Siyasa

APC ta lashe zaɓen Sanatan Kudancin Yobe

APC ta lashe zaɓen Sanatan Kudancin Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Babban jami'in hukumar INEC, Dr. Abacha Melemi na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gashua (FUGA), shi ne ya jagoranci zaɓen 2023 a lokacin da yake sanar da sakamakon a yau a garin Potiskum. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta INEC ta ayyana Sanata Ibrahim Mohammed Bomai a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wanda ya gudana yau Asabar, a Yobe ta kudu. Sanata Bomai na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 69,596 inda ya doke abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Hon. Halilu Mazagane, mai ƙuri'u 68,885. Sauran sun haɗa da Hon. Yerima Adamu na ADC 652, Hon. Jauro…
Read More
Abba Gida-Gida ya shawarci shugabanin ƙananan hukumomin da za a gudanar da zaɓen cike giɓi a yankinsu

Abba Gida-Gida ya shawarci shugabanin ƙananan hukumomin da za a gudanar da zaɓen cike giɓi a yankinsu

Daga RABI'U SANUSI a Kano Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya sake bai wa shugabannin ƙananan hukumomin jihar kano 44 da sauran manyan ma’aikatansu shawarar kauce wa kuskuren yin amfani da su wajen ɗibar kuɗaɗen ƙananan hukumomin kan zaɓen da za a sake a wasu yankuna a jihar. Wannan batun na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kakakin sabon Gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai ranar Alhamis. Sanarwar ta ce, Gwamnan mai jiran gado na da cikakkiyar masaniyar cewa gwamnati mai barin gado tana shirin fitar da kuɗaɗe da…
Read More
Zaɓen cike gurbi: PDP ta koka a Zamfara

Zaɓen cike gurbi: PDP ta koka a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Yayin da zaɓukan da za a sake ke gabatowa, jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta zargi ’yan sandan Nijeriya da yunƙurin musgunawa mambobinta a jihar a yayin zaɓen. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta ce, za a sake gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, kuma za a gudanar da zaɓen ne na kujerar ɗan majalisar dattawan Zamfara ta tsakiya da kuma kujeru biyu na majalisar wakilai. Ofishin yaɗa labarai na Dauda Lawal a ranar Larabar da ta gabata a Gusau ta ce jam’iyyar ta nuna damuwarta game da katsalandan…
Read More
Yawan mu ya kai mu ƙwace Majalisar Wakilai a hannun APC – ‘Yan adawa

Yawan mu ya kai mu ƙwace Majalisar Wakilai a hannun APC – ‘Yan adawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓaɓɓun 'yan majalisar wakilai na jam’iyyun adawa a Nijeriya, suna da yawan da za su iya ƙwace shugabancin majalisa ta 10, da za a buɗe cikin watan Yuni, a cewar wani ɗan majalisar wakilai na Jam'iyyar NNPP. Wannan matsayi ya fito fili ne bayan wani taro da zaɓaɓɓun 'yan majalisar wakilan, waɗanda suka fito daga jam'iyyun adawa suka yi a daren Talata. Matuqar hakan ta tabbata, matakin zai kasance karon farko tun bayan dawowar Nijeriya kan tafarkin dimokraɗiyya a 1999, da 'yan adawa suka shugabanci wata majalisar tarayyar a ƙasar. Haɗakar jam'iyyun adawa na…
Read More
APC a Delta ta musanta korar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa daga jam’iyyar

APC a Delta ta musanta korar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa daga jam’iyyar

Daga WAKILINMU Jam'iyyar APC ta musanta korar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege daga jam'iyyar kamar yadda rahotanni suka nuna. Da fari rahotanni sun nuna yadda APC a Jihar Delta ta kori Omo-Agege daga jam'iyyar cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Maris da kuma sa hannun Shugaban jam'iyyar na jihar, Ulebor Isaac a madadin shugabancin jam'iyyar a jihar. An ce sun ɗauki matakin korar ne bayan da suka zarge shi da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa da sauran laifuka waɗanda ba a bayyana ba. Sai dai kuma, tsagin APC a jihar da ke yin Mataimakin Shugaban…
Read More
APC ta kori Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Omo-Agege

APC ta kori Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Omo-Agege

Daga BASHIR ISAH Jam'iyyar APC a Jihar Delta ta kori Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege, daga zama mamban jam'iyyar kan zargin yi wa jam'iyya zagon ƙasa da sauran laifuka da ba a bayyana su ba. APC reshen Delta ta sanar da koran Omo-Agage daga jam'iyyar ce cikin wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Maris, 2023 wadda aka raba wa manema labarai a ranar Litinin. Idan ba a manta ba, Omo-Agege ya yi takarar gwamnan jihar Delta ƙarƙashin APC inda ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP, Sheriff Oborevwori a zaɓen da ya gudana kwanan baya.…
Read More
Ƙalubalantar canja fasalin Naira ya sa na sha kaye a zaɓe – Matawalle

Ƙalubalantar canja fasalin Naira ya sa na sha kaye a zaɓe – Matawalle

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya alaƙanta dalilin faɗuwarsa zaɓe da ƙarar da suka shigar da Gwamnatin Tarayya akan sauya fasalin kuɗi da Babban Bankin Nijeriya ya yi. Gwamnan ya zargi cewar, wasu ƙushoshi a cikin Gwamnatin Tarayya da yin yaƙi da shi tuƙuru domin ganin bai sake komawa gwamnan jihar ta Zamfara ba. Idan za a iya tunawa, Matawalle ya yi takara ne a jam'iyyar APC mai mulki, inda Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ya buga shi da ƙasa. Bugu da ƙari, gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje sun kai…
Read More
INEC ta sanar da ranar sake zaɓen majalisar jiha a wasu ƙananan hukumomi a Katsina

INEC ta sanar da ranar sake zaɓen majalisar jiha a wasu ƙananan hukumomi a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) reshen Jihar Katsina, ta ayyana ranar 14 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin ranar da za a sake gudanar da zaɓen wasu ƙananan hukumomin jihar guda uku da suka haɗa da Kankia da Ƙanƙara da kuma Kurfi. Hukumar ta bayyana cewar zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa a ranar 18 ga watan Maris, 2023 bai kammalu ba, saboda haka ne aka sake saka ranar da za a kammala su. INEC ta ce, dokokinta ne suka yi tanadin sake gudanar da zaɓe a rumfuna ko…
Read More
APC a Bauchi ta dakatar da shugabanta a matakin gunduma kan yi wa jam’iyya zagon ƙasa

APC a Bauchi ta dakatar da shugabanta a matakin gunduma kan yi wa jam’iyya zagon ƙasa

Daga BASHIR ISAH Jam'iyyar APC a Jihar Bauchi a matakin gunduma ta dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar, Alhaji Babayo Aliyu Misau, bisa zargin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa. Gundumar Kukadu Gundari a yankin Ƙaramar Hukumar Misau, ce ta dakatar da Babayo Aliyu a matsayin mamba a jam'iyyar bayan da ta zarge shi da aikata wa jam'iyyar zagon ƙasa. Shugabancin jam'iyyar Gundumar Kukadu ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Zango Lawan da Sakatarensa, Aliyu Hassan Adamu da kuma Mataimakiyar shugabar mata, Asabe Ahmed, shi ne ya bayyana sanarwar dakatarwar ga manema labarai a ranar Asabar. Sun bayyana cewa sun kira taron gaggawa a…
Read More