Gwoza. Ya ci gaba da cewa,…
Read More
Da Ɗumi-ɗuminsa: Buhari ya sanya hannu a kan dokar harkokin man fetur

Da Ɗumi-ɗuminsa: Buhari ya sanya hannu a kan dokar harkokin man fetur

Daga AMINA YUSUF ALI A yau Litinin, 16 ga watan Agusta, Shugaban Ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sanya wa ƙudurin harkokin man fetur hannu domin mai da shi doka. Bayanin haka ya fito ne daga mai bai wa Buhari shawara na musamman a kan hulɗa da jama'a da kuma watsa labarai, Femi Adesina a Abuja. Adesina ya ce hakan ya faru jim kaɗan bayan Shugaban ya dawo daga Landan a yayin da yake zaman killace kai na kwana biyar kamar yadda kwamitin tafiyar da harkokin yaƙi da annobar korona na Fadar Shugaban Ƙasa ya buƙata. Ya ce Buhari ya rattaba…
Read More
Ruftawar gada ta yi sanadin mutuwar matafiya 21 a Jigawa

Ruftawar gada ta yi sanadin mutuwar matafiya 21 a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a wasu sassan jihar Jigawa hakan ya haifar da ruftawar gadar da ta haɗa Basirka da Gwaram da jihohin Bauchi, Adamawa da Borno. Ruftawar gadar ta yi sanadin faɗawar wasu motoci guda biyu wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21 tare da jikkata matashi guda. Bayyanar jami'an tsaro a inda ibtila'in ya auku haɗa da ƙokarin jama'ar yankin, hakan ya taimaka matuƙa wajen fitar da gawarwakin matafiyan da haɗarin ya rutsa da su. Ya zuwa haɗa wannan labari, ba kai ga kammala tantance waɗanda suka…
Read More
Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun sace ɗalibai 15, ma’aikata 4, sun kashe ɗan sanda 1 da masu gadi 2 a Zamfara

Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun sace ɗalibai 15, ma’aikata 4, sun kashe ɗan sanda 1 da masu gadi 2 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tashin hankali ya ɓarke a Kwalejin Aikin Noma da Kiwon Lafiyar Dabbobi da ke Bakura a Jihar Zamfara, yayin da wasu gungun 'yan bindiga suka kai hari makarantar, Inda suka sace ɗalibai 15, ma'aikata 4, suka kuma kashe jami'in ɗan sanda ɗaya haɗa da masu gadi biyu. Mataimakin magatakardar kwalejin, Aliyu Atiku, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar tarho da safiyar yau Litinin. A Atiku, 'yan bindigar sun mamaye harabar makarantar da misalin ƙarfe 10 na daren jiya Lahadi kuma sun kwashe kimanin sa'a ɗaya da rabi suna cin…
Read More
INEC ta yi gargaɗin akwai gidan yanar rajistar zaɓe na ƙarya

INEC ta yi gargaɗin akwai gidan yanar rajistar zaɓe na ƙarya

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ja hankalin jama'a dangane da wani gidan yana na ƙarya na yin rajistar zaɓe a intanet. Hukumar ta yi gargaɗin ne a cikin wata sanarwa da Mista Festus Okoye, Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Faɗakar da Masu Zaɓe na INEC ya fitar a Abuja. Okoye ya ce an ja hankalin INEC ne zuwa ga wani saƙo da ake yaɗawa a soshiyal midiya game da wani gidan yana da aka ce wai na yin rajistar masu zaɓe na INEC ne “wanda ya sha bamban da ainihin gidan yanar rajistar INEC na gaskiyar."…
Read More