Labarai

Kwamishinan Hukumar Alhazai ya yi auren ɗiya a Kano

Kwamishinan Hukumar Alhazai ya yi auren ɗiya a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI a Kano A yau Lahadi, 15 ga watan Agustan, 2021 ne ɗaruruwan 'yan'uwa da abokan arziki suka yi dafifi i zuwa masallacin Murtala da ke Jihar Kano domin halartar ɗaurin auren Dakta Hannatu, ɗiya a gurin Alhaji Nura Hussaini Yakasai wanda Kwamishina ne mai kula da tsare-tsare da kuma harkokin Kuɗi a Hukumar Alhazai ta Najeriya. Wadda aka bayar da aurenta ga Arc. Muhammad Shafiq Kamal. A yayin da yake zantawa da 'yan jaridu a wajen ɗaurin auren, Alhaji Yakasai ya bayyana irin matsanancin farin cikinsa da Allah ya kawo shi ranar da zai ba da…
Read More
Miyetti Allah da CAN sun nuna damuwarsu kan harin Jos

Miyetti Allah da CAN sun nuna damuwarsu kan harin Jos

Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta yi tir da harin da aka kai wa al'ummar hanyar Rukuba da ke Jos, Jihar Filato. Haka nan, ƙungiyar ta buƙaci jami'an tsaro da su dukufa bincike don gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki don su fuskanci hukunci. MACBAN ta yi waɗannan bayanan ne cikin sanarwar da ta fitar ta hannun sakatarenta na ƙasa, Baba Othman Ngelzarma, a Jos a ranar Lahadi. Ƙungiyar ta nuna damuwarta kan yaddahar yanzu ba a gano wasu mazauna yankin ba kimanin su 40 da suka ɓata sakamakon harin. Yayin da ta…
Read More
Harin Filato: Sufeto-Janar ya ba da umarnin tura rundunar bincike, an damƙe mutum 20 an ceto 33 – Mba

Harin Filato: Sufeto-Janar ya ba da umarnin tura rundunar bincike, an damƙe mutum 20 an ceto 33 – Mba

Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin gaggawa da a tura rundunar bincike zuwa jihar Filato domin auna ɓarnar da ta auku yayin harin baya-bayan nan da kuma saka ƙaimi wajen ci gaba da tabbatar da lumana a yankunan da lamarin ya shafa. Baba ya ba da wannan umarnin ne cikin wata sanarwar manema labarai da ta fito ta hannu mai magana da yawun rundunar na ƙasa, CP Frank Mba, ran Lahadi a Abuja. Sanarwar ta ce ɗaukar matakin tura rundunar ya faru ne sakamakon harin da aka kai wa mazauna yankin Rukuba da ke…
Read More
Ambaliya ta raba ahali 120 da matsugunansu a Jigawa

Ambaliya ta raba ahali 120 da matsugunansu a Jigawa

Rahotanni daga Unguwar Tsallake da ke yankin ƙaramar hukumar Guri a jihar Jigawa, sun tabbatar da kimanin ahali 120 ne suka rasa matsugunansu biyo bayan ambaliyar ruwan da ta auku sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a yankin. Jami'in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Alhaji Sunusi Doro, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ran Asabar cewa, ibtila'in ya faru ne ta dalilin mamakon ruwan sama a Laraba da Alhamis da suka gabata. Doro ya ce ambaliyar ta mamaye sama da gidaje 120 wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa matsuguni ga mutane da dama. A cewar jami'in,…
Read More
Rikicin Filato: Lalong ya kafa dokar hana fita a wasu sassan jihar

Rikicin Filato: Lalong ya kafa dokar hana fita a wasu sassan jihar

Gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana zirga-zirga a yankunan ƙananan hukumomin Bassa da Jos ta Arewa da kuma Jos ta Kudu. Gwamantin Filato ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan hatsaniyar da aka samu a yankin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da ashirin tare da jikkata wasu da dama. Cikin sanarwar da ta fito ta hannun Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar a yau Lahadi, Dr Makut Macham, Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya ce, dokar hana zirga-zirgar ta soma aiki ne daga ranar 14 ga Agusta, daga ƙarfe 6 na yamma zuwa…
Read More
‘Yan sandan sun tabbatar da kuɓutar da shugaban APC da aka yi garkuwa da shi a Neja

‘Yan sandan sun tabbatar da kuɓutar da shugaban APC da aka yi garkuwa da shi a Neja

Rundunar 'yan sanda ta jihar Neja, ta tabbatar da kuɓutar da shugaban jam'iyyar APC na 'Zone C', Aminu Bobi, wanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi kwanan nan. Mai magana da yawun rundunar, DSP Wasiu Abiodun, shi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.Abiodun ya ce a ranar Juma'ar da ta gabata aka sami nasarar kuɓutar da Bobi da misalin ƙarfe 8:30 na dare, a dajin Igwama da ke yankin Bobi a ƙaramar hukumar Mariga da ke jihar. Jami'in ya ce, bayan da aka kuɓutar da Bobi an kai shi Babbar Asibitin…
Read More
‘Yan bindiga sun sace ɗan gidan hadimin Shugaba Buhari, Abubakar Maikano a Kaduna

‘Yan bindiga sun sace ɗan gidan hadimin Shugaba Buhari, Abubakar Maikano a Kaduna

'Yan bindiga sun sace Sanusi Abubakar Maikano, ɗan gidan Alhaji Abubakar Maikano, wanda babban jami'i ne daga cikin hadiman Shugaban Ƙasa Muhammadu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Wannan na faruwa ne bayan da ɓarayi suka fasa gidan Maikano da ke Fadar Shugaban Ƙasa watanni huɗu da suka gabata. Bayanan jami'an tsaro a Kaduna sun nuna an sace Sanusi ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare a ranar Asabar da ta gabata bayan da ya dawo daga gidan gonarsa. Yayin da wasu shaidu suka nuna an sace Sanusi ne a gidansa da ke Gwantu, hedikwatar ƙaramar hukumar Sanga a…
Read More
Sarkin Musulmi ga likitoci: Ku janye yajin aiki don amfanin al’umma

Sarkin Musulmi ga likitoci: Ku janye yajin aiki don amfanin al’umma

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙolin Harkokin Musulunci a Nijeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya shawarci likitocin da ke yajin aiki da su janye yajin aikin nasu don amfanin al'ummar ƙasa. Haka nan, Sarkin ya roƙi likitocin da su yi wa Allah, su dubi halin da ake ciki na fama da annobar korona da kuma ɓarkewar cutar amai da gudawa a wasu sassan ƙasa, sannan su dakatar da yajin aikin nasu. Sarkin ya yi waɗannan bayanan ne cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun Daraktan Gudanarwa na NSCIA, Malam Zubairu Usman-Ugwu, ranar Asabar a Abuja. Sanarwar ta nuna yadda Basaraken…
Read More
Rikicin Filato: Sojoji sun damƙe mutum 12

Rikicin Filato: Sojoji sun damƙe mutum 12

An samu aukuwar rikici a safiyar Asabar a yankin hanyar Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane tare da jikkata wasu. Bayanan da MANHAJA ta kalato daga yankin sun nuna hatta wasu matafiya da ke wucewa a daidai lokacin da rikicin ya faru, an ƙona musu mota, amma lamarin ya tsagaita sakamakon bayyanar jami'an tsaro a yankin. Jami'i mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven, Major Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar lamarin. Tare da cewa jami'an rubdunar ta musamman sun bayyana a inda aka samu hatsaniyar…
Read More
Tattaunawa ta musamman da Shugaban SMEDAN, Dr Dikko Umar Radda

Tattaunawa ta musamman da Shugaban SMEDAN, Dr Dikko Umar Radda

Mutum ne haziƙI wanda duk wanda ka tambaya shaida a kansa abu biyu yake faɗa na farko, mutum ne mai tsoron Allah sai kuma tausayi. Ya jima yana gwagwarmaya kan tallafawa al’umma da siyasa ba a iya Katsina ba a duk arewacin Nijeriya ba inda ba a ji da ganin tallafin Gwagware foundation ba. Jaridar Manhaja ta tattauna da Dr Dikko Umar Raɗɗa don jin me ne sirrin nasararsa da kuma abin da ya sa a gaba yanzu. Taƙaitaccen Tarihinka.Dr Dikko Umar Raɗɗa Gwagwaren Katsina shugaban ƙananan da matsakaitan masana’antu na ƙasa kuma shugaba na Gwagware Foundation wanda wannan gwagware…
Read More