Yaƙi da matsalar tsaro: A tsawaita wa’adin NYSC zuwa shekara 2 tare da ba su horon soji – Ishaku

Daga AISHA ASAS

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku, ya yi ra’ayin cewa donmin samun ƙarin matakan yaƙi da matsalolin tsaron ƙasar nan, zai kyautu a tsawaita wa’adin shirin yi wa ƙasa hidima, wato National Youth Service Corps (NYSC), zuwa shekara biyu tare da bai wa ‘yan yi wa ƙasa hidimar horo irin na sojoji.

Gwamna Ishaku ya bayyana haka ne yayin wani shiri da aka yi da shi a tashar ChannelsTV a jiya Laraba.

Gwamnantin Tarayya ta ƙirƙiro shirin NYSC ne a 1973 da nufin ƙarfafa wa matasan da suka kammala karatu a manyan makarantu gwiwa wajen gina ƙasa.

Ishaku na ra’ayin cewa tsawaita wa’adin NYSC zai taimaka wa matsan wajen samun dabarun iya kare kai musamman ma a irin wannan lokaci da ake fama da matsalar tsaro a ƙasa.

Ya ce, “Kamata ya yi NYSC ya zama na tsawon shekara biyu. Shekara guda ta samun horon soji, sannan shekara guda ta yi wa ƙasa hidima kamar dai yadda ake yi yanzu, ta yadda duk wanda ya kammala NYSC zai iya riƙe bindiga ya kuma kare kansa.

“Kamar dai yadda ake yi a ƙasar Isra’ia da Lebanon da sauransu, dole ne ku sanya ‘yan ƙasa su zama masu bada gudunmawa. Idan ya zamana ba za a iya samar da tsaro mai inganci ba, ya zama wajibi a bar jama’a su kare kansu.”