Labarai

Barka da Sallah: Matawalle ya jaddada alƙawarin magance matsalar tsaro a Zamfara

Barka da Sallah: Matawalle ya jaddada alƙawarin magance matsalar tsaro a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar jihar sakamakon ayyukan 'yan fashin daji don maido da zaman lafiya a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne ran jajibirin Babbar Sallah a wata sanarwa da ya gabatar ga al'ummar jihar kan bikin Idul Kabir na bana. A cewarsa, ƙalubalen rashin tsaron gwamnatinsa ta gaje shi ne daga tsohuwar gwamnati da ya gada shekaru biyu da suka gabata, yana mai jaddada cewa shirin sasanci, zaman lafiya da tattaunawa game da batun sulhu a tsakanin masu tayar da…
Read More
Bikin Sallah: Bukola Saraki ya yi wa ‘yan Nijeriya nasiha

Bikin Sallah: Bukola Saraki ya yi wa ‘yan Nijeriya nasiha

Daga WAKILINMU Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya a Majalisa ta tara, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar idin babbar sallah ta wannan shekara, inda ya yi kira ga musulmin Nijeriya da su ci gaba da jin tsoron Allah, don shi ne sinadarin bunƙasar ƙasa. Saraki ya bayyana haka ne a saƙon barka da sallah da ya fitar yau a garin Ilorin ta Jihar Kwara, wanda ke ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Yusuph Olaniyonu. Ya ce, kamar dai shekarar da ta gabata, idin babbar sallah ta wannan shekara ma za…
Read More
Igboho ya faɗa a komar hukuma

Igboho ya faɗa a komar hukuma

Daga WAKILINMU Jami'an tsaro sun cafke jagoran fafutIkar ƙwatar wa Yarabawa 'yanci, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho. An cafke Igboho ne jiya Litinin da daddare a Kwatano da ke Tarayyar Benin yayin da yake ƙoƙarin tsallakewa ya bar Afirka. Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, Igboho ya bar Nijeriya zuwa Kwatano ne saboda shirin da yake da shi na sulalewa daga Afirka zuwa ƙasar Jamus don tsoron kamun hukuma amma ya zamana haƙarsa ba cim ma ruwa ba. Ya zuwa haɗa wannan labari, jami'an tsaron da ke riƙe da Igboho na shirye-shiryen dawo da shi…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da shirin bunƙasa harkokin noma (NALDA) a Daura

Buhari ya ƙaddamar da shirin bunƙasa harkokin noma (NALDA) a Daura

Shirin buƙasa harkokin noma na ƙasa ko kuma Agricultural Land Development Authority (NALDA) a Turance, shi ne irin sa na farko da aka ƙaddamar a Nijeriya. A wannan Litinin Shugaba Buhari ya ƙaddamar da shirin a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, kamar yadda hadimin Buhari kan sha'anin sabbin kafafen yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na facebook.
Read More
NAF ta tabbatar da faɗiwar jirgin samanta a Zamfara, an ceto matuƙin jirgin

NAF ta tabbatar da faɗiwar jirgin samanta a Zamfara, an ceto matuƙin jirgin

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta tabbatar da faɗuwar jirgin samanta (Alpha Jet) a Zamfara wanda aka ce yana kan hanyarsa ta dawowa daga aikin shawo kan matsalar tsaro a tsakanin iyakokin Zamfara da jihar Kaduna ƙaddara ta faɗa masa. Daraktan Hulda da Jama'a da Yada Labarai na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ran Litinin a Gusau kuma wadda Manhaja ta mallaki kwafinta. Jami'in ya ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Yuli,…
Read More
Dalilan tsaro sun tilasta wa Masarautar Zazzau soke hawan Sallah

Dalilan tsaro sun tilasta wa Masarautar Zazzau soke hawan Sallah

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna Masarautar Zazzau a Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Maimartaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu, ta bayyana soke hawan Babbar Sallah yayin bikin Idul Kabir na bana. Masarautar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun Sakatarenta, Alhaji Barau Musa Aliyu (Sarkin Fulanin Zazzau). Tana mai cewa an soke hawan ne saboda dalilai na halin tsaro da kuma al'amarin cutar korona. ASanarwar ta ce an cim ma matsayar soke hawan ne yayin wani taro da majalisar masarautar ta gudanar. Sai dai masarautar ta bai wa jama'arta damar gudanar da Sallar Idi a dukkanin…
Read More
Bikin Babbar Sallah: Masarautar Kano ta soke hawan daushe saboda korona

Bikin Babbar Sallah: Masarautar Kano ta soke hawan daushe saboda korona

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Majalisar Masaurautar Kano ta ce ba za a gudanar da hawan Sallah ba yayin bikin Babbar Sallah na bana. Majalisar ta ce an soke hawan ne domin cika umarnin gwamnati wajen yaƙi da cutar korona duba da cewa cutar ta kunno kai a karo na uku. Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani ne ya sanar da hakan a wannan Litinin a  Kano. Alhaji Yusuf ya ce Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, shi ne ya ba da umarnin a sanar da batun soke hawan ga masu ruwa da tsaki na masarautar.Manhaja ta ruwaito Kwamitin Shugaban Kasa…
Read More
Yahaya ya miƙa saƙon goron sallah ga sojoji da iyalansu

Yahaya ya miƙa saƙon goron sallah ga sojoji da iyalansu

Daga AISHA ASAS Shugaban Sojojin Nijeriya, Lieutenant General Farouk Yahaya, ya miƙa saƙon taya murnar bikin Babbar Sallah ga sojojin Nijeriya da iyalansu. Cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Yahaya ya ce, "Ina farin cikin taya ɗaukacin sojojin Nijeriya da iyalansu murnar bikin Babbar Sallar 2021." Ya ce bikin Babbar Sallah lokaci ne da ke tunatar da al'umma game da biyayya da sadaukarwa wanda hakan na daga cikin kyawawan ɗabi'un kowane nagartaccen soja. Tare da yin godiya ga Allah Maɗaukaki bisa rahmarSa da kariyarSa a kansu yayin da suke ƙoƙarin sauke nauyin da ya rataya a kansuna na…
Read More