Labarai

Rigakafin korona: Lai ya musanta cewa Nijeriya na yawo da ƙoƙon barar neman tallafi

Rigakafin korona: Lai ya musanta cewa Nijeriya na yawo da ƙoƙon barar neman tallafi

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa kan cewa Nijeriya na kewayawa sassa tana miƙa ƙoƙon baranta na neman a tallafa mata da allurar rigakafin koroa. Ministan ya yi wannan ƙarin hasken ne yayin wata tattauna da kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ran Laraba, a Abuja. Ministan ya ce wasu daga cikin rigakafin Nijeriya ta sayo su ne ta hannun Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Afrika (AU) wadda aka cimma yarjejeniyar samar da rigakafin korona guda milyan 400 ta hanyar ciwo bashi a bankin AFREXIMBANK don amfanin ƙasashe mambobin AU. Don Haka Mohammed ya…
Read More
Cutar korona: Yau Nijeriya za ta karɓi rigakafin Johnson & Johnson guda 176,000

Cutar korona: Yau Nijeriya za ta karɓi rigakafin Johnson & Johnson guda 176,000

A wannan Laraba ake sa ran Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin korona samfurin Johnson & Johnson har guda 176,000, in ji shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Dr. Faisal Shuaib. Wannan na zuwa ne kimanin mako ɗaya da karɓar rigakafin korona samfurin 'Moderna' kimanin milyan 4 daga gwamnatin Amurka. Shuaib ya ce abin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta yi jinkiri wajen yi wa 'yan ƙasa rigakafin 'Moderna vaccine', shi ne don gudanar da bincike da kuma bai wa hukumarsu damar yin aiki tare da Hukumar Kula da Ingangancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) wajen samun…
Read More
Dalilin da ya kai tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Dickson ofishin EFCC

Dalilin da ya kai tsohon gwamnan Bayelsa, Sanata Dickson ofishin EFCC

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) tana riƙe da tsohon gwamnan Jihar Bayelsa kuma sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, Seriake Dickson. Wannan na zuwa ne biyo bayan gayyatar da EFCC ta yi wa tsohon gwamnan kan batun da ya shafi zargin aikata ba daidai ba da ofishinsa da kuma sarrafa kuɗaɗen gwamnati ba bisa ƙa'ida ba a shekara takwas da ya yi riƙe da jihar a matsayin gwamana, daga 2012 zuwa 2020. Da misalin ƙarfe 11 na safiyar yau Dickson ya isa ofishin EFCC da ke Jabi a Abuja,…
Read More
Kisan kai: Yadda sakin ɗan gidan tsohon Sbugaban Ƙasa, Aminu Yar’Adua daga kurkuku ya tayar da ƙura a Adamawa

Kisan kai: Yadda sakin ɗan gidan tsohon Sbugaban Ƙasa, Aminu Yar’Adua daga kurkuku ya tayar da ƙura a Adamawa

Bayanai daga jihar Adamawa na nuni da cewa hankula sun tattashi sakamakon sake ɗan gidan tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Musa Yar'Adua, wato Aminu Yar'Adua, da kotun Majastare ta yi daga kurkuku a ɓoye wanda ake zargi da laifin kisa An gurfanar da Aminu Yar’Adua a kotu ne bisa tuhumar kashe wasu mutum huɗu da mota a Adamawa sakamakon gudun wuce misali da mota. 'Yan jihar da dama na zargin cewa sakin Aminu na da nasaba da yadda rashawa ta yi wa fannin shari'ar Nijeriya kanta shi ya sa kotun ta iya ba da belin mutumin da ake zargi da aikata…
Read More
Mayaƙan Boko Haram-ISWAP 45 sun miƙa wuya a Konduga

Mayaƙan Boko Haram-ISWAP 45 sun miƙa wuya a Konduga

Mayaƙan Boko Haram da ISWAP a ƙalla su 45, ciki har da ƙananan yara da matasa, suka tuba suka miƙa wuya ga sojoji a yankin Arewa-maso-gabas. Mayaƙan sun miƙa wuya ne a Litinin da ta gabata a yankin Ƙaramar Hukumar Konduga a jihar Borno. Sai dai, wata majiya ta kusa sa sojojin ta ce mayaƙan sun miƙa wuya ne ba tare da miƙa makamansu ba. A cewar majiyar, waɗanda lamarin ya shafa 21 daga cikinsu daga Garin Dinya suke, sannan 24 daga ƙauyen Jaja Kalwa. Wasu mutum biyar daga cikin mayaƙan sun shaida wa jaridar PRNigeria cewa, an tilasta su…
Read More
‘Yan bindiga sun sace shugaban APC a Neja

‘Yan bindiga sun sace shugaban APC a Neja

Bayanai daga yankin ƙaramar hukumar Mariga a jihar Neja, sun nuna 'yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC na 'Zonne C', Aminu Bobi. Binciken MANHAJA ya gano cewa an yi gaba da Bobi ne a lokacin da ya je duba masu yi masa aiki a gona a ranar Asabar da ta gabata. Wata majiya ta kusa da wanda lamarin ya shafa ta ce, 'yan bindigar sun kai hari a gonar ne a kan babura inda kowane babur ke ɗauke da mutum uku, sannan suka yi ta harbe-harben bindiga a iska. Majiyar ta ƙara da cewa Bobi ne kaɗai 'yan bindigar…
Read More
Kotu ta ɗaure ma’aikatan banki biyu kan satar kuɗaɗen mamata a Kalaba

Kotu ta ɗaure ma’aikatan banki biyu kan satar kuɗaɗen mamata a Kalaba

Babbar Kotun Kalaba a jihar Cross River ta tura wasu ma'aikatan banki su biyu zuwa kurkuku bisa laifin satar miliyoyin Naira daga asusun ajiya na wasu mamata. An ɗaure Daniel Akpan Eno da Mbuk Idongesit ne bayan da hukumar EFCC a shiyyar Uyo ta gurfanar da su a kotun da Alƙali Edem Ita Kufre ke jagoranta a Kalaba bisa tuhumar haɗa baki da kuma wawushe maƙudan kuɗaɗe daga asusun ajiya a banki na wasu mamata. Alƙali Kufre ya yanke hukuncin ɗaurin wata uku ga Akpan da zaɓin tara na N50, 000.00, haka shi ma Idongesit da zaɓin biyan tara na…
Read More
‘Yan sanda sun cafke ‘yan fashin intanet a Keffi

‘Yan sanda sun cafke ‘yan fashin intanet a Keffi

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'yan sanda a garin Keffi, jihar Nasarawa, ta cafke wasu matasa su shida masu fashi a intanet da aka fi sani da 'Yahoo Boys'. Sanarwar manema labarai da rundunar ta fitar wadda ta sami sa hannun mai magana da yawun 'yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, a madadin Kwamishin 'Yan Sandan Jihar, ta nuna biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu game da harkokin ɓatagarin ne sai jami'anta suka yi musu dirar mikiya a maɓuyarsu da ke G.R.A Keffi inda aka kamo su. DSP Ibrahim Muhammed Siraj shi ne jami'in da ya jagoranci dakarun da…
Read More
Shugaban AMAC, Candido ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wakilin Jaridar Blueprint a Nyanya

Shugaban AMAC, Candido ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wakilin Jaridar Blueprint a Nyanya

Shugaban Hukumar AMAC ta Abuja, Hon. Abdullahi Adamu Candido, ya ziyarci iyalan marigayi Baba Yusuf, domin jajanta musu bisa rashin da ya same su. Marigayi Yusuf wanda wakilin Jaridar Blueprint ne a halin rayuwarsa, ya rasu ne ranar Talatar da ta gabata, 4 ga Agusta 2021, a gidansa da ke yankin Nyanya Gwandara a jihar Nasarawa. Kafin rasuwarsa, marigayi Yusuf mamba ne na tawagar 'yan jaridar Hukumar AMAC. Sa'ilin da yake isar da ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, Hon. Candido ya bayyana marigayin a matsayin ɗan jarida mai aiki tukuru daidai da dokokin aikin jarida. Haka nan, ya nuna damuwarsa kan…
Read More