09
Jul
Daga SUNUSI MUHAMMAD, a Gusau Aƙalla mutane 39 ne 'yan bindiga suka kashe a wani harin ramuwar gayya a Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara. A wata tattaunawa ta wayar tarho da wani mazaunin Faru mai suna Malam Lawali Ahmad Faru, ya ce, "'Yan bindigar sun afka wa garin ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Alhamis inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi da bindigogi a cikin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, wanda hakan ya yi ajalin mutane 39 wanda galibinsu maza ne." Ya ce 'yan taddan sun…
