Me ya sa Gwamnatin Tarayya ke son jihohi su kashe mutum 3,008?

Daga NASIR S. GWANGWAZO

A ranar Juma’a, 23 ga Yuli, 2021, ne dai Ministar Kula da Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Alhaji Rauf Aregbesola, ya yi kira ga gwamnonin jihohin ƙasar daban-daban da su gaggauta sanya hannu kan hukunce-hukuncen kotuna a faɗin tarayyar ƙasar na hukuncin kisa kan waɗanda a yanzu haka su ke jiran a aiwatar mu su da hukunci.

Ministan, wanda ya ke magana a Osogbo, Babban Birnin Jihar Osun, lokacin da ya ke ƙaddamar da sabon ginin gidan gyaran hali a jihar, ya ce, akwai kafatanin mazauna gidajen yari kimanin 3,008, da ke jiran a aiwatar mu su da hukuncin kisa, illa dai kawai gwamnonin jihohi daban-daban a ke jira su sa hannu kan takardar aiwatar da hukuncin.

A cewarsa, aiwatar da hukunci zai taimaka wajen rage cunkoson da a ke ta faman ƙorafi da shi a gidajen gyaran hali da ke Tarayyar Ƙasar, ya na mai cewa, wannan cunkoso shi ne babbar matsalar Hukumar Kula da Kurkuku ta Ƙasa.

Ya yi bayanin cewa, gidajen yarin Nijeriya bakiɗaya za su iya ɗaukar fursunoni guda 57,278 ne a halin yanzu, amma sai ya kasance su na ɗauke da mutane har guda 68,747, inda a ke da maza 67,422, yayin da mata guda 1,325 ke ciki. Wato dai akwai ƙarin fursunoni 11,469 kenan da su ka wuce adadin da gidajen yarin ke buƙata su iya ɗauka.

Minista Aregbesola ya ƙara da cewa, a cikin waɗanda a ke tsare da su ɗin, har guda 50,992 ne ke jiran shari’a, wato kashi 74 cikin 100 kenan na tsararru a faɗin nasar, inda tsararrun guda 17,755 ne kacal halastattun waɗanda a ka riga a ka yanke wa hukunci, wato kashi 26 cikin 100 kenan na fursunonin Nijeriya kaɗai.

A ta bakinsa, “a yanzu haka kawai adadin fursunoni 3,008, waɗanda a ka yanke wa hukuncin kisa, inda su ke jiran ranar aiwatar da hukunci kawai. Wannan ya haɗa da maza 2,952 da mata 56.

“A shari’un da a ka gama ɗaukaka ƙara da kuma hukunce-hukuncen da waɗanda a ka yankewa ba su ƙalubalantar hukuncin da a ka yanke mu su, ya kamata jihar ta aiwatar da hukuncin, ta yi abin da a ke buƙata, don kawo ƙarshen shari’un.”

To, amma sai ministan ya ƙara da cewa, gwamnonin jihohin za kuma su iya sauya dabara ta hanyar sakin waɗanda a ka yanke wa hukuncin kisan bisa la’akari da yadda su ka gyara halayensu da kuma tausaya mu su, musamman ga waɗanda tsufa ya cim-musu bayan sun daɗe a tsare da kuma waɗanda ke fama da ciwon da za su iya rasuwa.

Haka nan ya ƙara da cewa, waɗanda kuma su ka gyara halayensu su ka zamto nagari, gwamnonin za su iya sakin su ko rage mu su tsaurin hukunci zuwa hukuncin ɗaurin rai da rai ko wani ƙayyadajjen wa’adi.

Ya yi bayanin cewa, duk waɗannan abubuwa za su iya yiwuwa bisa dogaro da dokokin da su ka bayar da damar yin afuwa, waɗanda su ka yi tanadin cewa, lokaci zuwa lokaci a riƙa bin diddigin hukunce-hukuncen da a ka yanke, musamman na kisa, don sake duba lamarin.

Shi dai ministan ya na ta faman wannan bayanin ne, domin ya janyo hankali kan yadda za a buɗe hanyoyi da damarmakin rage cunkoson da a ke fama da shi a gidajen yarin Nijeriya, inda hatta ƙungiyoyin ƙasashen duniya da na cikin gida ke kokawa kan hakan tare da fafutukar ganin an samar da mafita, saboda lamarin ya na janyo wa ƙasar suka kan tauye rayuwar wasu jama’a.

Wannan ya sanya ministan ya yi ƙarin haske da da irin ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ke yi wajen ganin ta rage cunkoson, inda ya ce, a shekarar bara, lokacin da annobar Cutar Korona ta ɓarke, sai da a ka saki fiye da fursunoni guda 5,000, domin maganta matsalar.

Ya ƙara da cewa, gwamnati ta kuma gina gidajen kurkuku na zamani masu cin ɗaurarru guda 3,000 a Kano, Ribas da Abuja a ƙoƙarinta na maganta matsalar, ya na mai cewa, za a ƙara gina wasu a dukkan yankunan siyasar ƙasar guda shida masu ingantattun kayan aiki.

Tabbas waɗannan matakai da a ka ɗauka da kuma wanda Gwamnatin Tarayya ta nema a wajen gwamnonin jihohi ta bakin Ministan Cikin Gida za su taimaka matuƙa gaya wajen maganta matsalar cunkoson gidan maza, wanda ya ke ƙara haɓaka yaɗuwar cututtuka da ƙu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *