Har yanzu makarantu 10 na rufe saboda matsalar tsaro a Neja – Kwamishina

Kwamishinar Ilimi ta Jihar Neja, Hanatu Jibrin Salihu, ta bayyana cewa har yanzu makarantu 10 daga cikin makarantun sakandare na kwana guda 56 da ake da su a jihar Neja na ci gaba da kasancewa a rufe saboda matsalar ‘yan bindiga, tare da cewa ‘yan aji shida na makarantun da lamarin ya shafa an sahale musu rubuta jarrabawar kammalawa a wasu makarantu.

Kwamishinar ta bayyana hakan ga manema labarai ne jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa a Alhamis da ta gabata a Minna, babban birnin jihar.

Ta ce 25 daga cikin makarantu suna aiki, kana ɗaliban makarantun da ke rufe an tuttura su zuwa wasu makarantu don ci gaba da karatunsu bayan tattaunarwar da hukumomin makarantun suka yi da iyayen yara.

A hannu guda, Hanatu ta ce Majalisar Zartarwa ta amince da a yi wa Bahago Secondary School da ke Minna kwaskwarima kan kuɗi Naira milyan 427.6.

A cewarta, “Wannan shi ne kashi na biyu na shirin bunƙasa makarantu. An kafa Bahago Secondary School ne tun a 1958 kuma wannan shi ne karon farko da gwamnati za ta yi wa makarantar kwaskwarima bayan shekaru 50.”

A ƙarshe, ta ce gwamnatin jihar na iya ƙoƙarinta don kawar sa matsalolin tsaron da suka addabi wasu makarantu kwana a jihar.

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *