31
Jul
Daga HAMISU IBRAHIM Yara 'yan ƙasa da shekara 5 su sama da miliyan uku ake sa ran za a yi wa rigakafin cutar shan inna (polio) da sauran cututtuka masu kassara yara ƙanana a jihar Kano daga ran 31 ga Yuli zuwa 3 ga Agustan 2021. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr Aminu Tsanyawa, sa'ilin da yake jawabi a wajen taron bita tare da 'yan jarida a Kano game da shirin yaƙi da cutar. Dr. Aminu wanda Babbar Sakatariya Amina Aliyu Musa ta wakilta a wajen taron, ya ce za a gudanar da yaƙi…
