Labarai

Ogun: Gwamna Abiodun ya ƙaddamar da Amotekun

Ogun: Gwamna Abiodun ya ƙaddamar da Amotekun

Daga WAKILINMU A matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da matsalar tsaro a Jihar Ogun, Gwamnan jihar, Dapo Abiodun, ya ƙaddamar da shirin bada tsaro na cikin gida, wato Amotekun. Da yake jawabi yayin ƙaddamawar, Gwaman ya ce ba a samar da Amotekun don ta zama kishiya ga sauran hukumomin tsaro ba, face don ƙarfafa wa fannin tsaron jihar. Ya ce gwamnatinsa za ta bai wa shirin Amotekun cikakken haɗin kai tare da samar masa da kayan aikin da yake buƙata don cim ma manufar kafa shi. Tuni Gwamnan ya nuna alamar mara wa shirin baya ta hanyar…
Read More
Filato: Gobara ta yi ta’asa a kasuwar doya a Qu’an Pan

Filato: Gobara ta yi ta’asa a kasuwar doya a Qu’an Pan

Daga WAKILINMU An samu aukuwar mummunar gobara a kasuwar doya ta Namu ta Tsakiya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Qu'an Pan, Jihar Filato. Manhaja ta kalto cewa gobarar ta auku ne da daddare a Lahadin da ta gabata inda ta lalata tarin doya da sauran kayayyakin abincin na muƙudan kuɗaɗe. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, jaridar Daily Nigerian ta ce ba a kai ga gano sababin faruwar gobarar ba. Bayanai daga yankin sun nuna sama da manona 100 ne ibtila'in gobarar ya shafa. Tare da yin kira ga gwamnati a matakai daban-daban da su tallafa wa waɗanda lamarin…
Read More
An gano mutum 51ɗauke da cutar tarin fuka a Binuwai

An gano mutum 51ɗauke da cutar tarin fuka a Binuwai

Daga UMAR M. GOMBE Dr Chubby Eze daga gidauniyar KNCV Foundation mai zaman kanta, ya ce mutum 51 ne aka tabbatar sun kamu da cutar tarin fuka (TB) daga cikin mutum 609 da aka yi musu gwaji a Makurdi babban birnin jihar Binuwai. Eze ya bayyana haka ne sa'ilin da yake amsa tambayoyin manema a Makurɗi a Juma'ar da ta gabata, tare da cewa an ɗauki samfurin mutane daga sassan ƙananan hukumomin jihar aka tafi da su cibiyoyin gwaji. Mr Dominic Alamkah wanda ke da hannu a shirin gwajin, ya shawarci waɗanda aka gano ɗauke da cutar da su tabbatar…
Read More
Kaduna: Ana ci gaba da binciken gano sarakunan da suka ɓace

Kaduna: Ana ci gaba da binciken gano sarakunan da suka ɓace

Daga FATUHU MUSTAPHA A halin da ake ciki, jami'an tsaro a jihar Kaduna sun bazama bincike domin gano wasu masu rawani su uku da suka ɓata a masarautar Atyap cikin ƙaramar hukumar Zangon Kataf waɗanda aka sace su bayan kammala wani taron sulhu da suka gudanar a Lahadin da ta gabata. A cewar Gwamnatin Jihar Kaduna, mutum shida ne suka ɓata da farko a kan hanyarsu ta komawa gida bayan taron. Ta ce jami'an tsaro sun samu nasarar gano mutum guda daga cikinsu kuma sun miƙa shi ga 'yan sanda, kana wasu mutum biyu daga ciki sun tsere daga hannun…
Read More
Ƙoƙarin da Nijeriya ke yi don kauce wa sake fama da annobar korona, Ministan Lafiya

Ƙoƙarin da Nijeriya ke yi don kauce wa sake fama da annobar korona, Ministan Lafiya

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnatin Tarayya ta bada haske kan wasu matakan da ta ɗauka domin tabbatar da Nijeriya ba ta yi fama da ɓarkewar annobar korona karo na uku ba. Yayin da wasu ƙasashen duniya suka soma sake fama da bugun annobar karo karo na uku, Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aikin gwaje-gwaje da take yi domin ganowa, killacewa da kuma kula da waɗanda suka kamu da cutar. Ehanire ya bayyana haka ne a Litinin da ta gabata a Abuja yayin da kwamitin Shugaban Ƙasa kan Yaƙi da Cutar Korona ke…
Read More
Matawalle ya sha rantsuwa kan ba shi da hannu a matsalar tsaron Zamfara

Matawalle ya sha rantsuwa kan ba shi da hannu a matsalar tsaron Zamfara

Daga WAKILINMU Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi rantsuwa da Ƙur'ani kan cewa ba shi da wata alaka da 'yan bindigar da ke addabar jiharsa. Gwamnan ya ƙalubalanci mazauna jihar, da su ma su kwatanta shan ranstuwa kamar yadda ya yi domin tabbatar da cewa ba su da hannu cikin matsalar tsaro da ta addabi jihar. Gwamnan ya yi hakan ne a ranar Lahadi a garin Gusau, babban birnin jihar yayin karɓar lambar yabo da Cibiyar Karatun Ƙur'ani ta Nijeriya ta ba shi a matsayin Khadimul Ƙur'an. Ya ce kamar yadda ya sha faɗa lamarin rashin tsaron nan ba gwamnatin…
Read More
Ogun: ‘Yan bindiga sun sace Sarkin Ijebu-Igbo

Ogun: ‘Yan bindiga sun sace Sarkin Ijebu-Igbo

Daga WAKILINMU Rahotanni daga yankin Ijebu-Igbo a jihar Ogun sun nuna wasu 'yan bindiga sun sace sarkin yankin, Oba Alade Meta, a ranar Asabar. Wata majiya ta ce a wannan rana, sarkin ya bar fadarsa da misalin ƙarfe 11 da wata motarsa 'jeep' zuwa unguwa. A kan hanyarsa ta komawa gida misalin ƙarfe 3 na rana, 'yan bindiga suka tare shi a hanya, suka fidda shi a motarsa tare da yin awon gaba da shi sanna suka bar motar tasa a nan. Tun daga wannan lokaci ya zuwa haɗa wannan labari, babu wanda ya san inda sarkin yake. Haka ma…
Read More
AMAC: Candido ya ɗauki nauyin karatun yara 29

AMAC: Candido ya ɗauki nauyin karatun yara 29

Daga AISHA ASAS Shugaban Hukumar Abuja Municipal (AMAC) Abdullahi Adamu Candido, ya yi alƙawarin bada tallafin karatu na musamman ga ɗaliban firamare su 29 da suka shiga gasar baje fasahar rubutun insha'i na bikin Ranar Farin Ciki ta Duniya na 2021 da kuma ƙaddamar da littafi wanda ya gudana a sakatariyar Hukumar Makarantun Firamare (LEA) da ke Wuse, Abuja. Shugaban ya sanar da haka ne a wajen wani taron bita ga manema labarai wanda ya gudana a Keffi, Jihar Nasarawa. Candido ya ce tuni an ware kuɗi naira milyan N26 domin cika wannan alƙawari da ya ɗauka na bada tallafin…
Read More