Siyasa

Tambuwal ya sha da ƙyar a takarar Sanatan Sakkwato ta Kudu

Tambuwal ya sha da ƙyar a takarar Sanatan Sakkwato ta Kudu

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi nasarar lashe kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu da ya nema. Baturen zaɓen yankin, Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo, shi ne ya sanar da nasarar Tambuwal inda ya ce ya samu ƙuri'u 100,860 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin karawarsa na APC, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba wanda ya tsira da ƙuri'u 97,884. Nasarar Tambuwal ɗin dai na zuwa ne bayan da zaɓen kujerar ya kasance wanda bai kammalu ba a zaɓen yayin zaɓen 'yan Majalisar Tarayya da aka gudanar ran 18 ga watan Maris ɗin da ya…
Read More
Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

Hedikwatar INEC ta ƙi amincewa da bayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa

*Ta ba da umarnin dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaɓe Babban Ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ya dakatar ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen cike giɓi na Gwamnan Jihar Adamawa da ya gudana ranar Asabar. Ofishin ya ɗauki wannan mataki ne bayan da labarin ayyana 'yar takarar Jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓe da Kwamishinan Zaɓe na jihar, Farfesa Hudu Yunus Ari, ya yi a ranar Lahadi ya isa gare shi. Cikin sanarwar da INEC ta wallafa a shafinta na Tiwita mai ɗauke da sa hannun Kwamishinan hukumar, Barista Festus…
Read More
Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Sanata Binani ta ɗaɗa Gwamna Fintiri da ƙasa a Adamawa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ayyana Sanata Aisha Dahiru (Binani) a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa. Kwamshinan Zaɓe na Jihar Adamwa, Farfesa Hudu Yunus Ari, shi ne ya bayyana nasarar Binani wadda ta kasance 'yar takarar Jam'iyyar APC. Da fari, Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam'iyyar PDP ne ke gaba da yawan ƙuri'u kafin daga bisani Binani ta shige gabansa. Magoya bayan jam'iyyar PDP sun nuna rashin jin daɗinsu ganin Kwamishinan Zaɓe na jihar ne ya bayyana sakamakon zaɓen maimakon Baturen Zaɓe. Da wannan nasarar da ta samu, a iya cewa Sanata Aisha ta zamo mace ta…
Read More
Zaɓen cike giɓi: NNPP ta lallasa APC a Fagge

Zaɓen cike giɓi: NNPP ta lallasa APC a Fagge

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Jam'iyyar NNPP, Barista MB. Shehu, ya lashe zaɓen ɗan Majalisar Wakilai na ƙaramar hukumar Fagge a Jihar Kano. Nasarar da MB Shehu ya samu ta kawo ƙarshen ɗan majalisa mai wakiltar shiyyar a Majalisar Wakilai, Aminu Sulaiman Goro na Jam'iyyar APC wanda ke kan wa'adinsa na uku a Majalisar. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Baturen zaɓen Ibrahim Tajo Suraj, ya ce MB Shehu ya samu ƙuri'u 19,024 daga jimillar ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da ɗan takarar Jam'iyyar Labour, Shuaibu Abubakar ya rufa masa baya da ƙuri'u 12,789. Sakamakon zaɓen ya nuna Aminu Sulaiman Goro…
Read More
Ado Doguwa ya lashe zaɓen Ɗan Majalisar Wakilai na mazaɓarsu

Ado Doguwa ya lashe zaɓen Ɗan Majalisar Wakilai na mazaɓarsu

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Alhassan Ado Doguwa, ya lashe zaɓen ɗan Majalisar Wakilai na Mazaɓar Tudun Wada/Doguwa a Jihar Kano. Doguwa ya lashe zaɓen ne yayin zaɓen cike giɓi INEC ta gudanar a ranar Asabar. Baturen zaɓen, Farfesa Sani Ibrahim, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen inda ya ce ɗan takarar Jam'iyyar APC, Ado Doguwa, ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 41, 573. Ya ce ɗan takarar Jam'iyyar NNPP, Yushau Salisu ne ya zo na biyu da ƙuri'u 34,831, yayin da ɗan takarar Jam'iyyar PDP ya zo na uku da ƙuri'u 2,111.
Read More
An sake zaɓe a ƙananan hukumomi 16 a Kano

An sake zaɓe a ƙananan hukumomi 16 a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano A ranar Asabar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta sake zaɓe a wasu ƙannan hukumomi guda 16 a Jihar Kano. Ƙananan hukumomin Fagge da Ungoggo da Dawakin Tofa da Makoɗa, Warawa da sauran na daga cikin wuraren da sake zaɓe ya shafa. Mahaja ta kalato cewar tun da misalin ƙarfe 7:30 na safe da yawan masu zaɓe sun fito domin kaɗa ƙuri'arsu. Sauran yankun da zaɓen ya shafa har da Gabasawa, Gezawa, Tudun Wada, Doguwa, Gwarzo, Takai, Garko, Wudil, Ajingi, Danbatta da kuma Gaya. Wasu masu sanya ido kan zaɓe sun bayyana wa Manhaja gamsuwarsa…
Read More
Ododo ya zama ɗan takarar gwamna na APC a Kogi

Ododo ya zama ɗan takarar gwamna na APC a Kogi

Tsohon Odita Janar na Gwamnatin Jihar Kogi, Usman Ododo, ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar Gwamna da Jam'iyyar APC ta shirya a jihar. Zaɓen fidda gwanin ya gudana ne a gundumomi 239 a tsakanin ƙananan hukumomi 21 da jihar ke da su. Ododo ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 78,704 inda ya doke sauran abokan hamayyarsa su shida. Ododo na hannun daman Gwamna Yahaya Bello ne wanda ya tsayar da shi takara 'yan kwanaki kafin zaɓen. Sakataren Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani na takarar gwamna na Jam'iyyar APC, Patrick Obahiagbon, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen, inda ya ce baki…
Read More
Kano: ‘Yan daba sun kai hari rumfar zaɓe a Kurna

Kano: ‘Yan daba sun kai hari rumfar zaɓe a Kurna

'Yan daba sun kai hari rumfar zaɓe mai lamba 030 cikin Gundumar Alasawa Kwaciri, Kurna Gabas a yankin Ƙaramar Hukumar Fagge, Jihar Kano. Bayanai sun ce sun kai harin ne ɗauke da makamai tare da tarwatsa masu zaɓe inda kowa ya tsere neman mafaka. An yi sa'a 'yan sanda a yankin sun yi aikinsu wajen kwantar da tarzomar inda suka kora 'yan dabar da kuma bai wa jama'a da ma jami'an zaɓe kariya kana aka ci gaba da zaɓe yadda aka tsara. Sai dai babu wanda ya jikkata sakamakon harin. A ranar Asabar Hukumar Zaɓe, INEC, ta gudanar da zaɓen…
Read More
APC ta lashe zaɓen Sanatan Filato ta Tsakiya

APC ta lashe zaɓen Sanatan Filato ta Tsakiya

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Hon. Diket Pland na Jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Filato ta Tsakiya. Sa'ilin da yake bayyana sakamakon zaɓen a Pankshin, Baturen zaɓen, Dr. Jima Lar, ya ce Hon Plang ya lashe zaɓen ne da ƙuri'u 131,129. Yayin da Yohanna Gotom na Jam'iyyar PDP ya rufa masa baya da ƙuri'u 127,022, sannan Garba Pwul na Jam'iyyar Labour ya zo na uku da ƙuri'u 36,510.
Read More