Sojoji sun kama kayayyakin Boko Haram a Barno

Daga AISHA ASAS

A wani shirin tsaftace yankin Muna daga harkokin ‘yan ta’adda a jihar Barno, rundunar bataliya ta 195 na shirin Operation HADIN KAI (OPHK), tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) ta kama ‘yan Boko Haram biyu tare da ƙwace tarin kayayyakin da aka tanada don amfanin ‘yan Boko Haram.

Kayayyakin da sojojin suka kama sun haɗa da gatari, kekuna guda biyar, wayar salula biyu, man fetur, ƙwayoyin ƙara kuzari, kayan abinci da dai sauransu.

Yayin samamen sojojin sun lalata sansanonin ‘yan ta’addan da dama tare da tsaftace yankin daga harkokin ‘yan bindiga.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Onyema Nwachukwu, ya fitar a Litinin da ta gabata, jami’in ya ce an yi ɗauki ba daɗi tsakanin sojoji da ‘yan ta’addan a ƙauyen Labe a daidai lokacin da ‘yan ta’addan suka yi yunƙurin arcewa inda sojojin suka yi galaba a kansu.

Tuni dai shugaban sojoji Major General Faruk Yahaya, ya jinjina wa dakarun bisa ƙoƙarin da suka yi, tare da kira a gare su da su matse ƙaimi wajen kawar da ‘yan ta’adda da harkokinsu a yankin baki ɗayansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *