Labarai

Majalisar Dokokin Kano ta buƙaci Ganduje ya sauke Muhyi

Majalisar Dokokin Kano ta buƙaci Ganduje ya sauke Muhyi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Majalisar Dokokin jihar Kano, ta buƙaci Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya sauke dakataccen shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna majalisar ta buƙaci gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan da kwamitinta na wucin-gadi da ta ɗora wa aikin gudanar da bincike kan ƙorafin da ofishin babban akantan jihar Kano ya shigar gaban Majalisar a kwanakin baya. Kazalika, ta ce yayin zaman Majalisar na yau Litinin, kwamitin ya gabatar wa Majalisar rahotonsa inda a ciki ya…
Read More
Bidiyo: Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a Keffi

Bidiyo: Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a Keffi

Daga BASHIR ISAH Sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu a garin Keffi, jihar Nasarawa, hakan ya haifar da ambaliya a wasu sassan garin. Ruwan saman wanda aka soma da asubahin yau Litinin, an shafe sama da sa'o'i biyar ana tafkawa. Daga cikin wuraren da aka samu aukuwar ambaliyar har da fitacciyar gadar nan ta Antau, wadda ta cika ta batse da ruwa ta yadda ma amfani da ita ya gagari jama'a. Bayanan da Manhaja ta tattaro sun nuna ambaliyar Gadar Antau ta shafi wasu gidaje da ke yankin tare da lalata kayayyaki da dama amma ba a samu hasarar…
Read More
Yau Buhari zai tafi London

Yau Buhari zai tafi London

Daga UMAR M. GOMBE A wannan Litinin ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi Landon don halartar wani babban taro na duniya kan batun ilimi, wato Global Partnership for Education (GPE) na 2021 zuwa 2025. Hadimin Buhari kan sha'anin yaɗa labarai, Mr. Femi Adesina, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a safiyar Litinin. A cewar Adesina, taron wanda na haɗin gwiwa ne tsakanin Firam Ministan Birtaniya da Shugaban Ƙasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ana sa ran ya haɗa kawunan shugabannin ƙasashen duniya da gwamnatoci da masu ruwa da tsaki har ma da…
Read More
Hoto: Yadda jana’izar Bantex ta gudana a Kaduna

Hoto: Yadda jana’izar Bantex ta gudana a Kaduna

A wannan Lahadin aka gudanar da jana'izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Architect Barnabas Yusuf Bala da aka fi sani da Bala Bantex. Jana'izar ta samu halartar manyan baƙi na kusa da nesa, 'yan siyasa, jami'an gwamnati da sauransu. Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai na daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar, wanda bayan kammalawa ya nuna godiyarsa a madadin Gwamnatin Kaduna ga ɗaukacin waɗanda suka halarci jana'izar kamar dai yadda ya wallafa a shafinsa na facebook.
Read More
An tsawaita wa’adin shirin sadar da lambar shaidar ɗan ƙasa da layukan sadarwa zuwa Oktoba

An tsawaita wa’adin shirin sadar da lambar shaidar ɗan ƙasa da layukan sadarwa zuwa Oktoba

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta ƙara wa’adin shirin shigar da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) cikin bayanan mallakar layin waya (SIM) ya zuwa 31 ga Oktoban 2021. Gwamnati ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun manyan jami’ai biyu, wato Dr. Ikechukwu Ainde na Hukumar Sadarwa ta Nijeriya da kuma Mr Kayode Adegoke na Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa. Sanarwar ta ce an ɗauki matakin tsawaita wa’adin shirin ne sakamakon buƙatar hakan da masu ruwa da tsaki suka nuna domin bai wa shirin damar kaiwa ga jama’ar da ke gefen birane, baƙi mazauna ƙasa…
Read More
Matsalar rashin aiki ta fi ƙamari a mulkin Buhari – Bankin Duniya

Matsalar rashin aiki ta fi ƙamari a mulkin Buhari – Bankin Duniya

Daga UMAR M. GOMBE Wani sabon rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa, a tarihin Nijeriya matsalar rashin aiki ta fi ƙamari ne a gwamnatin Buhari. Rahoton ya ce matsalar rashin aikin ta fi shafar matasan Nijeriya ne da kashi 42.5 cikin 100, yayin da 'yan gaba da matasan ke da kashi 26.3 cikin 100. A cewar rahoton, a halin da ake ciki matsslar rashin aikin yi a Nijeriya ta tumbatsa har ninki biyar daga kashi 6.4 a 2010 zuwa kashi 33.3 a gaɓar ƙarshe ta 2020 kamar yadda rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ya nuna. Rahoton ya ce matsalar rashin…
Read More
An kama ma’aurata kan shirya garkuwar ƙarya a Neja

An kama ma’aurata kan shirya garkuwar ƙarya a Neja

Daga WAKILINMU Rundunar 'yan sanda a jihar Neja sun cafke wasu ma'aurata, Mohammed Mohammed da matarsa Sadiya Ibrahim Umar bisa laifin shirya garkuwar ƙarya da kawunansu a yankin Limawa da ke Minna babban birnin jihar. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna a ranar 15 ga Yuli, 2021 aka ba da bayanin cewa wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da Sadiya bayan ta shiga keke napep daga mararrabar Challenge da ke Maitumbi da nufin zuwa hanyar tsohon filin jirgin sama a Minna bayan da ta tashi daga wajen aikinta a Maitumbi. Ana cikin…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta ba da tallafin miliyan N15 ga iyalan ’yan sanda 13 da aka kashe

Gwamnatin Zamfara ta ba da tallafin miliyan N15 ga iyalan ’yan sanda 13 da aka kashe

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da gudummawar zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 15 ga iyalan jami’an ‘yan sandan Nijeriya da aka kashe a wani kwanton ɓauna da wasu 'yan bindiga suka yi a makon da ya gabata a ƙauyen Kurar Mota da ke ƙaramar hukumar Bunguɗu ta jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Ibrahim Magaji Dosara ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka miƙa wa Manhaja a Gusau, ranar Juma'a. A cewar sanarwar, kowanne daga cikin iyalan wadanda suka mutu za su karɓi Naira miliyan ɗaya, yayin da za a bai…
Read More
Direban jirgin da ’yan bindiga suka harbo a Zamfara ya yi basaja

Direban jirgin da ’yan bindiga suka harbo a Zamfara ya yi basaja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu bayanai da ke fitowa game da jirgin Sojin Saman Nijeriya (NAF) da ’yan bindiga suka yi wa varin wuta har ya faɗo, inda matuƙin jirgin ya tsira da rayuwar sa a jihar Zamfara. Sojin Saman Nijeriya a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne suka bayyana yadda matuƙin jirgin saman su ya tsira da rayuwarsa a lokacin da 'yan bindiga suka ɓaro jirgin daga sama a iyakar jihar Zamfara da kuma Kaduna. Ko da yake, jaridar Daily Trust ta haɗa rahoton yadda matuƙin jirgin ya sha da kyar, inda ta haƙaito cewa matuƙin…
Read More
Babbar Sallah: Sarkin Musulmi da sauran jagorori sun yi tambihi

Babbar Sallah: Sarkin Musulmi da sauran jagorori sun yi tambihi

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar nan ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya yi kira ga shuwagabanni a Nijeriya da su kasance masu tsoron Allah, su fitar da talakawansu daga ƙangin rayuwa. Alhaji Abubakar III ya bayyana haka ne a a jawabin saƙon sallah, wanda ya gabatar ranar Talatar nan a Jihar Sokoto. Inda ya ƙara da cewa, yananyin ƙangin rayuwar da al'ummar ƙasar nan ke ciki, abin dubawa ne. Kuma abu ne da yake buƙatar a ɗauki wasu matakai don ganin an daƙile shi. A cewar sa,…
Read More