Labarai

Gwamnatin Zamfara ta tallafa wa iyalan ɗan jaridar da ya rasu a Kaduna

Gwamnatin Zamfara ta tallafa wa iyalan ɗan jaridar da ya rasu a Kaduna

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau. Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da gudunmawar kayan abinci dabam-daban da kuma kuɗi da ba a bayyana adadinsu ba ga iyalan wakilin Jaridar The Sun, Mohammed Munirat Nasir, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Litinin da ta gabata a gidansa da ke Kaduna. Da yake gabatar da tallafin ga matar marigayin, Maryam Mohammed Munirat a madadin Gwamna a gidan marigayin da ke Kaduna a ranar Asabar, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya ce, "Ina fatan in gabatar da waɗannan kayan abinci a matsayin tallafi ga dangin da ya…
Read More
Kwalara ta kashe mutum 60 a Katsina

Kwalara ta kashe mutum 60 a Katsina

Aƙalla mutum 60 ne aka ruwaito sun rasu sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa ko kuma kwalara, a tsakanin wasu ƙauyukan jihar Katsina. Kwamishinan lafiya na jihar, Yakubu Danja ne ya bayyana haka ranar Asabar da ta gabata a wajen taron shekara-shekara na 2021 na Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NMA) reshen jihar da ya gudana a jihar. Sai dai, Kwamishinan bai yi ƙarin bayani ba kan takamammen lokacin da aka samu rashe-rashen ba. Danja ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gudanar da shirin wayar da kan 'yan jihar dangane da yaƙi da cutar a tsakanin ƙananan hukumomi 34 da…
Read More
Ta banka wa kanta wuta saboda tsananin kishi a Jigawa

Ta banka wa kanta wuta saboda tsananin kishi a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Wata mata 'yar kimanin shekara 25 da haihuwa, ta banka wa kanta wuta saboda tsananin kishi a ƙauyen Ƙwayamawa da ke cikin ƙaramar hukumar Dutse a jihar Jigawa. Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna cewa, sai da matar ta bulbule kanta da man fetur kana daga bisani ta cinna wa kanta wuta. An ce bayan da ta ga uwar-bari sakamakon raɗaɗin wutar ta ke cin ta, sai ta ruga waje tana ihu tana neman taimako, inda a nan waɗanda ke kusa suka taimaka wajen kashe wutar. Duk da dai an yi nasarar kashe…
Read More
2023: Matashi ya fi cancanta da mulkin Nijeriya – IBB

2023: Matashi ya fi cancanta da mulkin Nijeriya – IBB

A cikin wata wasiƙa da Tsohon Shugaban Ƙasa, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya aika wa jagoran APC, Bola Tinubu, da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jaddada musu cewa Nijeriya ta fi buƙatar matashin shugaba a 2023. Haka ma, ko a wata hira da aka yi da shi a tashar ARISE TV a Juma'ar da ta gabata, an ji Babangida ya ce, "Na soma hanƙoron matashin shugaba a Nijeriya." Ya ce, "Na riga da na ga mutum ɗaya ko biyu ko uku daga irin waɗannan matasa, na yi imanin za su iya muddin za mu jawo su." Atiku da…
Read More
Kotu ta yanke wa magidanci hukuncin kisa a Jigawa

Kotu ta yanke wa magidanci hukuncin kisa a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Wata Babbar Kotun Jihar Jigawa mai zamanta a garin Gumel, ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mai suna Rabi’u Mamman. Sanarwar Daraktan Sashin Ayyuka na Musamman da Harkokin Baƙi na Ɓangaren Shari’a na jihar Jigawa, Malam Abbas Rufa’i Wangara, ya sanya wa hannu ta ce, kotun ƙarƙashin jagoranci Mai Shari’a Abubakar Sambo Muhammad ta sami Mamman da aikata kisan kai wanda ya saɓa wa sashi na 221(B) na kundin Penal code. Kotun ta samu Rabi’u Mamman da ke garin Medinlaban a yankin ƙaramar hukumar Gagarawa da ɓoye kansa a…
Read More
Kotu ta tura ɗan gidan tsohon Shugaban Ƙasa Yar’aduwa kurkuku kan zargin halaka mutum huɗu a Yola

Kotu ta tura ɗan gidan tsohon Shugaban Ƙasa Yar’aduwa kurkuku kan zargin halaka mutum huɗu a Yola

An ingiza ƙeyar ɗan gidan tsohon Shugaban Ƙasa, Umaru Musa Yar’adua, Aminu Yar’adua, zuwa kurkuku a Yola, jihar Adamawa bisa zargin murƙurshe mutum huɗu har lahira da mota. Aminu Yar’adua, ɗan shekara 36, ɗalibi ne a Jami'ar Amurka da ke Nijeriya (AUN), wata kotun Majatare ƙarƙashin jagoranci Alƙali Jummai Ibrahim ta ba da umarnin a kai shi kurkuku a Alhamis da ta gabata bisa zargin kashe mutum huɗu da mota. An maka aminu a kotu ne bisa tuhumar yin ajalin wasu mutum huɗu sakamakon mummunan tuƙin da ya yi a ranar 23 ga Yunin 2021. Bayanan farko da 'yan sanda…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da iyayen Kakakin Majalisar Zamfara

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da iyayen Kakakin Majalisar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da yin garkuwa da mahaifi da kishiyar mahaifiyar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Nasiru Muazu Magarya, a wani hari da 'yan bindigar suka kai a ƙauyen Magarya da ke cikin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Mai magana da yawun rundunar, SP Shehu Muhammd, shi me ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Hussaini Rabiu ya tura isassun jami'an tsaro da nufin ceto mutanen da aka sace. Sai dai wani mazaunin yankin mai suna Muhammadu Lawali, ya shaida wa wakilin MANHAJA ta waya…
Read More
Tsohon gwamnan Kano da Binuwai, Dominic Oneya ya rasu

Tsohon gwamnan Kano da Binuwai, Dominic Oneya ya rasu

Bayanai daga jihar Delta suna tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan jihar Kano da Binuwai na mulkin soja, Dominic Oneya. Oneya ya rasu ne a Larabar da ta gatabata a garinsu Agbarho, jihar Delta. Majiyar jaridar Solacebase ta ce, marigayin ya rasu ne bayan da ya yi fama da rashin lafiya. An haifi Dominic Obukadata Oneya ne a ranar 26 ga Mayun 1948 a yankin ƙaramar hukumar Apapa a jihar Legas. A halin rayuwarsa, marigayin ya yi gwamna a Jihar Kano a ƙarƙashin mulkin soja daga Augustan 1996 zuwa Augustan 1998 a zamanin mulkin marigayi General Sani Abacha. Kazalika, ya riƙe…
Read More
Tsohon Mataimakin Sufeto-Janar, Nuhu Aliyu ya rasu

Tsohon Mataimakin Sufeto-Janar, Nuhu Aliyu ya rasu

Tsohon Mataimakin Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, Nuhu Aliyu, ya rasu. Marigayin ya rasu ne a Kaduna bayan fama da rashin lafiya, in ji wata majiya ta kusa da mamacin. Aliyu haifaffen garin Kontagora ne a jihar Neja, kuma an haife shi ne a Yunin 1941. A halin rayuwarsa, Aliyu ya yi sanata har na wa'adi uku, wato a 1999 da 2003 da kuma 2007, inda ya wakilci yankin Neja ta Arewa a Majalisar Dattawa. Ya riƙe muƙamin Shugaban Kwamitin Harkokin 'Yan Sanda na Majalisar Dattawa daga1999 zuwa 2003. Kafin ya yi murabus daga aikin ɗan sanda, sai da ya da…
Read More
Zulum da Shettima sun ziyarci Abba Kyari?

Zulum da Shettima sun ziyarci Abba Kyari?

An bayyana cewa Gwamna Umara Babaga Zulum na jihar Borno, da gwmanan Borno na dauri, Sanata Kashim Shettima, ba su san hanyar zuwa gidan DCP Abba Kyari ba balle kuma su ziyarce shi. Mai magana da yawun Zulum, Malam Isa Gusau shi ne ya bayyana haka don ƙarin haske kan ji-ta-ji-tar da aka yaɗa cewa jagororin biyu sun ziyarci Kyari a gidansa. Gusau ya ce ya zaɓi ya yi magana kan batun ne tun da shi Abba Kyarin bai fito ya yi wa duniya bayani game da batun ba kamar yadda ya yi alƙawari. Isa Gusau ya ce wasu makusantan…
Read More