Labarai

Masari ya yi tir da yadda jami’an tsaro ke kashe mutane da tuƙin ganganci a Katsina

Masari ya yi tir da yadda jami’an tsaro ke kashe mutane da tuƙin ganganci a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi tir da yadda ake samun aukuwar yadda jami'an Hukumar Kwastam ke kashe 'yan jihar saboda tuƙin ganganci da abubuwan hawa. Gwamnan ya bayyana ɓacin ransa ne cikin wata sanarwa wadda Darakta Janar na Yaɗa Labaran Gwamnatin Jihar, Abdu Labaran Malumfashi, ya sanya wa hannu a ranar Juma'a. Masari ya ce, daga wannan lokaci gwamnatinsa ba za sake lamuntar aukuwar irin haka a jihar ba. Gwamnan ya yi magana ne a matsayin martani dangane da mummunan haɗarin da ya auku a Litinin da ta gabata a jihar, inda wani jami'in Kwastam ya murƙushe…
Read More
Za a yi wa Lai Mohammed wankan sarauta a matsayin Kakakin Kebbi a Satumba

Za a yi wa Lai Mohammed wankan sarauta a matsayin Kakakin Kebbi a Satumba

Ranar 25 ga Satumba mai zuwa Sarkin Argungu a jihar Kebbi, Alhaji Mohammed Mera, zai naɗa Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, a matsayin Kakakin Kebbi. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya samu a ranar Juma'a. A bara ne Sarkin Argungu ya sanar da naɗa Lai a muƙamin yayin da yake bayyana tsare-tsaren bikin kamun kifi a Abuja da aka saba gudanarwa a Argugun wanda aka gudanar daga 11 zuwa 14 ga Maris na 2020. Sanarwar ta ce an yi nisa da shirye-shiryen wankan sarautar da za a…
Read More
Dattijon ƙasa, Ahmad Joda, ya kwanta dama

Dattijon ƙasa, Ahmad Joda, ya kwanta dama

Daga AMINA YUSUF ALI Allah ya yi wa ɗaya daga cikin fitattun manyan Ƙasar Nijeriya, Ahmad Joda rasuwa. Ya rasu yau Juma'a, a garin Yolan Jahar Adamawa. Marigayin ya rasu ne bayan matsananciyar doguwar rashin lafiya wacce ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Marigayin ya rasu ne yana da shekaru 91 da haihuwa. Kuma tsohon ɗan jarida ne wanda ya yi shuhra a fagen. Haka nan, yana ɗaya daga cikin manyan Sakatarorin Gwamnatin Ƙasar nan a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon, yayin mulkin soja. A inda ya yi ritaya a matsayin babban sakataren ma'aikatar masana'antu. Bayan Yaƙiin…
Read More
Nijeriya ta samu ƙarin mutum 753 da suka harbu da cutar korona – NCDC

Nijeriya ta samu ƙarin mutum 753 da suka harbu da cutar korona – NCDC

Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta bayyana ceqa an samu ƙarin mutum 753 da suka harbu da cutar korona a faɗin ƙasa a tsakanin sa'o'i ashirin da huɗu da suka gabata. Cibiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet a safiyar Juma'a, inda ta nuna ƙarin da aka samu ya shafi wasu jihohi goma sha huɗu ne. NCDC ta ce jihohin da lamarin ya sha sun haɗa da: Legas 364, Akwa Ibom 141, Oyo 74, Rivers 46, Abia 38, Ogun 24, Kwara 20, sai kuma Birnin Tarayya, Abuja mai mutum 12. Sauran jihohin su ne, Ekiti…
Read More
An sako kwamishinan da aka yi garkuwa da shi a Neja

An sako kwamishinan da aka yi garkuwa da shi a Neja

Bayan kwanaki biyar da yin garkuwa da shi, 'yan bindiga sun sako Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Neja, Alhaji Sani Idris, da suka sace a jihar. Sanarwar da ta fito daga ahalin kwamishinan, ta nuna an sako Idris ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare ran Alhamis da ta gabata. Mr. Ado Ada, wanda ɗan'uwa ne ga kwamishinan, ya bayyana farin cikinsu dangane da dawowar Idris, tare da danganta nasarar dawowar da ƙoƙarin 'yan'uwansa ba tare da biyan wani kuɗin fansa ba. Sanarwar ta ce bayan da aka sako Idris, sai da aka binciki lafiyarsa kana daga bisani aka miƙa…
Read More
Da Ɗumi-ɗuminsa: Yau Buhari zai dawo daga London

Da Ɗumi-ɗuminsa: Yau Buhari zai dawo daga London

A wannan Juma'ar ake sa ran dawowar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daga London. Buhari zai iso Nijeriya ne can da misalin ƙarfe 5 na yamma bayan shafe kwanaki kimanin 18 a Ƙasar Birtaniya. Buhari ya halarci wani babban taro na duniya da aka shirya a kan sha'anin ilimi, wato GES a taƙaice, sannan bayan kammalawa ya tsaya duba lafiyarsa. Buhari da Tinubu a London A jiya Alhamis, an ga Buhari tare da jigo a jami'yyar APC, Bola Ahmed Tinubu awani hoto da aka yaɗa wanda ke nuni da lokacin da Buhari ya ziyarci Tinubu a London.
Read More
Cutar korona ta yi ajalin matar tsohon Shugaban Ƙasa, Sehu Shagari

Cutar korona ta yi ajalin matar tsohon Shugaban Ƙasa, Sehu Shagari

Allah Ya yi wa matar tsohon Shugaban Kasa Shehu Shagari, Hajiya Hadiza Shagari rasuwa. Sanarwar da ta fito daga ahalin marigayiyar ta hannun Capt. Muhammad Bala Shagari (rtd), ta nuna Hajiya Hadiza ta rasu ne a safiyar Alhamis samakon cutar korona. A cewar sanarwar, "Cikin alhini muna sanar da rasuwar mahaifiyarmu, Hajiya Hadiza Shehu Shagari, matar tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR (Turakin Sokoto). "Mun rasa ta ne da safiyar Alhamis, 12 ga Agusta, 2021 da misalin ƙarfe 3 na asuba bayan ta yi fama da cutar korona a cibiyar killace mutane da ke Gwagwalada, Abuja.” An…
Read More
Tiwita za ta ci gaba da aiki a Nijeriya nan ba da daɗewa ba – Lai

Tiwita za ta ci gaba da aiki a Nijeriya nan ba da daɗewa ba – Lai

Gwamnatin Tarayya ta ce nan ba da daɗewa ba za ta ɗage dokar haramta harkokin  microblogging da Tiwita a Nijeriya. Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da hakan jim kaɗan bayan kammala taron mako-mako na Majalisar Zartarwa a Abuja, wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo. Lai ya bayyana hakan ne yayin da yake ƙarin bayani dangane da tattaunawar da ake yi da masu harkar micro-blogging wanda a cewarsa galibinsu sun amince da dokokin da aka gindaya musu. Ministan ya ƙara da cewa, ɓangarorin da ba a rigada an daddale ba a kansu…
Read More