Labarai

An sako Sarkin Kajuru

An sako Sarkin Kajuru

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna Bayanai daga jihar Kaduna sun nuna Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, ya samu 'yanci bayan sako shi da 'yan bindigar da suka yi garkuwa da shi suka yi. Babban ɗan Sarkin kuma Madakin Kajuru, Alhaji Musa Alhassan Adamu, shi ne ya tabbatar da labarin sakin sarkin. Ya ce suna zaune a gida da rana, kwatsam sai suka ga sarkin ya shigo. Sai dai ya ce ba a sako ragowar mutum 13 da aka yi garkuwa da su tare da sarkin ba. Ya ce cikin ƙoshin lafiya mahaifin nasu ya komo gida. Amma cewa an garzaya…
Read More
Nijeriya ta ware wa Hukumar NIA Naira biliyan 4.87 don leƙen asirin WhatsApp

Nijeriya ta ware wa Hukumar NIA Naira biliyan 4.87 don leƙen asirin WhatsApp

Daga UMAR M. GOMBE Majalisar Tarayya ta amince da kasafin Naira bilyan N4.87 da aka ware don amfanin Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (NIA) wajen bibiyar kiraye-kiraye da saƙonni a wayoyi haɗa da Thuraya da manhajar WhatsApp. Kuɗaɗen wani ɓangare ne na ƙarin kasafin Naira biliyan N895.8 da Shugaba Buhari ya nema a watan jiya wanda Majalisar Dattawa da ta wakilai suka amince da shi a makon jiya bayan da suka cilla kasafin da ƙarin biliyan N87. A cewar Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Rabon Kasafi, Sanata Barau Jibrin, za a yi amfani da ƙarin kasafin ne wajen samar…
Read More
‘Yan bindiga sun buƙaci fansar milyan N200 kafin su saki Sarkin Kajuru

‘Yan bindiga sun buƙaci fansar milyan N200 kafin su saki Sarkin Kajuru

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna Kawo yanzu, 'yan fashin dajin da suka yi garkuwa da Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, sun buƙaci a ba su fansar milyan N200 kafin su saki sarkin. Idan dai za a iya tunawa, Manhaja ta ruwaito yadda aka sace basaraken tare da wasu ahalinsa su 13, ciki har da jikokinsa da safiyar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke garin Kajuru a jihar Kaduna. Mai magana da yawun Masarautar Kajuru, Dahiru Abubakar, shi ne ya bayyana batun kuɗin fansar da 'yan bindigar suka nema a ranar Litinin. Haka nan, Abubakar ya ce 'yan bindigar…
Read More
An kama sojan da ya kashe ɗalibi a Kalaba

An kama sojan da ya kashe ɗalibi a Kalaba

Daga WAKILINMU Rundunar Sojoji ta Nijeriya ta bayyana cewa ta kama wani sojan da aka tura aiki a Gidan Yarin Calabar bisa zargin kashe wani ɗalibi da ke ajin ƙarshe a Jami'ar Kalaba mai suna Mr Gray Agbesu a ranar Juma'a, 9 ga Yuli 2021. Daraktan sashen hulɗa da jama'a na rundunar, Brig.- Gen Onyema Nwachukwu, cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata, ya ce an cafke sojan ne a daidai lokacin da ya yi ƙoƙarin arcewa gudun kada a kama shi. Ya ce yanzu haka sojan na tsare a hannun 'Yan Sandan Sojoji kuma an…
Read More
Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex ya rasu

Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex ya rasu

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna Allah Ya yi wa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Yusuf Barnabas Bala, da aka fi sani da Bantex, rasuwa. Bayanan na Manhaja ta kalato sun nuna Bantex ya rasu ne da safiyar Lahadi. Marigayin ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan jihar ne a 2015 da 2019, yayin wa'adin farko na Gwamna Nasir El-Rufai. A 2019 ne Bantex ya saki muƙamin nasa a matsayin mataimakin gwamna don neman kujerar sanata a shiyyar Kaduna ta Kudu inda abokin takararsa na PDP, Danjuma La’ah, ya kada shi. Gwamna El-Rufai ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da samun labarin rasuwar…
Read More
‘Yan bindiga sun sace shugaban kwaleji a Zamfara

‘Yan bindiga sun sace shugaban kwaleji a Zamfara

Daga SUNUSI MUHAMMAD, a Gusau. An sami ruɗani a Kwalejin Nazarin Harkokin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Bakura da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara a ranar Asabar yayin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace shugaban Kwalejin Nazarin Harkokin Gona mallakin gwamnatin jihar Zamfara, Malam Habib Mainasara a cikin gidansa da ke makarantar. Da yake yi wa wakilinmu ƙarin haske ta waya, mataimakin rajistara na kwalejin, Malam Aliyu Atiku Bakura, ya ce 'yan bindigar sun yi wa gidan shugaban makarantar ƙawanya ne da misalin ƙarfe 2:30 na tsakar daren…
Read More
An yi garkuwa da basarake da iyalansa a Kaduna

An yi garkuwa da basarake da iyalansa a Kaduna

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna Wasu 'yan bindiga a jihar Kaduna sun kai hari a masarautar ƙaramar hukumar Kajuru, inda su ka sace sarkin garin, Alhaji Alhassan Adamu da wasu daga cikin iyalansa. An sace Sarkin tare da iyalan su 13 a harin da 'yan bindigar suka kai da tsakar daren Lahadi. Binciken Manhaja ya gano an sace Sarkin mai shekara 85 tare da matansa uku, jikokinsa biyu, ma'aikatansa uku da kuma ƙarin mutum biyar. Bayanai sun nuna cewa Sarkin ya gudanar da taro ranar Juma'a a kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankinsa. Wannan…
Read More
AIB ta yi ƙarin haske kan binciken haɗarin jirgin saman da ya ci ran Attahiru da wasu

AIB ta yi ƙarin haske kan binciken haɗarin jirgin saman da ya ci ran Attahiru da wasu

Daga WAKILINMU Hukumar Binciken Haɗurra (AIB) ta ba da sanarwar cewa nan da mako guda za ta fitar sakamakon binciken farko dangane da haɗarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaban Rundunar Sojoji , Lt. Gen. Ibrahim Attahiru, tare da wasu mutum 10. Babban Jami'in Hukumar, Akin Olateru, shi ne ya bayyana hakan ran Alhamis da ta gabata a Abuja yayin da yake bayyana rahotannin da hukumar ta shirya kan haɗurran jirgin sama da suka auku har guda takwas. Sai dai, jami'in ya ce bayan miƙa rahoton nasu, zaɓi ya rage ga Rundunar Mayaƙan Sama na Nijeriya (NAF), ko…
Read More