Mansurah Isah ta ƙalubalanci DPO kan ƙin sauraron ƙorafin fyaɗe da suka kai masa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Mansurah Isah, ta ƙalubalanci DPO na ofishin ‘yan sanda na Hotoro a jihar Kano da ya yi aikinsa yadda ya kamata saboda a cewarta jama’a na kallonsa.

Da alama dai kalaman Mansurah ba su rasa nasaba da yadda ɓatagarai ke lalata rayuwar ƙananan yara a jihar Kano ta hanyar yi musu fyaɗe da sauransu, inda ta ce iyaye da yawa na nan suna kuka saboda yadda aka ɓata wa yaransu rayuwa bayan an sace yaran an kuma sako su.

Mansurah ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram a cikin wannan makon inda ta gwamatsa Hausa da Ingilishi wajen bayyana ra’ayin nata.

A cewarta, “Akwai iyaye da dama waɗanda ba za su iya cewa komai ba in banda kuka saboda yadda aka ci zarafin ‘ya’yansu.

“An yi garkuwa da su, an yi musu fyaɗe, an wahalar da su an kuma yi safarar su, duk da haka iyayensu sun yi shiru saboda gudun kada yaran su shiga ƙunci ko su samu taɓin hankali.

“Su kuma ‘yan sandan da ya kamata su ba da kariya suna wani nuƙu-nuƙu. Sannan a ƙarshen lamari su ɗora wa mutum laifi, har ma su ce sun kama mutum da laifin rashin ɗa’a.”

Ta ƙara da cewa, wannan ne ya sa mutane da dama ba za su iya cewa komai ba idan irin wannan matsalar ta faru ta lalata rayuwar yara sai dai su yi ta faman kuka da shiga ƙunci iri-iri saboda takaicin abin da ya faru.

Tana mai cewa, “Muna buƙatar samun canji saboda Allah.”

Sai dai ganin yadda Mansurah ta saki jiki ta bayyana ra’ayinta musamman kuma a kan ‘yan sanda, hakan ya sanya wasu daga cikin masu bibiyarta a shafin nata na Instagram suka nuna tsoronsu kada wani abu biyo baya.

Don kuwa ɗaya daga cikin ‘comment’ ɗin da aka yi ƙarƙashin bayanan da Mansurah ɗin ta wallafa cewa ya yi bai so yadda Mansurah ɗin ta wallafa wani abu a kan DPO ɗin ba saboda sanin halin ‘yan sanda da kuma yadda ƙasar take a yau.

Amma maimakon ta tsorata sai Mansurah ta ci gaba da ce, “Wannan shi ne dalilin da ya sa jama’a ke tsoro. Don haka ku sani, in wani abu ya same ni, a binciki ofishin ‘yan sanda na Hotoro.

“‘Yarmu aka yi wa, mun sha kuka, mun
shiga damuwa. Kuma an ce kar mu damu. An ce ba mu da ‘case’. Allah mana gani,” kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram.